Ka san ana arziki da kashin kare?

A duk lokacin da 'ya'yan Kathleen Corridon suka yi bikin ranar haihuwarsu addu'a ɗaya kawai suke yi, ita ce ta fatan ganin ranar da iyayensu za su yarda a ajiye kare a gidan.

Corridon mai shekara 60, wadda tsohuwar akanta ce ta ce, ''duk abin da 'ya'yan nawa suke so shi ne mu mallaki kare a gidan nan.''

''Matsalar ita ce mijina tsohon ma'aikacin gidan waya ne (mai raba wasiku ) ya yi shekara 40 yana wannan aiki. A lokuta da dama kare na binsa har ma ya cije shi idan ya je kai wasika gidaje. Saboda haka ba ya kaunar kare ko alama.''

A karshe dai iyayen sun hakura sun mika wuya bayan da 'ya'yan nasu suka kai shekara 10 da 12. Amma kafin a kawo karen sai da babar tasu (Corridon) ta yi yarjejeniya da su cewa dole ne su tabbatar suna kwashe kashin karen da duk wani abu da ya zubar a lambunsu.

Wannan yarjejeniya tsawon wata daya kawai ta yi. Saboda haka sai Corridon ta rage kudin kashewar da suke ba wa 'ya'yan nasu na mako-mako, ta yi hayar wani kamfani mai suna When Doody Calls, domin ya rika kwashe kashin karen nasu a kan dala tara a duk mako. Corridon ta ce, ''dole ne a kwashe kashin babu wata tantama.''

Kamfanin When Doody Calls mai kwashe kashin karen wanda aka kafa a shekara ta 2001 yana aiki ne a yankin arewacin New Jersey, a Amurka (wanda ya yi cinikin dala miliyan hudu da rabi a 2011), yanzu yana da mutanen da yake yi wa aiki a gidajensu har 450, in ji mai kamfanin Mary Ellen Levy.

Kamfanin ba ya tsaya ga kwashe kashin kare ba ne kadai, yana kuma sarrafa kashin mutane ya mayar da shi magani da kuma makamashi

Barking mad

Ba kimiyya ba ce ta kai Meg Retinger ga kirkirar wannan fasaha ta kasuwancin kwashe kashin kare ba, maimakon haka, kuskuren taka kashin kare ne ya jawo.

A shekara ta 2008 ne daya daga cikin masana kimiyya na kamfaninta ya zo aiki wata rana yana ta korafin cewa da safiyar nan kafin ya zo aiki ya taka kashin kare.

A wannan lokacin wani kamfani (BioPet Vet Lab Inc a Knoxville, Tennessee) yana sayar da kayan gwajin kwayoyin halitta wanda ake iya amfani da shi ko da a kan dabbobi.

A shekara ta 2010 sai kamfanin ya fara sayar da kayan gwajin kwayoyin halittar da za a iya gwajin kashin kare, ga kamfanoni da masu gidaje da ke bukatar masu karnuka su yi rijistar kwayoyin halittar karensu kafin su kama haya a gidajen.

A duk lokacin da aka ga kashin wani kare a muhallin sai a gwada shi a gano karen da ya yi shi ,a kuma ci tarar mai shi. Gwajin da ake kira PooPrints yanzu shi ne babban aikin kamfanin, inda kusan gidaje 3,000, yawanci a nahiyar Amurka ta Arewa sun yi rijista da kamfanin, wanda ake biya dala 50 a gwajin kwayoyin halittar na farko da kuma dala 75 domin gwajin kashin.

A garin Timberwood masu karnuka ana cinsu tarar dala 50 a karon farko, a karo na biyu ana yi masa tarar dala 100 karo na uku kuwa sai dala 200 zai biya, bayan tara ta uku sai mai gidan ya nemi karen da mai shi su tashi daga gidan, abin da sau daya kawai Violette ya yi.

Rage hayakin da ke bata muhalli

Ka manta da maganar makamashin hasken rana, kashin mutane ma zai iya zama wani makamashi mai kyau maras gurbata muhalli.

Kamfanin sufurin motar safa na First West of England, ya fara aiki da wata motar safa mai daukar mutane 40 wadda ke amfani da iskar methane da ake samu daga dagwalon bahaya da sharar abinci.

Kuma a yanzu kamfanin yana shirin fara amfani da wasu manyan motocin safa-safa masu bene guda 110 masu amfani da makamashin da ake samu daga bahaya.

Wannan fasaha ta samu karbuwa har ma abokin gogayyar kamfanin, Wessex Bus shi ma ya nemi gwamnati ta bas shi izinin amfanin da motocin safa masu aiki da irin makamashin a motocinsa 20 nan da shekara ta 2019.

Kamfanin First West ya ce sharar abinci da bahaya da fitsari ta fasinja daya a shekara za ta samar wa safa daya makamashin da za ta yi tafiyar kilomita 60.

Haka kuma ita wannan motar safa ta rage yawan hayakin da motoci irinta ke fitarwa wadanda suke amfani da mai da kashi 30 cikin dari.

Nasara a fagen aikin lafiya.

Kashi yana da daraja a wurin likitoci, domin a yanzu an samu fasahar da ake sarrafa kashi ya zama magani.

Tunanin cewa za a iya amfani da kashin mutum ta wannan hanya ba a santa ba sosai a 2005, lokacin da Catherine Duff, mai shekara 60 a yanzu, wadda ke zaune a Indiana, ta kamu da wata cuta bayan da ta sha wani magani. Ctar tata ta yi tsanani har ta sa ta amai da gudawa da sauran matsaloli har ta kai ba ta iya fita daga gida. Bayan shekaru bakwai da ta kamu da wannan rashin lafiya sai likitanta ya kawo shawarar a yi mata tiyata a cire babban hanjinta. Amma kuma likitan ya ce ko da an yi mata tiyata ba lalle ba ne ta rayu.

Maimakon a yi mata wannan tiyata ta sauya mata babban hanji Duff ta yanke shawara yin wani abu daban, wanda shi ne dashen kananan kwayoyin halitta masu rai na cikin bahaya (kashi), kuma daga yi mata wannan aiki sai kawai ta rika samun lafiya, ta ci gaba ta rayuwarta.

Tun daga yi mata wannan tiyata shekara hudu baya, wannan hanya ta zama wata sabuwar fasaha da har asibitoci ke amfani da ita kuma wasu ma sun bullo da wasu dabaru nasu na irin wannan aiki.

Daya daga cikinsu shi ne wani shiri na taimako da ake kira OpenBiome, wanda kawo yanzu ya aika da samfurin bahaya sama da 12,000, ga likitoci da asibitoci da suke aikin tiyatar a kan sama da dala 385 zuwa 535 kowanne.

Ana karbar bahayar ne daga mutane 32 wadanda ake biyansu dala 40 a kan abin da suke bayarwa kullum, wanda kuma dole ne a mika shi cikin minti 45 da yin kashin.

Aiki ne mai muhimmanci a harkar kula da lafiya, wanda mutane da yawa ke dariya a kansa idan suka ji, in ji Sasha Liberman, mai aikin tattara bahayar. Ta ce ''mutane da yawa na bayar da hadin kai idan ka gaya musu abin da kake yi.''

" Mutane da yawa suna daukar abin kamar wani shirme ne, amma idan ka yi musu bayani sai abin ya burge su da ba su mamaki."

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. There are people making millions from your pet's poo