Ka san illar rashin bashi a kanka?

Hakkin mallakar hoto Dennis Steshenko Getty

Akan ce bashi hanji ne, cikin kowa akwai shi. Ba shakka dukkanninmu mun taba yi. Me? Cin bashi mai yawa: bashin zuwa makaranta, da bashin sayen gida, da bashin yin wani abu kamar zuwa yawan shakatawa a wata kasa kamar yankin Karebiyan (caribbean).

Ga nazarin Maria Atanasov

Ganin yadda muka shiga wani zamani na rage amfani da tsabar kudi a hannu, sai ta hanyoyin waya da intanet, abu ne mai sauki ka dauko katinka na banki, ka biya kudin wani abu kamar shayi ko gahawa da ka saya, maimakon ka lalubi 'yan canjin da ke aljihunka ka biya. Ta hanyoyi da dama bashi abu ne ya danganci neman sauki.

To amma me zai faru idan a ko da yaushe sai mun yi fafutuka a karshen wata domin mu biya bashin? Mun karkata ga shafin intanet na tambaya da amsa domin jin ta bakin jama'a ko yana da alfanu a ce ba bashi a kan mutum. Ga abin da wasu suka ce game da cin bashi.

Wane irin bashi ne?

Wannan tambaya ta rasa wani muhimmin bangare nata, wanda take bukatar a fayyace irin bashin da mutum ya ci, in ji Kostantinos Boulis. Ya ce, ''bashin abubuwan jin dadin rayuwa abu ne da za a kyamata kamar majina. Idan ka sayi duk wani abu da ya kai dala 100kuma ka biya bashin a cikin shekara daya, za ka biya akalla kusan dala 120.

Idan ka duba za ka ga wannan sakarci ne, Ba wai ka sayi abin da watakila ba ka bukata ba ne ba ma sam-sama, ka biya wani karin kashi 20 cikin dari ne ba gaira ba dalili.''

Cin bashi domin aiwatar da wani abu na rayuwa da za ka amfana a gaba, ya ce, ''wannan wani abu ne na daban kacokan, kuma wajibi ne ka yi tunani da shawara mai kyau kan abin da za ka yi da kudin da kuma abin da bai dace ka yi da shi ba.

Idan ka karbi gida bashi, wanda za ka biya a tsawon shekara 30, inda za ka rika biyan kashi uku da rabi cikin dari na kudin a duk shekara, to wannan abu ne mai kyau idan yanayin ya dace ka yi hakan.''

Amma idan har yanzu kana ganin bashi illa ne ''to hakan yayi daidai domin za ka samu ka yi barcinka lafiya kalau ba tare da wata fargaba ba,'' ya kara da cewa. ''Illa dai zai kasance gadon naka ba wani wanda za kamore masa ba ne, kuma gidanka zai kasane dan kankani bai kai wanda kake bukata ba.''

Abu ne mai amfani

A wani lokacin bashi abu ne da za a iya dauka mai amfani wanda mutum zai kyautatta rayuwarsa da shi kamar yadda Jeremy Karmel ya ce. ''A wurin mutane da dama bashi ne abu ne da za su iya amafni da shi wajen cimma burinsu..''

Karmel ya yi misali da ilimi a matsayin daya daga cikin abubuwan da za a iya daukar bashi saboda su. Ya ce, ''idan kana son zama likita ko lauya, kuma iyayenka ba masu kudi ba ne sosai, za ka iya rancen kudi domin ka samu ka yi wannan karatun.

Ya kara da cewa, ''cin bashi ba karamin ba ne. Wajibi ne ya kasance kana da wani kuduri da tsari kyakkyawa da za ka biya bashin. Saboda haka,a wurin mutane da dama bashi abu ne da zai basu dama su cimma burinsu shekaru kafin idan da a ce ba su ci bashin ba ba za su iya cimma burin ba.''

Kada ka yi sake da damarka.

Wajibi ne ka sayi kayan da kake bukata a lokacin da kake matukar bukatarsu, in ji Vivek Nagarajan. Ya ce, '' Na ranto kudi in sayi babur. Na ranto kudi domin domin in je wata kasa na zauna, in auri wadda nake so. Na yi rance domin in yi abubuwa da dama da zan ji dadi.''

''Duka dai sai ya kasance ina cikin bashi da nake biya har tsawon shekara goma.'' ya kara da cewa. ''Sai dai duk da haka albashina ya isa in biya duka bashin, duk da cewa na biya kashi 20 cikin dari ko makamancin haka na kudin ruwa, abin da nake samu ya karu da kashi 1000 bisa dari tun shekara ta 2003, saboda haka lissafin ya zo min daidai ta yadda zan ci bashi in sayi abu yanzu, kuma ba zai dame ni ba a gaba.

Idan da ban yi sayayyar ba, na ce sai na tara kudi sannan na saya to da kila abin ya zo min da jinkiri sosai sanna kuma na bata lokaci matuka''

La'akari da shekarunka?

Marc Bodnick ya nuna cewa ya kamata ka yi la'akari da shekarunka idan za ka ci bashi. Ida n kana matashi, yanzu ka fara rayuwarka, to za ka iya cin bashi. Amma idan lokaci ya ja, ka kai munzalin da kake samun albashi mai yawa, to ka guji bashi. '' Bashi takura mutum yake. Yana hana ka damar yin tsare-tsare na dogon lokaci a game da rayuwarka Kana son ka yi ka yin kasada kana faduwa, kuma bashi ne zai sa ka yi ta kame-kame na ganin ka cimma burinka.''

Amfanin bashi ya dogara da abin da za ka samu

Har kullum idan za ka ci bashi to ka duba abin da za ka samu in ji Gil Eyal. ''Kawai ka lura ka ga cewa idan har za ka ranci kudi da ruwa na kashi biyu cikin dari kuma kana da tabbacin za ka samu kashi biyar cikin dari na kudin, za ka iya cin iya bashin da za ka iya samu'' ya ce.

Ya dogara ga al'ada

Jett Fein shi kuwa yana kallon lamarin bashin ne ta wata fuska daban. Ya ce, ''lamarin ya dogara da yadda kake kallon bashi. 'yan kabilar Tivi na Najeriya da ke Afrika ta yamma suna kallon bashi ta wata siga mai ban sha'awa da na taba gani: su s suna daukar bashi ne a matsayin wani abu mai kyau saboda suna ganin in har ka ci bashi to za ka samu alaka ta tsawon lokaci da mutane.''

Bashi na mayar da kai bawa

Wasu na ganin kamat ya yi ka guji bashi ko ta halin kaka. '' Bashi bauta ne,'' in ji Brian Fey. ''Gara ka mutu ba bashi a kanka da a ce ka mutu bawa. Phil Bradford ya kawo aya ce ma daga littafin Baibul wadda ke cewa, ''Mai arziki shi ke mulkin talaka, kuma mai cin bashi bawan mai bayar da bashin ne.''

Shi kuwa Amadasun Efe ya kwatanta bashi ne da kamar ace mutum ne ya goya kaya mai nauyi a bayansa kuma yana son hawa tsauni. ''Yawan girman bashin, yawan girman dutsen,'' kamar yadda ya rubuta, '' Da sannu za ka ga cewa nauyin da yake dawo da kai baya ya kai yadda ba za ka iya hawa tsaunin ba da kayan a bayanka, daga nan sai dai ka dawo baya ko ma ka fado kasa.

Za ka ga kowa yana ta wuce ka, saboda su ba sa dauke da wani kaya a bayansu, a takaice dai ba wani bashi a kansu. A daya hannun ta jiki da kua hankali ka zama bawan wanda ya baka bashin da ya dankwafar da kai. Duk wani tunani da za ka yi shi ne ta yaya za ka raba kanka da wannan nauyi na bayanka.''

Efe ya ce to a nan 'yanci wani abu ne na daban kuma. '' Ina kana cikin 'yancin kanka to kana cikin yanayi ne da za ka iya yin komai. Ba ka da wani tarnaki. Wuri ne da kai ke da iko.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The surprising downside to being debt free