Kayan da bai kamata ka sa ba zuwa neman aiki

Hakkin mallakar hoto Alamy

A lokacin da aka gayyace ka ganawar ɗaukar aiki, ka san irin kayan da ya kamata ka sa wadanda za su nuna kamala da sanin ya kamata. Ka san irin takalmin da ya dace ka sanya da riga da wando, kuma kada ka bar riga ƙirji a buɗe.

Kwararre kan daukar ma'aikata Reed Ellis, ya tuna da wani da ya halarci wata ganawar daukarsa aiki. Mutumin ya iya gaisuwa kuma ya kware wajen magana da mu'amulla. Sai dai kashe tufafin da ya sa ba su dace ba a ce ya halarci wannan ganawa da su.

Hakkin mallakar hoto iStock

Ellis ya ce, ''yadda ka nuna kanka da frko abu ne da ke da matukar muhimmanci wurin ganawa da kai idan za a tantance ka domin daukarka wani aiki, saboad haka tufafi da duk abin da ka sa na da muhimmanci sosai.''

Hatta mutumin da yake jin cewa yana da kwarewa a aikin da zai je a gana da shi domin daukarsa aikin, yakan yi fargabar wannan ganawa. Haka kuma abin da yake kara tayar wa da mutum hankali shi ne irin kayan da zai sa, da kuma wanda bai kamata ya sanya ba.

Zaben kayan da suka dace na halaratar ganawar aiki a da abu ne mai sauki, inda za ka sa kwat mai duhu, wadda a ko da yaushe tana dacewa. Amma a tsarin ayyukan zamani na yanzu, ka'idojin sun sauya. Wandon jins da 'yar karamar rigar zamani (t-shirt), su ne ma'aikata suka fi amfani da su, hatta shugabannin wasu kamfanonin ma za ka ga irin kayan da suke sa wa kenan.

Shugaban kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg, ya yi fice waje sanya irin wadannan tufafi kullum zuwa wurin aikinsa.

Mun mika tambayar irin kayan da ya kamata mutumin da zai halarci ganawar daukarsa aiki ya kamata ya sa, ta yadda za a dauke shi a matsayin wanda ya dace da aikin , ga wasu kwararru.

Steve Brown na wani kamfanin daukar ma'aikatan fasahar zamani da ke Landan (Empiric Do your research), wanda ya ce, kokari za ka yi ka samu wanda yake aiki a wani kamfnin dukar ma'aikata ka tambaye shi kayan da yake ganin ya kamata ka sanya idn za ka je ganawar nemn aikin wani kamfani na aiki iri kaza.

Idan kuma ba haka ba, sai ka tambayi sauran jama'a, ko kuma idan ka san wani wanda yake aiki a kamfninsai ka tambaye shi. Duk kuma idan kana ganin hakan bai yi ba, kana iya buga wa jami'in da zai gana da kai ko wanda zai dauki aikin, kafin lokacin ganawar. ''Ba za a hukunta ka ba saboda wannan binciken da ka yi,'' in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Shawarar Browon, ita ce, '' ka zabi kayan da za su fito da kai sosai, ka kure adaka. Idan wuri ne da ake tsammanin ku sa kananan kaya, sai ka sa kananan kaya na zamani na gani na fada. Idan kuma wuri ne da ke sa ran a gan ku cikin jinsi da 'yar riga ta gayu, to kana iya sanya kwat. Ka sni cewa gara a ce ka yi ado kamar ka kure adaka da ace adonka bai yi kai ba, duk inda za ka je ganawar.

Jon Lees, marubucin littafin How to Get a Job You Love cewa ya yi , sai ka duba kawai yadda kake son a ganka. Ba wai kawai ka kalli kanka ka ce ka yi shigar da adon da suka dace ba, a'a ka dauki kanka kamar dama kana aiki ne a wurin, amma kuma ka yi hankali da abin da ya kamata ka sa.

Ya ce wannan na nufin sanya kayan da suka dan zarta wanda ya kamata ace idan kana wurin aikin ka sa. Idan kana son ka kawar da wata fargaba ma game da kayan da za ka sa, kana iya sayo wasu sababbin kaya kafin lokacin.

Idan ka hallara a wurin ganawar, ka bar kwat da jakarta a zauren karbar baki na wurin, ka shiga wajen da 'yar ambulan dauke da takardunka (maimakon jaka), a ga kamar kai ma'aikacin wurin ne ma ba bako ba.

Gwendolen Andre ta kamfanin Professional Staffing Group da ke Boston cewa ta yi, a wurin da ake sanya kaya kusan kowane iri, kama daga shat da kwat da suwaita, wato wurin da babu wata ka'ida ta kayan da za ka sa, ta shawarci mutum da ya sa kananan kaya masu kyau.Ta ce, wannan wata dama ce da za ka iya sanya wasu kayayyakin na ado wadanda za su kara ma kyau (kamar sarka da dan karamin lakataye).

Wannan wuri ne da ba zai sanya ka wata fargaba ba, indai ba aikin da za a dauke ka na manyan jami'ai ba ne, to wannan shi ne za ka yi shiga ta sosai, ka sanya kwat.

Gabrielle Rossi ta kamfanin Whole Foods Market da ke arewacin California wadda a kamfaninsu kusan babu wani tsari na sanya kaya na musamman, idan ka yi shiga ta sosai sai a dauka za ka je wata ganawar daukar aiki ne.

Amma kuma duk da haka Rossi na ganin indi har za ka je neman aiki ne to kamata ya yi ka sanya kaya masu kyau ya fi dacewa. Ta ce bai dace ba ka sanya kaya kamar na zuwa motsa jiki, ko jins da 'yar karamar riga kamar suwaita ko kuma gajeren wando ba.

Kasancewar ta yi wa mutane masu neman aiki akalla 20 tambayoyin tantancewa, a shekarar da ta wuce, kusan a ce ta san komai. Babban abin da ke bata mata rai, shi ne misali mace ta zo da wandon jins tana cin chingam, da fitar da kirjinta sosai da sanya sarka da warwaro da zobuna da yawa, da farar riga ba singileti da kaya matsattsu sosai.

A kamfanin su Jennifer Medeiros Rodan + Fields na San Francisco, ma'aikatan kowane sashe sukan sanya kayan da suke so, misali jins, kuma ka ga an dauke su aiki, amma hakan ba yana nufin za ta ba ka shawar ka sanya jins idan za ka je neman aiki ba.

Ta ce zan so mutumin da zai je ganawara dukarsa aiki ya sanya kaya fiye da kima maimakon ya sanya wadanda ba su dace ba, domin ko ba komai yanayin yadda aka dauke a wannan lokacin zai iya yi tasiri kan fassarar da za a yi maka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. What not to wear to a big job interview