Barci ba sai da ƙwayoyi ba

Kerstin Schneiderbauer, wadda ke aikin ƙididdiga ba ta iya yin barci yadda take so. Idan da akwai tarin ayyuka a gabanta sai ta yi ta tunanin waɗannan ayyuka da za ta yi har cikin dare lokacin da ya kamata ta yi barci.

Har cikin dare za ka ga cewa idan ba wani aiki da aka ba ta ta yi a gida take yi ba, za ka ga tunaninta yana kan aiki na gaba ta yadda zai bullo mata, wanda hakan ya hana ta barci.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ɗan barcin minti 30 a lokacin aiki na da amfani

A lokacin da wata kawarta ta ba ta shawarar samun wata kwararriya da za ta koyar da ita yadda za ta iya samun yin barci da kyau, da farko ta ki yarda da hakan. ''Ni ina ganin me mutum zai yi da wani kwararre me bayar da shawara kan barci? Na yi ta yi wa mijina magana a kan lamarin. Amma kuma na ci gaba da yin haka tsawon shekara daya da rabi,'' in ji Schneiderbauer, wadda ke zaune a kusa da Vienna babban birnin Austria.

Tana ganin wannan kwararre kan barci ba abin da zai yi mata illa ya ba ta jerin abubuwan da zai ce ta yi da kuma wadannan za ta bari.

Amma sai ta yi mamaki darasin farko da ta yi da kwararriya kan barci Christina Stefan ba yadda ta yi tsammani ba yake, ya ba ta mamaki. Darasin ya kasance kamar na aiki da rayuwa da kuma barci an dunkule su wuri daya.

Stefan ba tana gaya wa Schneiderbauer abin da za ta yi ne ba, tana yi mata tambayoyi ne game da kanta da ma iyalanta. Babbar matsalar Schneiderbauer dai ita ce ba ta iya tsayawa da aiki. Bayan darasi goma da suka yi da kwararriyar sai barcinta ya inganta.

Daga nan ta koyi yadda za ta iya zama cikin tsanaki hatta da daddare idan ba ta yi barci ba, ta kuma dena wasu dabi'u da take yi idan ta ci bashin barci.

A takaice dai Schneiderbauer sai ta fara rubuta dukkanin ayyukan da za ta yi na gobe tun da yamma kafin washegarin, wanda hakan ya bata damar tsara ayyukanta yadda ya kamata, kuma ta daina shigo da maganar damuwarta ta aiki a yayin hirarta ta yamma.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Tunanin ƙirga tumakai na ɗaya daga dabarun samun yin barci

Kusan rabinmu ba ma barci sosai: kashi 45 cikin dari na al'ummar duniya na fama da matsalar barci wadda ke barazana ga lafiya da da yanayin ingancin rayuwarmu, kamar yadda wani nazari da aka yi a shekara ta 2008 ya nuna.

Kuma illar da hakan ke yi wa lafiya na da girma sosai. Rashin barci da kyau ka iya haddasa wa yara teba ko kiba da kuma sauran matsaloli da suka shafi tunanin dan adam, kamar damuwa a bangaren manya.

A Burtaniya kadai ana rubuta wa mutane magungunan barci sama da miliyan goma a duk shekara, kamar yadda wani rahoto na hukumar lafiya ta kasar ya bayyana.

A Amurka an bude kananan asibitoci na kula da matsalar barci sama da 2,800, kuma kamar yaddda kamfanin da ke fitar da kididdigar ci gaban kamfanoni a duniya IBIS ya bayyana, asibitocin sun samu cinikin kusan dala bliyan bakawai da miliyan dari daya.

Sannan kuma an yi cinikin kayayyakin taimaka wa mutum ya ji dadin barci kamar su katifa da matashin kai da sauransu, da magungunan sa barci na gargajiya da na shagunan sayar da maganai na kusan dala 58 a shekarar 2014.

Steven MacGregor wanda ya kirkiro Leadership Academy da ke Barcelona kuma kwararre a kan lafiyar manyan ma'aikata ya bayyana barci a matsayin wani muhimmin abu na aiki wanda ya wajaba koya kuma a kware a kansa, kuma aiki ne da ke bukatar a bas hi muhimmancin gaske a kullum.

Ya ce, irin ayyukan da rashin barci ke shafa shi ne tunanin babban jami'i, kamar yadda za a bullo wa da wata matsala ta rashin tabbas.

Stefan ita ma tana ganin barci a matsayin wani muhimmin abu na jami'ai wanda zai iya taimaka musu daukar matakin da ya dace da kuma iya jure wa damuwa.

Amma kuma duk da haska yawancin mutane ba sa neman taimako idan suna fafutukar yadda za su samu hutu(barci). Masu shirya ranar barci ta duniya, yawancin matsalolin barci larurori ne da za a iya karewa ko magani, amma kuma duk da haka kashi daya bisa uku na masu matsalar ne kadai suke neman taimakon kwararru.

Dan barci

Dadin abin shi dai barci ba abu ne da sai a wani wuri na musamman kamar dakinka na kwana za a yi shi ba. Dan barci na 'yan mintina kadan tsakanin wannan taro da wancan shi ma yana da amfani.

Hukumar lura da barci ta Amurka ta ce dan barci na minti 30 zai iya taimaka maka, ka wartsake ka ji garau a aikinka ba tare da ka takura wa lokacin barcinka na dare ba.

Sa kanka barci

Mai taimaka wa Schneiderbauer kan matsalar tatat ta kasa barci, ta ba ta shawara da ta kirkiri wata siffa a zuciyarta wadda za ta rika bujuro mata da hutu, kuma ta iya bujuro da siffar a duk lokacin da take bukata.

An bukaci Stefan wadda ta mimmike a kan doguwar kujera a kwance a ofishinta a Vienna, da ta bayyana a rubuce da kuma a hoto kyakkywan yanayi na hutu.

Schneiderbauer ta bayyana wannan yanayi na hutu a matsayin lokacin da take jin tana linkaya a tafkin wanka, da lokacin da take jin jikinka sakayau ba nauyi, kuma sai karar numfashinta kawai take ji.

Ta ce to a duk lokacin da take son jin wannan yanayi na hutu, to sai ta shiga wannan tunani na tanayin wanka a tafki, ga ta ga kifaye a kusa da ita, ta yi shiru ba ta jin karar komai sai ta numfashinta.

''Ba wannan yanayin nake siffantawa ba kadai, ina kokarin har ma na ji shi. Yanzu abin ya zama jiki a wurina. Yanzu cikin 'yan mintina kadan nake iya jin kaina a wannan yanayin. Idan ina son na ji.''

Kudurin samun sauyi.

Kwararre shi kadai ba zai iya sa mutum ya rika barci ba. Dole ne ya kasance kana da kudurin yin hakan, in ji Sibylle Chaudhuri kwararriya mai bayar da shawara da taimaka wa wadanda ke fama da matsalar barci, wadda ke zaune a Ratinghem a Jamus.

In dai har kana son samun nasara a kokarinka na maganin matsalarka ta kasa barci to lalle sai ka sa kudurin hakan a zuciyarka, domin koyarwa ta danganci sauyi ne, shi kuwa sauyi abu ne mai wuya a wurin yawancin mutane in ji Chaudhuri

Hakkin mallakar hoto Getty
Ganin haske kan matsalar

Wani bangare na cimma wannan buri shi ne ka kalubalanci al'adunka. ''Yawancin mutane suna daukar barci a matsayin wani abu da ke faruwa kawai a jikin mutum, kuma dole sai ya faru, duk yadda ka yi da jikinka.

To ian ganin abu mafi muni shi ne ka rena barci, kamar zuwa wurin motsa jiki ne, dole ne mu motsa jikinmu domin mu iya barci da kyay, in ji Chaudhuri

Ta kara da cewa sirrin yin barci mai dadi shi ne sauya yanayin rayuwarka. Yawanci mu muke hana kanmu barci ta hanyar munanan dabi'unmu. Babban abu mai wuya shi ne yadda mutane za su sauya dabi'unsu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to induce sleep without drugs