Za ka iya zaburad da ƙwaƙwalwarka ta ƙara aiki?

Hakkin mallakar hoto iStock

Sanya wa kaina wa'adin kammala wani aiki ba abu ne mai sauƙi ba. Duk yawan lokacin da na ɗiba wa kaina na yin wani aiki a ƙarshe sai na zo ina ta fama kada lokacin ya ƙure ban gama ba.

Ga nazarin Alina Dizik

Na san cewa ina da abubuwa da dama masu sanya ni shiririta na kasa yin aikin da ya kamata na yi a kan lokaci. Amma a kwanannan ina jarraba wata dabara ta rage yawan lokacin da nake diba wajen kammala wani aiki.

Ma'ana ina takura kaina na kammala aikin da na saba yi a kasa da lokacin da na saba yinsa, domin ya kasance ina aiki fiye da yadda na saba wato na kara kwazo, kuma na rage shiririta.

Misali wayar da zan yi a cikin sa'a daya a da, yanzu cikin minti 30 nake yinta. Ko wankin da zai dauke ni minti 30 yanzu ina yinsa a cikin minti 10, kuma da zarar lokacin da na ware na kammala aiki ya yi sai na kama aiki na gaba.

Hasali ma ina saita kararrawar wayata ta yadda za ta tuna min da zarar lokacin kammala aikin da nake yi ya yi, kuma na ci gaba da wanda na tsara yi na gaba.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Ba za ka iya gama abubuwan da ke gabanka ba

A wurin ma'aikata da dama gajarta lokacin da suke dauka su yi wani aiki da suke yi a kullum, ko a ko da yaushe wata dabara ce ta bunkasa aikin nasu, in ji Craig Smith wanda ya kafa kamfanin Trinity Insight, wani kamfanin Intanet a Philadelphia.

A shekarar da ta wuce Smith ya gwada rage wa'adin kammala wani aiki da aka ba wasu ma'aikata 17. Sai ya kasance dadaddun ma'aikatansa sun iya kammala aikin a cikin sabon wa'adin da aka diba musu. Ya ce, ''idan ka saba da aiki sosai to za ka fi iya kammala shi da wuri, ko da an rage maka lokacin da aka saba ba ka.''

Sai dai ya ce, idan ana maganar aiki ne da ake maimaitawa a ko da yaushe wajen aiwatar da shi ba wai abin da ya kunsa ba, misali bincike, yin tambayoyi da rubutu da gyara labari ko rahoto, sai abin ya zama wani sabo a kusan a ko da yaushe za ka yi shi, ba abu ne mai sauki ba kamar yadda na gano.

A tsari za ka iya rubuta duk abubuwan da kake son yi a rana, da lokacin da ka ware musu dan takaitacce. To amma dukkaninmu muna ganin yadda abin yake kasancewa, ba lalle ba ne mu iya aiwatar da su kamar yadda muka tsara.

Matsalar ba ta wa'adi ba ce, ta yadda ka tsara aikinka ne

An gano cewa matsalar da muke gamuwa da ita ba wai ta sanya wa'adin kammala abu ba ne, ta yadda muke yi wa kanmu dabara ne cewa ga yadda za mu gama aiki ba tare da lokaci ya kure mana ba.

Akwai dabarar yadda ake sanya dan gajeren wa'adi, amma kuma abin ba shi da sauki kamar yadda na yi tsammani.

Hakkin mallakar hoto iStock

Akwai amfani mai yawa na sanya gajeren wa'adi daidai, Bradley Staats, farfesa a jami'ar North Carolina Kenan-Flagler a Amurka ya gaya min a yayin wata hira wadda na ware wa minti 25 (wadda da a baya ne minti 30 zan ware mata).

Staats ya ce, ''ta hanyar yi wa kanmu iyaka, muna tilasta wa kanmu kammala aikin, kuma za mu iya rarrage abubuwan da ba su zama dole ba, sannan mu bi gajeruwar hanya indai har babu wata matsala a tattare da yin hakan.''

Kuma ba shakka sanya takaitaccen wa'adi a kan aiki zai iya sa ma'aikata natsuwa. Farfesan ya kara da cewa, ''watakila muna rena amfanin da muke samu daga hakan.''

Tsara ayyuka gaba daya na takaitaccen wa'adi, na dakushe kokarin ma'aikaci a can gaba, saboda ma'aikaci ba ya samun dan lokacin da za a iya cewa na shiririta, wanda zai ba shi damar yin tunani na basira da samo mafita kan wata matsala. In ji malamin jami'ar.

Hanya mafi kyau

Samun matsaya ta tsaka-tsaki ita ce mafita, kamar yadda Ryan Holiday, kwararre kan harkokin sadarwa wanda ke Austen, wanda kuma ya wallafa littafin 'The Obstacle Is the Way: The Timeless Art of Turning Trials into Triumph'.

Holiday na kokarin raba lokacinsa tsakanin rubuta ayyukansa na yau da kullum na tafiyar da wurin aikinsu. Tsarinsa gaba daya ya dogara ne a kan tsara aiki cikin takaitaccen wa'adi.

Idan yana aiki daga gida Holiday, yana daukar kusan rabin rana yana ayyuka masu tsawo, wadanda suka hada da rubutu ko nazari, ba tare da sanya wani wa'adi na tilas ba.

Bayan cin abincin rana,sai kuma ya mayar da hankalinsa kan 'yan takaitattun abubuwa, kamar waya da taruka da kuma aika amsoshin wasikun email da ya samu cikin wa'adin minti 30.

Aiki a kan abubuwa mafiya muhimmanci da safe, na ba shi damar yin ayyuka masu dan gajeren wa'adi wadanda ya tsara. Sanya wa ayyukanka takaitaccen wa'adi na sa ka ji ka gamsu (yadda za ka ga kana ta kammala ayyukan da ka sa a gaba).

Abu mai muhimmanci a nan ba wai shi ne kawai ka ga ka kammala aikin ba. Kafin ka sanya dan takaitaccen lokaci ko wa'adi a kan abu, ka nazarci lokacin da ake ganin aikin zai iya dauka.

Tun da yawanci kusan aiki daya muke yi, maimaita abubuwa muke yi kullum, sanin wa'adin da za ka iya yin aiki abu ne mai sauki. Staats ya ce abin da ya dace shi ne sai na sanya wa'adin wajen yin mafi muhimmancin aikin, daga baya na yi amfani da lokacin da ba wani muhimmin aiki zan yi ba in karasa aikin da na ci karfinsa.

Ba shakka maganar ko ka sanya takaitaccen wa'adi ma tun da farko tana da 'yar sarkakiya. Idan ka san yadda aikin a karshe zai kasancewa ,to yana da kyau ka sanya takaitaccen wa'adi, in ji Staats.

Ya ce, ''mutum yana bukatar ya san abin da ya ke son ya cimma, domin ya iya sarrafa lokacin da ya warewa aikin yadda ya kamata.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Can you really trick your brain to work more efficiently?