Kana koyar da 'ya'yanka juriya?

Mutumin da ke ganin ya wadatu da kansa, mai girman kai ba ya ɗaukar alhakin wata gazawa ko matsala. Domin shi a wurinsa a duk lokacin da wata matsala ta faru to fa laifin wani ne amma ba nashi ba.

Ga nazarin Sydney Finkelstein

Ko ka ga dan wasan sulun kankara na Amurka, Jeremy Abbott, a lokacin da ya fadi a lokacin wasan Olympics a Sochi, inda ya fadi ya buge da bango, ya rike kuibinsa yana nuku-nuku saboda zafi?

Kila kuma ka ga yadda ya yi ta maza ya tashi cikin dakika goma, ya kuma cigaba da gasar sulun, duk da irin halin da ya shiga na kunya da ciwo da kuma fargaba.

Duk abin da nake tunani dai a wannan lokacin shi ne, jaruntar da wannan yaro na ya nuna, cewa lalle kam shi jarumi ne.

A harkar kasuwanci akwai yadda muke kiran wannan kokari- juriya. Yawanci wannan shi ne sirrin sinadarin da ya raba mutanen da suka kai ga nasara da kuma taron mutane wadanda za su iya abin da ke bukata amma kuma su ba 'yan baiwa ba ne.

Idan likitoci za su iya bayyana wannan kalma ta juriya, dukkaninmu za mu so ta. Babban abin alfaharin dai shi ne kowannenmu zai iya rayuwa ta juriya a wurin aikinmu da ma sauran harkokinmu na yau da kullum, idan har muna son yin hakan.

Abu ne da zai iya kasancewa mai wuya, a wani lokacin ma za ka ga kamar ba za a iya cimma sa ba, amma kuma wannan shi ya kara masa muhimmanci da amafani.

Ga wata jarrabawar gaggawa: Idan har ka yi amanna da wannan bayanin na sama gaskiya ne, to za mu iya cewa kana da juriya fiye da yadda kake tsammani. Juriya na bukatar kwarin guiwa da karfin hali. Amma kuma kamar yadda shugabanci da dama yake, ci da zuci abu ne mai illa.

Farfadowa da murmurewa daga rashin nasara abu ne da ke bukatar cewa kai kanka ka yarda cewa akwai wata matsala, kuma kai ne ka haddasa matsalar.

Shi mutumin da yake ganin ya isa, karansa ya kai tsaiko, wanda kuma ke da girman kai ba ya daukar alhakin wata matsala idan ta faru.

A wurin irin wadannan mutanen duk wata matsala da ta faru, to fa su ba su ba ne da laifi, laifin wani ne. Mun ga irin wadannan misalai da dama a lokacin gasar wasan Olympics a Sochi.

Za ka ga 'yan wasan kwallon gora suna dora wa alkalin wasa laifi kan wata matsala, ka ga masu wasan sulun kankara suna korafi cewa kankarar ba ta da karfi, su kuwa masu horar da 'yan wasan tseren sulu suna dora alhakin rashin nasarar da suka samu a kan sabbin rigunan zamani na wasan da aka zaba wa 'yan wasansu.

Saurara: Sydney Finkelstein ya tattauna wanna kalma ta juriya da wani tsohon kwararren dan wasan sulun kankara

Amma ka kwana da sanin cewa ba a banza za ka san yadda wannan dabi'a ta koma-baya take ba. Bayan nazarin shekaru na matsaloli a kamfanoni da hukumomi a fadin duniya, idan akwai wani abu daya da na koya shi ne yakana da nuna gaskiyata a duk lokacin da aka samu kuskure, wannan shi ne abu daya tilo da za ka yi ka gyara gaba.

Kowa yana gamuwa da rashin nasara amma kuma ba kowa ba ne yake farfadowa daga wannan koma baya ba, har ya yi nasara.

Muhimmancin abin shi ne ka koyi darasi daga rashin nasara maimakon ka bari wannan koma baya ya dankwafar da kai.

Saboda haka yawancinmu muna da dabi'ar binne kanmu a kasa idan muka fuskanci bayani ko wata magana da ba ma son ji.

Misali Ron Johnson, shugabn kamfanin JC Penney, ya dukufa wajen bunkasa wannan kamfani, har ya zama ba ya la'akari da duk alamun da ma'aikata da masu sayen kayan kamfanin suke nunawa na kalubalantar tsauraran matakan da yake dauka na sauya tsarin kamfanin.

Shi kam ya gwammace ya yi watsi da duk wasu maganganu da surutai na masu adawa da shi, a maimakon haka ya gwammace ya saurari wadanda suka yadda da tsarinsa.

To wannan dai ba yadda ya kamata a tafiyar da harkokin kamfani ba. Yana da kyau ka saurari duk wani bayani na abin da ba ka sani ba, ko ma abin da ya fi ka yi duk abin da za ka yi ka san abin da kake fatan ba gaskiya ba ne, wannan ita ce alamar shugaba mai juriya.

To in ba haka ba ta yaya za mu dauki dabarun da za mu sauya idan ba mu san matsaloli ba?

Asalin hoton, Robert CianfloneGetty Images

Bayanan hoto,

Jeremy Abbott na Amurka ya tashi ya cigaba da gasar sulu bayan da ya fadi a wasan Olympics na Sochi na 2014, har ya yi nasara

Kalubalen juriya ba wai kawai ya shafi rayuwarmu ta aiki ba ne. Idan kamar ni kake, to zai kasance kana da tunani a kan inda mutum ke samun dabi'ar juriya, kuma ka duba ka ga ko muna taimaka wa 'ya'yanmu ta yadda wannan dabi'a za ta zama wani ginshiki na rayuwarsu.

Ina ganin lalle akwai abin da zai sa mu damu. Idan iyaye suka taimaki 'ya'yansu fita daga wata matsala ko wani yanayi na kalubale, kama daga yi musu aikin da aka ba su na makaranta su yi a gida, zuwa cike takardarsu ta shiga makaranta, to wadannan iyaye fa ba taimakon 'ya'yan suke yi ba.

Iyaye suna son kare 'ya'yansu daga rashin nasara, amma kuma ba su san ta hakan suna hana 'ya'yan nasu damar koyo da sabawa da kalubalen rayuwa ne ba, wanda kuma wajibi ne ba ga rayuwarsu ba kadai hatta ga aikinsu a gaba.

Idan muka fifita kare kimar 'ya'yanmu fiye da sa su a hanyar da za su koyi kalubalen rayuwa, to a rashin saninmu muna koyawa matasanmu yadda za su zama malalata ne a rayuwarsu, ba dadi ba ragi.

Kuma hakan ko kadan ba zai taimaka musu ba a wannan duniya da ke cike da kalubale da gogayya, inda yawan rashin nasara ke ta karuwa, maimakon raguwa.

Misali idan ka duba jerin kamfanoni 100 da suke kan gaba a duniya tsawon lokaci, za ka ga yawan kamfanonin da suke yin kasa ko ficewa daga jerin na karuwa.

Wannan na nufin yayin da a cikin shekara 25 da ta wuce kashi 20 cikin dari na manyan kamfanonin da ke cikin jerin guda darin suka fice daga rukunin, bayan shekara goma, to a yanzu kuwa kashi 30 ne cikin dari na kamfanonin suka fice daga jerin a wani wa'adin na shekara goman.

Kuma yadda kamfanoni ke durkushewa haka muke rasa ayyukanmu. Tuni yawancinmu muke tunanin sauya aiki a lokuta da dama, to amma hakan ba zai yuwu ba sai mun sauya sana'ar da muka kware a kanta baki daya, kila fiye da sau daya.

Wannan shi ya sa a yau ya zama wajibi mutum ya kasance a kullum yana koyon wani sabon abu, da kuma kulla mu'amulla. Ita sabuwar sana'ar ma'anarta ko da yaushe kana da wani abu da za ka gabatar, ita kuwa mu'amullar ana son ka rika kulla ta ne domin ya kasance kana da masaniyar duk wani aiki da za a nemi ma'aikata.

Juriya ba tana nufin idan ka fadi ka iya tashi ba ne kadai, tana nufin a shirye kake da duk abin da ya zo maka. Ko da kuwa ba ka san ko menene ba.

Gamuwa da matsala da faduwa a yayin sulun kankara a gaban miliyoyin 'yan kallo wannan ba wani sabon abu ba ne, illa kalubale ne na gwagwarmaya da gogayya na wurin aikin da ke cike da bukatar jajircewa.

Tashi ka ci gaba da wannan tsere na sulu ba abu ne da kake da zabi a kansa ba, abu ne da ya zama wajibi.

Me kake gani? Shin muna koya wa 'ya'yanmu juriya?

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Resilience: A Lesson From Sochi