Yadda za ka samu aikin da ba ka tsoron Litinin

Hakkin mallakar hoto Alamy

Litinin rana ce ta mako wadda yawancin ma'aikata musamman masu zuwa ofis suka tsani zuwanta tun daga daren Lahadi saboda za su koma bakin aiki. To ta yaya za ka samu aikin da ba ya tattare da wannan fargaba?

Sydney Finkelstein ta yi mana nazari

Karshen rayuwar karatu da jarrabawa ce ta miliyoyin daliban jami'a. Ka kama hanyar samun diploma, kuma ka fara hawa hanyar ainahin rayuwa a matsayin ka na wanda ya kai munzalin kula da kansa.

Inda a yanzu kai ne shugaba da kuma direban rayuwarka. Wannan babban ci gaba ne daga matsayin wanda iyayensa da malamansa na jami'a ke gaya masa abin da zai yi a kullum.

Kai ne da iko yanzu. To, me zai faru gaba?

Zabin sana'ar da ta ke da damarmaki da yawa ka iya sa ka cimma nasara sosai a rayuwarka. To amma mu nawa ne za mu yi tunanin zabar wata sana'a wadda ke bunkasa, amma kuma ba ka da sha'awarta?

Aiki yana da muhimmanci a rayuwarmu- ka tsaya ka yi tunanin yawan sa'o'in da muke yi a wurin aiki ka kuma kwatanta da wasu abubuwan kuma da muke yi, wannan zai sa dole ka zabi abin da ka fi so.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Idan ka san inda ka fi ƙwarewa neman aikinka zai fi zama cikin sauƙi, kuma za ka fi farin ciki idan ka samu aikin

Sana'ar da ka zaba ka yi a rayuwarka za ta yi tasiri sosai a kan nasarar da za ka samu a rayuwarka. Duk da cewa yawancin mutane za su iya yin nasara a wannan sana'a, hanyar da ka dauka ta samun nasara a wannan fage na da alaka da nasara da za ka samu ko akasinta, kamar yadda komai zai iya yi maka.

Amma hakan na nufin kenan za ka dauki hanyar yin wata sana'a wadda ba ka da sha'awa, saboda kawai sana'a ce da ake samu sosai?

Zaben hanyar da ta dace

Ka sa a ranka cewa nasara a rayuwa ta dogara ne ga dan wani abu mai sauki: Wasu sana'o'in suna bunkasa da sauri sosai ta yadda za ka ga ana samun damarmaki baja-baja a cikinsu. Misali akwai sana'o'i na zamani da suka danganci fasaha a fannin samar da kayayyaki ko makamashi da makamantansu.

Da zarar ka fahimci inda baiwarka take, to ka san inda za ka nufa kai tsaye da neman aiki.

Za ka ga duk sana'ar da take bunkasa tana jan mutane, ana ta tururuwa kanta, ta yadda zuwa wani lokaci za ka ga ana samun gogayya, wanda hakan kuma zai rage damar samun aiki a cikinta.

Saboda haka idan ba ka da tabbas inda damar samun aikinka take da kuma kwarewarka, me za ka yi?

Ka yi gaskiya

Gaskiya ne cewa yawancin mutane sun fi son yin abin da suka fi kwarewa a kai. Ina matukar kaunar kirkiro sabbin hanyoyi kuma in gaya wa mutane su. Wannan shi ne ya kai ni ga koyarwa a Jami'a, kuma a kullum ina godiya kan irin nasarar da nake samu a wannan fanni.

To kai me ka kware a kansa? Me ka iya; wane aiki kake jin dadin yi. Ka rubuta su, sannan kuma ka yi wannan tambayar: A wane irin aiki ake bukatar wannan kwarewar? Sabanin haka, idan ka samu kanka a aikin da ba a darraja kwarewarka sosai, ba rashin farin ciki ne kadai zai dame ka ba, zai kasance kana ma bata lokacinka ne mai muhimmanci.

Idan ka har ka kware wajen mu'amulla da mutane me zai sa ka zauna a gaban kwamfuta kullum kana shiga shafukan sada zumunta da muhawara?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Za ka ga abin kamar me sauki ne, amma yana da matukar tasiri. Da zarar ka fahimci inda baiwarka take, za ka samu saukin neman aiki wato ka san inda za ka nufa da bukatarka ta neman aiki, kuma za ka fi samun kwanciyar hankali idan ka samu aikin.

Sabanin haka ma zai iya tasiri. Idan kana da sha'awa kan wasu sana'o'i kamar kiwon dabbobi ko aikin hakar mai, to sai ka mayar da hankalinka wajen koyon yadda ake yin abin, ta yadda za ka yi fice a kai, domin a gaskiyar lamari duk yadda wata sana'a take burge ka, ba ta yadda za a ce za ka iya yinta haka kawai ba tare da ka dukufa koyonta ba, har ma ka yi fice a cikinta.

Ka zama mai dabara

To idan kuma ya kasance ba ka da tabbas a kan abin da kake bukata fa, ko abin da kware a kansa ko wanda kake son yi fa? Wannan shi ne yadda mutane da yawa suke a lokacin da suka gama makaranta (jami'a), kuma ba su yi wasu ayyuka ba da yawa. Babu wata matsala da hakan, abin da kake bukata shi ne ka san matakan da ya kamata ka dauka a gaba.

Sana'ar da kake son yi ba wani abu ba ne da ya fi karfinka.

Shawarar da zan ba ka a nan ita ce ka yi dabara ka koyi iya sana'o'in da za ka iya, wanna na nufin shiga wata kungiya ko zuwa koyon wata sana'a a lokacin da kake karatu.

Yawan sana'o'in da kake yi shi zai sa ka san abin da ka fi kwarewa ko baiwa a kai. Yadda za ka yi shi ne a kowace shekarar karatunka a jami'a ya kasance cewa akwai wata sana'a da kake koya. Kuma idan bayan ka gama makarantar ka ji cewa ba ka gamusu ba, to sai ka ci gaba da jarraba wasu sana'o'in.

Idan a haka ka dace ka gano sana'ar da ka fi so, to sai ka fara mayar da hankali a kanta, amma kafin ka gano hakan, ci gaba da jarraba wasu fannonin karin dama ce ta sanin abubuwan da kake so da kuma baiwa a kansu.

Duk abin da kake yi kada ka tsaya a gefe-gefe kana tsammanin ka fahince shi cikin sauki, ka kutsa cikinsa sosai sai domin ka faimce shi da kyau.

Ka samarwa kanka lokacin yin hakan, kada ka manta fa cewa kai ne jagoran rayuwarka, wajen nema wa kanka aikin da kake kaunar yi.

Ka zama mai basira

Akwai wani abu guda daya da ya rage idan har kana son sama wa kanka tarin zabin sana'o'in da za ka dauka. Ka bayar da fifiko a kan sana'a ko kwarewar da ake amfani da ita a duniya yau da kuma inda duniyar take tafiya.

Wannan kwarewa ce ko ilimi da za a iya amfani da shi a kusan dukkanin ayyuka, wanda kuma da wuya a yi shi da na'ura, domin hakan zai kara wa ilimin ko kwarewar daraja, kuma za a rika nemanka duk inda ka nufa.

Kamar yadda rahoton taron tattalin arzikin duniya a kan yadda ayyuka za su kasance a gaba, wanda aka yi a watan Janairu na 2016, wadannan manyan ayyuka ko kwarewa sun hada da ilimin warware wata babbar matsala mai wuya, da ilimin tunani mai zurfi, da ilimin kirkira, da lura da iya kula da mutane da makamantansu.

Babban sakon da nake son ka sani duka a nan shi ne: Aiki ko sana'ar da za ka yi a rayuwa ba aba ce da ta fi karfinka ba. A gaskiya ma daya ce daga cikin abubuwa mafiya muhimmanci da kake bukatar kulawa da su sosai a matsayinka na jigo ko shugaban rayuwarka.

Idan har za ka sa daren ranar Lahadi ya zama daidai da daren ranar Juma'a (lokacin da ma'aikata suka fi murna saboda hutun karshen mako) za ka san cewa ka yi nasara.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to find a job with no Sunday night blues