Raba kanka da damuwa kafin damuwa ta raba ka da kanka

Hakkin mallakar hoto Daniel Hambury Getty

Damuwa, tsoro, fargaba. Karanta waɗannan kalmomi kaɗai zai iya sanya ƙirjinka ya ɗaure ka rasa ta yi. To yanzu ka yi tunanin abin da kowacce kalma a cikinsu za ta iya yi ga aikinka.

Wadanda suke da raunin zuciya da tsoro za su iya manta abubuwan da suka sani, ko su yi hayaniya da abokan aikinsu ko kuma su samu kansu a kan hadarin kamuwa da bugun zuciya.

Mafita? Akwai hanyoyin da za ka bi domin maganin damuwa ko fargaba ko tsoro, har ma ka sauya su su zama alheri a aikinka.

Manyan kwararru masu mu'amulla da shafin mu'amulla tsakanin ma'aikata na intanet LinkedIn sun tattauna hanyoyi na dabara kan yadda zai iya tafiyar da rayuwarsa ba tare da fargaba ko tsoro ko damuwa sun yi tasiri a kansa ba.

Ga abin da wasu daga cikinsu suka ce:

Gretchen Rubin, marubuciyar "The Happiness Project" and "Happier at Home" Idan tana cikin yanayi na zakuwa ko damuwa tana ba wa kanta hutu ne daga aikin da take yi. Ta ce, "idan kana jin abu ya dame ka, ka tsara wa kanka wani dan hutu, ka sarara," kamar yadda ta rubuta a shafin a kasidarta mai taken 'Feeling Stressed Out? Find a "Comfort Food" for Your Mind.

Abin da take yi shi ne wani lokaci sai ta dauko littafin adabi na yara. Wani lokaci kuma ta taba tafiya sinima da rana.

''Mutane kowa da abin da yake yi, girki ne, sahar ko goge-goge, ko wasa da 'yar kyanwarka ko karenka, ko wasan bidiyo ko wasan kwallon kwando da dai duk wani abu da za ka iya yi da zai debe maka kewa daga wannan damuwa. Idan za ka iya samun wani abu da za ka yi wanda sa ka motsa jikinka, ko ka fita waje ko ya sa ka hadu da wasu muitane wannanzai fi.''

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Muhimmin abin shi ne ka kawar da zuciyarka daga abin da yake damunka. Rubin ta ce. ''Ta hanyar jinjina wa kanka, za ka sa ka ji dadin kanka, sannan kuma za ka karfafa kanka ta yadda za ka iya fitar da kanka daga duk wani yanayi na damuwa ko mai wahala.''

Ilya Pozin, babban jami'in kamfanin Open Me:

Kana cikin damuwa saboda ka kasa kammala abubuwan da ke gabanka a lokacin ranakun aiki?

Ya ce Lahadi ka iya zama mafitarka in ji Pozin a kasidarshi mai suna 'Why Productive People Work On Sundays.'

Ya ce, Litinin yawanci rana ce da kusan kake kokarin kammala ayyukan da suka kai ka har karshen mako, galibi za ka tarar kana da tarin wasikun email da abubuwan da ke bukatar ka mayar da hankalinka sosai a kansu da zarar ka shiga ofis a ranar.

Domin maganin irin wannan yanayi na aiki da zai dame ka sai na tsara yadda nake wasu ayyuka a duk ranar Lahadi domin na amu damar shiga satina ba tare da wani abu a gabana ba.''

Ka shirya wa makon da kyau ta hanyar gamawa da 'yan kananan abubuwan da ke gabanka. In ji Rubin ''idan kana da wani babban aiki a gabanka da za ka fara ranar Litinin, idan ka fara da 'yan kananan tun ranar Lahadi hakan zai sa ka samu safiyar cikin sauki.''

Za kuma ka iya duba wasikunka na email, ka shiray yadda za ka tunkari makon da ke tafe, ka tabo wasikun email din da ka bari ba ka kula da su ba. Amma kuma fa ka lura ka da ka mayar da ranar Lahadin ta zamar maka ranar da kowane mako za ka rika kokarin yin duk ayyukan da a baya ka guje su.

Sauran batutuwa masu muhimmanci:

Idan aka samu kai cikin wani hali Anthony Scaramucci, na kamfanin SkyBridge Capital, yana komawa ne ga maganganu na basira na fitattun mutane na duniya da suka hada da Winston Churchill.

A rubutunsa mai sunan 'Words of Wisdom: 8 Famous Quotes to Help You Embrace Fear and Achieve Success, Scaramucci ya ce, " babban abin yi shi ne, ka yi karfin hali, ka jure ka kutsa ka shiga cikin abin da ke ba ka tsoron, da sa ka fargaba da rashin tabbas ka sanya kafarka gaba ko da menene zai faru.

Damuwa da gajiya ka iya hana mutum sukuni, kuma babu wanda zai so ya yi aiki da shugaban da ba zai kawo cigaba ba.'' kamar yadda wakiliyar CNBC Julia Boorstin ta rubuta a kasidarta mai taken, '3 Key Reasons to be Optimistic Like Steve Case.

Maimakon haka, yanayin mutumin da ke da kwarin guiwa da buri zai iya galaba a kan duk wani kalubale, ya zama wata dama ta cigaba kamar yadda ta rubuta, inda take bayar da misali da abin da ta koya a tattaunawarta da mutumin da ya kafa kamfanin yada labarai na AOL.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Beating stress before it beats you