Ya za ka kare kanka daga shiga tsaka-mai-wuya?

Hakkin mallakar hoto iStock

Idan ba za ka iya jure ɗabi'ar mutumin da ke mu'amulla da kamfaninku ba wanda kuma shi ne babban kwastomanku, wanda yake wani abu na keta doka to ya zama dole ka ɗauki wani mataki.To amma ya za ka bullo wa lamarin?

Tambaya: Ɗaya daga cikin manyan 'yan kasuwar da ke mu'amulla da kamfaninmu wato kwastomanmu yana wasu harkoki na kasuwanci tsakanin ƙasashe waɗanda suka saba doka, waɗanda kuma ba shakka sun saɓa dokokin aikinmu.

Na gaya wa shugabana a wurin aikin, amma ya yi watsi da damuwar da nake nuna wa a kan lamarin. Ina tsoron cewa idan na yada maganar za ta iya shafar aikina, domin shugaban nawa ba zai sake amincewa da ni ba( domin shi kadai na gaya wa maganar).

Haka kuma ina fargabar cewa idan ban kai maganar gaba ba, akwai yuwuwar cewa lamarin zai iya kai mu gidan yari ko kuma a bata mana suna. Me ya kamata na yi?

Amsa: Wane tabbaci gare ka cewa abin da mutumin yake yi ya saba wa doka? Ka tuntubi wani lauya a kamfaninku ko a waje kan lamarin ka ji ko ya saba wa dokar?

Ka kalli abin ta fuskar dokokin kasashen duniya, ka duba ka ga ko abin da yake ya saba dokar kasar da yake yinsa. Ko kuma abu ne da aka saba yi a harkar kasuwancin wanda kuma ba ya bukatar binciken kwakwaf a wani wurin?

Dole ne ka samu amsar duka wadannan tambayoyi kafin ka dauki matakin da idan ka dauka ka riga ka dauka kenan ba za ka iya sauya ba, wanda kuma zai iya shafar matsayinka a kamfanin.

A gaba kuma sai ka shiga intanet ka duba duk wata doka da ke bayar da kariya ga wanda duk ya kwarmata wani abu na rashin gaskiya, wadda ta bambanta daga kasa zuwa kasa da kuma ma'aikata zuwa ma'aikata.

Ka tabbatar ka yi amfani da wayar salula ko wata na'ura ta tafi-da-gidanka ko kwamfuta ta kashin kanka, maimakon kwamfutar wurin aikinku ko kuma intanet din wurin aikin naku.

Ka tabbatar ka adana duk wata magana ko tattauna wa ko musayar wasika da ka yi da shugaban aikin naka, da kwastoman naku da kuma duk wani da kuka yi maganar da shi.

Ka bugo dukkanin takardun abubuwan da suka wakana tsakaninka da wadannan mutanen ka adana su ko kuma ta tura wasikun email din zuwa email dinka na kanka ba na kamfanin ba, idan har dokokin kamfanin sun yarda da haka.

Idan ka samu kanka a gaban shari'a da mutumin ko hukuma ko da kamfanin naku a kan lamarin za ka iya gabatar da wadannan takardu a matsayin shedar abin da ka sani.

Ka yi tunani a kan matakin da shugabanka na wurin aikin ya nuna da farko a tsanaki. Ka san cewa shugaba naka ya dauki abin a matsayin wani abu da bai saba doka ba, in ji farfesa Maurice Schweitzer na jamia'r Pennsylvania.

Domin ka tabbatar ko kana bin abin yadda ya daidai, malamin ya ba da shawarar da ka tuntubi kadan daga cikin wasu manyan shugabannin wurin aikin naku ( a boye ba tare da sun san ko wanene kai ba), idan har za ka iya hakan.

Idan har sun yarda cewa bai dace ka yarda da wannan abu da mutumin yake yi ba ko kuma kada ka yarda abin ya shafe ka, to sai ka dauki mataki.

To a wannan lokacin sai ka kara komawa wurin shugaban naka, ka nuna masa ya san cewa barin lamarin ya ci gaba abu ne da ya fi karfin ikonka, kuma ka kawo shawarar matakin da ya kamata a dauka, in ji Schweitzer.

Idan a wannan karon ma shugaban naka bai dauki maganar taka da muhimmanci ba, to kana bukatar zuwa sama (shugaba na gaba). Da fatan cewa kana da wani shugaba wanda ka yarda da shi, wanda za ka iya tunkara domin neman shawara. Idan kuma babu, to sai ka yi karfin hali ka nufi wurin wani babban jami'i wanda ya yi fice da gaskiya.

Kana da gaskiya cewa ba lalle ku kare lafiya tsakaninka da shugaban naka ba a kan lamarin. To amma dole ne ka kare kima da mutuncinka da kuma sana'arka, ko da kuwa ka rasa wannan aikin ko an tilasta maka barinsa.

Ka yi tunanin rayuwarka a gaba, in ji Schweitzer, wanda ya kara da cewa, ''Zai fi maka wuya ka samu wani aikin idan shari'a ta same ka da laifin aikata abin da ya saba wa doka.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The art of confronting unethical client activities