Wasan kwamfuta a lokacin aiki zai iya bunkasa aikinka?

Hakkin mallakar hoto flickr

Sanya wasannin bidiyo a wayarka ta komai-da-ruwanka ko iPhone ka iya zama sirrin da zai kai ka ga nasara, idan kana yin wasannin a wurin aikinka.

Alina Dizik ta yi mana bincike

Lokacin da abokan aikin William Bauer suka gan shi yana wasan bidiyo maimakon aiki wasu daga cikinsu sun dauka yana bata lokaci ne kawai.

Amma Bauer mai shekara 24 wnda ke taimaka wa wajen tafiyar da harkokin kamfanin gidansu na Royce Leather wanda ke Amurka ba aikin banza yake ba a lokacin.

Wasan bidiyon da yake yi (Angry Birds) na minti biyar na taimaka masa ya huta tare ba shi damar yin tunani da kyau yadda zai iya shawo kan matsaloli da kalubalen aikin da ke gabansa.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasan bidiyo na minti biyar zai iya sa tunaninka ya inganta

Ya ce, '' abu ne da ke sa kaina ya washe,'' in ji Bauer wanda ya saba yin wasan bidiyon da wayarsa da rana lokacin da aiki ya dan yi sauki.

Tsawon lokacin da ake dauka ana aiki, da kan kai sama da sa'o'i 100 a mako na sa mutum ya gaji har ya kusan kasa tafiyar da aikin a rana, in ji ma'aiakacin, kuma a kana hakan ya ce yin wasan bidiyo a lokacin na sa ya huta tare da ba shi karfi da basirar ci gaba da aikin da yamma.

Ba Bauer ba ne kadai mutumin da ke bin irin wannan hanya ta yin wasan bidiyo a lokacin aiki domin ya huta. Ma'aikata da yawa suma suna yin hakan do,in suna samun damar hutawa da yin aikinsu cikin sauki.

Kimiyya na nuna cewa masu yin hakan kila na nufin wani abu ne. Masana kimiyyar tunanin dan adam da ma'aikatan masu yin wasan kansu suna cewa alfanun da ke tattare da hakan ya wuce nishadi.

Mutane da dama suna amfani da wannan lokaci na wasan bidiyo domin kawar da gajiyar aiki a duk tsawon rana, da kuma samun hanyar yadda za su jure da aikin da ke cin rai a duk tsawon rana.

Ba kamar duba shafin Facebook ko shiga intanet ba, wasan bidiyo abu ne da ke daukar hankali da sa mai yinsa ya dukufa kansa sosai, bayan haka yana kuma kara mana kwarin guiwar da muke bukata na tunkarar kalubalen da ke tattare da aikinmu wanda ba lalle mu samu a aikin ba. Wasu wasannin bidiyon ana tsara su ne ta yadda za su sa ka samu kwarewa ko mai dogaro da kanka in ji Chris Ferguson, farfesan kimiyyar tunanin dan adama a jami'ar Stetson a DeLand ta Florida a Amurka

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Wasan bidiyo lokacin aiki; hutu ne ko sirrin bunƙasa aiki

Duk da karin sha'awar da ma'aikata ke nuna wa ta yin wasan bidiyo domin bunkasawa da kuma samun nasara a wuraren aikinsu babu bincike na kimiyya mai yawa da aka yi a fannin. Amma wadanda suke yinsa na cewa tasirin wasan kai tsaye suke samunsa, ba da wani jinkiri ba.

Maganin matsala

Ka tsara lokacin da ya kamata ka yi wasan bidiyo a wurin aikinka. Lokacin da ya fi dacewa ka yi wasan shi ne lokacin da ka ga ba ka iya yin aiki da yawa, kamar lokacin da kake jin kasala ko barci da rana.

Wasan bidiyo zai iya taimaka ma da basira da kuma sanin yadda za ka magance matsala. Idan aiki ya kakare maka, ka bar shi, ka je ka kama yin wasan bidiyo na dan lokaci, zai iya ka samu wata basira ta yadda za ka bullo wa matsalar, ko kuma tunaninka ya washe, in ji masana.

Ferguson ya ce, ''wasan yana sa mutane su wartsake duk yadda yanayin aikinsu yake,'' kuma ya kara da cewa yawancin mutane ba sa jin wuyar barin wasan su koma bakin aikinsu.

A wasu lokutan, bukatar yin wasan za ta iya kasancewa da wahala. Amma dai Ferguson ya ce wasannin za su iya ba wa mutum yanayi na kwanciyar hankali da nishadi ta yadda zai iya jure yin aikin da yake da wahala.

Kuma ya ce wasan zai iya ba wa mutum damar sanin wasu dabaru kamar na shugabanci, wanda idan ba ta wasan ba, ba za ka san su ba. kana samun wannan kwarewa da ilimi idan ka fuskanci duniya kuma kana yakar mugayen mutane, wannan yana ba ka karin kuzari.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lokacin da ya fi dacewa da wasan kwamfuta ga ma'aikaci shi ne lokacin da ya gaji

Eric Brantner, wanda ya kafa shafin intanet na Scribblrs a Houston da ke Amurka, shafin da ke mayar da hankali a kan harkokin yada labarai ya ce yana yin 'yan mintina kadan ne kawai yana wasan bidiyon da wayarsa a lokacin cin abincin rana.

Sannan kuma yana yin wasu mintina 20 zuwa 30 yana wasan bidiyon a kwamfutarsa, wanda kuma hakan na raba shi da duk wata damuwa a rana. Ya ce magana ce kawai ta neman sararawa daga tarin abubuwan da ke gabanka na aiki da kuma kawar da tunaninka daga aikin.

Wasu masu kamfanoni ko masu daukar ma'aikata na ganin amfanin da ake samu daga yin wasan bidiyon, abin da ya sa suke sanya tsarin a kamfanin. Wasu sabbin kananan kamfanoni da kuma kamfanoni na harkokin fasaha kamar su Facebook da Google da dadewa sun sanya wa ma'aikatansu wasannin da sauran abubuwa na dauke wa ma'aikaci hankali daga ayyukan ofis, a kwamfutocinsu, domin karfafa wa ma'aikatan guiwa da kulla kyakkyawar dangantaka tsakanin ma'aikatan.

Wasu kamfanonin ma suna sanya tsarin amfani da wasannin domin sa nishadi da gasa domin karfafa wa ma'aikatansu guiwa su samu nasara wajen tafiyar da ayyukansu, in ji Ferguson. Misali ma'aikatan da ke tallata hajar kamfanoni ka iya bin diddigin kudin da za su iya samu na kamashonsu, kuma su yi gogayya da abokan aikinsu domin cimma wani mataki na cinikin da suke jawo wa kamfanin, ta hanyar amfani da wasan bidiyon da ya yi kama da irin kasuwancin nasu.

Takaita lokacin wasan

Su irin wadannan wasanni na kwamfuta na musamman an tsara su ne ta yadda ba za su dauki lokaci mai tsawo ba. A kan yi su ne yadda za su dace da dan takaitaccen lokacin da ya kamata ma'aikaci ya yi amfani da shi ya samu gamsuwa, ba tare da wasan ya rike shi ba, kamar yadda Ferguson ya yi bayani.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ko manyan kamfanoni za su rungumi wannan tsari inda ma'aikata ke wasan kwamfuta domin sararawa?

''Sun saukaka wasannin, ta yadda idan zai dauki sa'a daya a mamaye Faransa, za a yi hakan cikin minti 10 kawai, in ji shi.

Bincike ya nuna yin wannan dan wasan na kwamfuta yana da amfani, kamar yadda wani bincike da masana suka yi a jami'ar jihar Kansas a Amurka a 2014, a kan ma'aikata daga masana'antu daban-daban, sun gano cewa, wadanda suka yi wasan da wayoyinsu na minti daya ko biyu a lokacin hutunsu sun fi jin nishadi da farin ciki fiye da abokan aikinsu da ba su yi wasan ba.

Duk da wannan sakamako, in ban da sabbin kananan kamfanoni, yawancin manyan kamfanoni da suka dade da kafuwa suna ganin wannan tsari na yin wasan bidiyon ba shi da wani amfani.

Domin jawo hankalin abokan aikinsa su rungumi tsarin yin wasan a lokacin hutunsu Sam Williamson, mai shekara 27, inda ya fara sanya kidan tsoffin wakoki domin ya ga yadda abokan aikinsa a kamfanin Guardian Removals, da ke Edinburgh a Ingila, suka ji kidan ba ya dauke musu hankali kamar kidan da ke dauke da wakoki, wanda ta hakan ya yi shirin yin wannan tsari na wasan kwamfutar a lokacin hutu.

A yanzu, Williamson ya ce, yana da wani wasan kwamfuta mai kade-kaden tsoffin wakoki a ofishinsa, kuma shi da abokan aikin nasa suna yin wasan a ranakun Juma'a ko wasu ranakun da safe. Ya ce hakan, ''hakan yana taimaka ma ka fara aikinka da kyau.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Can gaming at work make you more productive? .