Ka san sirrin nasarar ba-zata ta Leicester?

Ƙungiyar ta yi ɗaya daga manyan nasarori na ban mamaki da aka taɓa samu a tarihin ƙwallon ƙafa, wannan kuma nasara ce ta dabarar sayen 'yan wasa a kan masu dogaro da bayanai ko alƙaluma.

Angela Henshall ta yi nazarin sirri huɗu na nasarar

Gagarumar nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Leicester ta samu wadda ba a taba tsammani ba za ta iya samar musu da kudi sama da dala miliyan 217 kamar yadda masu fashin bakin bayanan harkokin kwallo Repucom suka bayyana.

To amma ta yaya aka yi 'yar karamar kungiya daga yankin tsakiyar Biritaniya ta yi wannan nasara ta ban mamaki da ba a taba gani ba a tarihin wasa?

A wannan zamani da masu sarauta wadanda ke da dimbin kudi marassa iyaka suke tafiyar da harkokin kwallon kafa, abu ne da ba a taba tsammani ba cewa kungiyar da ke baya a dangi cewa za ta iya shammatar harkar kwallon kafa haka.

A watan Agusta na 2015 damar da ake ba kungiyar Leicester ta daukar kofin Premier kashi daya ce a cikin 5,000. A wannan watan dai hukumar caca ta Ladbrokes ta ba wa tsohon kocin kungiyar Manchester United Sir Alex Ferguson damar kashi daya a cikin 1,000 ya yi nasara a wani wasan talabijin mai suna Strictly Come Dancing.

Wannan labari ne mai matukar ban mamaki, hasali ma ana rade-radin tuni har an fara shirya wani fim a Hollywood ta Amurka domin nuna yadda mashahurin dan wasan gaba na kungiyar ya rikide har kuma ya burunkasa daga leburan kamfani zuwa kungiyar kwallon Ingila ta kasa.

To amma shin wannan abu ne da ba a taba tunanin zai faru ba? Mun yi nazarin sirri hudu na wannan nasara ta kungiyar me kama da almara ko dabo.

Dabarar sayen 'yan wasa, kuma masu araha.

Kwararrun masana lissafi a yanzu suna da matukar muhimmanci ga kungiyoyin wasanni, inda suke taimaka wa kungiyaoyi kamar su Manchester United zayyana tsarin jerin 'yan wasan da suka fi dacewa, yawanci kuma 'yan wasa ne da ke da albashin da ya ke sama da miliyan goma, wadanda za su iya cin manyan kofuna.

Zakarun gasar Premier ta bara Chelsea, a misali ta yi amfani da 'yan wasan da ta kace musu fam miliyan 215, kwatankwacin dala miliyan 310.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fam mliyan daya kacal aka sayo Jamie Vardy

Leicester ta yi amfani da tsarin kididdiga ta sarrafa dan karamin kasafinta na fam miliyan 57 kasa da dala miliyan 82 ta hanyar tsohon tsari, inda ta yi cefanen 'yan wasanta daga kananan kungiyoyi a gasannin da ba a san su sosai ba.

Jenny Amalfi, darektar koyo da rayawa a kamfanin daukar ma'aikata na Airswift ta ce: ''Iya dauko mutanen da suka dace a lokacin da ya dace,a wurin da ya dace kuma a farashin da ya dace zai iya zama bambancin nasara da rashinta na wani aiki.''

Jami'ar ta ce, nasarar Leicester ta dogara ne kacokan a kan tabbatar da ganin cewa duk dan wasan da suka sayo ya dace.'' Kungiya ce mai tsari sosai kuma kowa a cikinta ya san aikin da ya kamata ya yi, wanda wannan abu ne da kungiyoyi da dama da ma kamfanoni ko hukumomi suke fafutukar a kai.''

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Da an dauka Riyad Mahrez ba zai taba iya babban wasan kwallon kafa ba saboda lenge-lenge ne bashida kwari

Dan wasan gaba na Leicester Jamie Vardy, na daya daga cikin 'yan wasa masu mafiya amfani, masu araha, wanda aka siyo daga kungiyar da ba a santa ba sosai ta Fleetwood Town FC a kan fam miliyan daya kacal, kuma dan wasan ne ya fi ci wa kungiyar kwallo, har 22 a bana.

Wani dan wasan da ya ba da mamaki kuma shi ne Riyad Mahrez, wanda a da aka dauka ba zai iya zama wani babba dan kwallo ba ma saboda ana ganin ba shi da kwari.

Hatta sayen 'yan wasa ma daga kungiyar Le Havre ta gasar lig na biyu na Faransa sa'a ce kawai, domin kungiyar ta Leicester ta je domin duba wani dan wasa ne daban amma kuma sai ta ga Mahrez ya ma fi wanda suka je zawarci.

Ka yi iya wasa iya karfinka

''Maimakon su rika mayar da hankali kan nazarin irin yanayi ko dabarar abokan karawarsu, 'yan wasan kungiyar sun zabi su rika zage damtse ne, suna wasa iya karfinsu, su wujijjiga abokan karawar kuma su tsare gida sosai,'' in ji Amalfi.

Kwararru na ganin wannan dabara ce ta yadda kungiya ke amfani da kwarewar da ta mallaka, wadda jami'ar Harvard ( fannin kasuwanci) ta bayyana a matsayin karfin gogayyarta.

Ka samo tsohon shugaba wanda zai dogara da makaminsa

Kocin da aka taba yi wa lakabi da mai karewa a matsayi na bayan zakaru a kullum, Claudio Ranieri wanda tsohon kocin Chelsea ne ya yi zaman jiran wannan lokaci har tsawon shekara 30.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Claudio Ranieri ya mayar da hankali wajen renon 'yan wasa da yake da su ne

Kociyan ya mayar da hankalinsa wajen raya 'yan wasan da daman yake da su a kungiyar ta Leicester. Chris Roberts, darektan horo na kamfanin bayar da shawarwari kan harkokin kasuwanci, mai suna Accelerating Experience, ya nuna cewa 'yan wasan Raineri da farko ba wasu gwanaye ba ne. ''Ammaneman 'yan wasa a tsanaki da bayar da fifiko kan matasan 'yan wasa, da kuma sayo 'yan wasa masu araha, amma kuma masu kwazo, su suka taimaka wa kungiyar har ta gagara.

Ranieri wanda aka taba yi masa lakabi da kocin da a kullum sai ya sauya 'yan wasa da dabarar wasa, sauyi 27 kawai ya yi a tsarin 'yan wasansa a dukkanin wasan gasar ta Premier ta bana, wanda wannan shi ne mafi kankanta a tarihi.

Ya mayar da hankali wajen ganin ya raya kowane dan wasa a matsayin wanda zai iya tsere sa'a sanna kuma ya horar da dan wasan yadda zai iya wasa da takwarorinsa tare, abin da a karshe ya kai shi ga samar da cikakkiyar kungiya mai karfin samun nasara.

Tunanin abin da ya kamata na Ranieri ''ya taimaka wajen ciyar da kungiyar gaba har ta kai sama,'' in ji Chris Underwood, manajan darektan kamfanin nemo manyan jami'ai na Adastrum Consulting.

Dabarar Ranieri ta jibanci nuna sha'awa da dagiya da kuma burin kafa tarihi, wanda wannan abu ne da a yanzu ya yi!''

Maimakon ba wa 'yan wasansa ladan makudan kudade da motocin gayu na Ferrari, dabarar Ranieri ta kunshi shirya wa 'yan wasan nasa liyafar cin kayan kwalan da makulashe ne, idan sun yi nasara a wasa.

Dabarar tsawaita wasa

Stuart Podmore, na kanfanin saka jari na Schroders, ya ce, '' akwai darussan da za a koya na nasara a juriya da hakurin zuba jari. Ya ce, ''kungiyar jure wa dabararta ta tsawon lokaci, ta hanyar amfani da 'yar riba kadan ta 'yan wasa da kuma rashin tsoro.''

Wannan nasara ta tarihi da Ranieri ya yi ba ta rude shi ba, domin ba wani babban sauyi da zai yi a kungiyar, saboda ya jaddada cewa ba shi da niyyar zawarcin manyan 'yan wasa, ganin cewa wai yanzu kudade na shigo wa kungiyar.

Sai dai kuma Underwood na Adastrum ya ce, bincike a kan shugabanci ya nuna cewa buri yana da iya lokacinsa, ''kuma akwai lokacin da burin shugaba a wani aiki zai cika.''

Ya zuwa yanzu ba a san ko haka lamarin zai kasance ga Ranieri ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. Four secrets to Leicester FC's fairy-tale win