Ya soyayya tsakanin lauyoyi masu shari'a da juna take?

Ni ne ke kula da al'amuran da suka shafi dokoki da rikici a kamfaninmu na lauyoyi. Ta yaya zan hukunta wani lauyan kamfanin namu da ke soyayya da wata lauyar da muke shari'a da ɓangarensu?

Nazarin Chana R Schoenberger

Amsa: Ɗaya daga cikin muhimman aikin lauya shi ne ya tsare duk wani abu da ya shafi mutumin da yake karewa. Wannan abu ne mai wuya idan akwai masu fuska biyu a tsakanin lauyoyinka, wato suna aiki da kamfaninka amma kuma suna da wata alaka da ɗaya kamfanin da ke wakiltar wani da kuke shari'a da shi.

Idan ka kalii yanayin a taƙaice za ka ga yanayi ne da ke nuna alamar wani rikici da ke shirin barƙewa.

''Duk lokacin da na kalli lamarin sai na ga abin ba shi da kyau kuma sai na ga ya ƙara muni,'' in ji Carl E Schneider, farfesa a kan shari'a kuma farfesa a aikin likita a jami'ar Michigan. ''Abu ne na sakarci.'' Ya ce.

Abu na farko da kamfanin zai yi, in ji Schneider ya ce, shi ne a fitar da lauyan da yake soyayyar daga cikin lauyoyin da suke wakiltar mutumin a kotu.

Mataki na gaba kuma: ka duba ka ga ko ya dace lauyan ya ci gaba da aiki a kamfanin, idan aka yi la'akari da halayyarsa wadda ba ta dace ba. Maganar hukuncin da ya dace daya ce ko lauyan da ake magana a kansa babba ne ko karami ne, in ji Scneider.

A matsayinka na wanda ke kula da da'ar ma'aikata a kamfanin na lauyoyi sai ka bi ka'idar ladabtar da duk ma'aikacin da ya aikata wani abu da bai dace ba.

Ya kamata a ce akwai kwamitin da ke da alhakin kula da irin wadannan matsaloli, idan babu shi, to sai ka kai maganar gaban manajan hadin gwiwa na kamfanin. Abokan hadin gwiwa na kamfanin wato sauran lauyoyi za su duba su ga matakin da ya kamata su dauka a kan wannan lauya.

Mataki na gaba kuma shi ne, sai ka duba ka tsara yadda kamfanin zai bayyana wa sauran abokan aiki abin da ya faru, domin lauyoyin daya bangaren da kamfanin yake shari'a da su na bukatar sanin abin da ya faru in ji Scheider. Ya dace a sheda musu abin da ya faru, domin shi ne adalci, saboda abu ne da zai iya yi wa aikinsu zagon kasa.

Akwai wanda kuma ya kamata ya san lamarin?

Wannan ya danganta da dokokin lauyoyin jihar da abin (soyayyar) ya faru. ''Zai fi kyau ka yi riga-malam masallaci, ka gaya wa mutumin da kamfanin naku yake kare wa a sharia'r abin da ya faru (kafin ya ji daga wani wuri).'' Kamar yadda Schneider ya bayar da shawara. Amma fa kada ka yi tsammanin wannan tattaunawa taku da mutumin za ta yi dadi fa.

Duk da haka wani abu mai dadin ji shi ne, ba lalle ne mutumin ya bar kamfanin lauyoyinku ba ya koma wani, saboda abu ne mai wuya sosai mutum ya sauya kamfanin lauyoyi ana tsakar shari'a musamman babbar shari'a, in ji Schneider.

Babban hadari ga mutumin da kuke karewa da kuma kamfanin naku shi ne, za a iya ba wa daya bangaren lauyoyin da kuke shari'a da shi wasu bayanai a game da shari'ar, ko da ba da niyya ba.

Idan shari'ar tana gaban alkali, to kila zai fi kyau ka kamfaninku ya gaya wa alkalin lamarin sannan ku jira matakin da zai iya biyo baya.

Yaya za ka kauce wa irin wannan abin a gaba? Ka kara ba wa lauyoyin da ke aiki a kamfanin naku horo kan bin dokokin aiki da kaucewa rikici, tun da bisa ga dukkan alamu ba a kiyayewa da dokokin.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Strange legal bedfellows