Yadda za ka iya samun riɓar ƙafa

Yin wani aiki na daban bayan ainahin aikinka abu ne da mutane da yawa ke sha'awar yi. To idan kana daga cikin masu wannan buri ga yadda za ka bullo wa lamarin.

Kamar yadda Kate Ashford ta yi nazari

Da rana, Robin O'Neal Smith ita ce babbar jami'ar yada labarai ta wata makarantar lardi. Bayan wasu sa'o'i kuma sai ta zama marubuciya kuma editar masu yada labarai ta shafukan intanet.

A yanzu tana samun karin dala 1000 a duk wata daga karin aikin da take yi wanda ta bullo da shi shekara biyu da ta wuce, bayan nata na ainahi.

Ta ce, '' na fara aiki ne na kula da shafukan sada zumunta, amma kuma sai na fahimci cewa akwai bukatar yada labarai ta intanet matuka fiye da facebook da Twitter,'' in ji Robin mai shekara 56, wadda take zaune a Pennsylvania da ke Amurka.'' Ta kara da cewa, " daga nan ne sai na fara aikin da mutum daya mai shafin yada labaran ta intanet kuma nan da nan sai na kara."

Asalin hoton, alamy

Bayanan hoto,

Idan kana tunanin yin wani abu, ka san cewa za ka iya gamuwa da matsala

Kudin da za ta rika samu daga wannan aiki na bayan aikinta da zai fi yawa idan da tana da isasshen lokaci. Ta ce, ''dan lokaci kadan nake da shi da zan yi rubuce-rubuce, tun da ina da cikakken aikin da nake yi, na dauki hayar wasu mutane kuma da sun kware a aikin, zan kara yawan masu shafukan intanet din da nake yi wa aikin.''

A yanayin aikin yanzu inda yawancin ma'aikata ba na didindin ba ne, ba abu ne mai sauki ba ka rika yin wani aiki bayan naka na ainahi. A Amurka kashi 12 cikin dari na ma'aikata masu cikakken aiki suna taba wasu ayyukan kamar yadda binciken 'Staples Advantage Workplace Index'. Ya nuna

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A Burtaniya an yi kiyasin akwai kusan masu irin wannan aiki na ribar-kafa su kusan miliyan daya da dubu 800 da takwas, kuma a Turai yawan irin masu aikin ya karu da kashi 45 tsakanin 2004 da 2013.

Idan kana tunanin jarraba wannan dabara kai ma to ga wasu abubuwa da ya kamata ka duba.

Abin da ake bukata: Akwai bukatar ka karfafa wa kanka guiwa tare da kudiri, ka kasance mutumin da zai iya ayyuka daban-daban a lokaci daya tare kuma da samun isasshen lokaci da ba ka komai.

''Fara wata harka ta kasuwanci kamfani ne na miliyoyin dala ko sayar da malafa ne kawai a kan titi, abu ne da ke bukatar aiki sosai," in ji Sam McIntire, wanda ya kirkiro shafin DeskBright, na intanet mai koyar da harkokin kasuwanci a Amurka.

Ya ce, '' kana bukatar yin tsare-tsare da suka hada da zayyana abin da za ka yi da tunanin hanyar tallata abin da kuma tsarin tallar, ga kuma bukatar ware isasshen lokaci.''

Haka kuma dole ne ka tambayi kanka dalilin da ya sa kake son fara harkar kasuwancin. Za ka yi ne domin kawai ka samu karin kudi ? Ko saboda kana da burin wani abu ne da kake da sha'a wa wanda kuma kake son duniya ta amfana da shi?

Kana son fara kasuwanci ne da kake fatan zai zama sana'arka gaba daya a nan gaba? To dazarar ka duba duk wadannan abubuwa ka tsara su kana iya fara harkarka, in ji Judith Lukomski, mutumin da ya kirkiro kamfanin Transitions Today, a California.

Yawan lokacin da kake bukata domin shiryawa ya dogara ga irin harkar da za ka yi. A wurin wasu bai wuce samun shafin intanet ba da yin rajista da hukuma da kuma yin inshora kafin kawai ka kama aiki in ji Jason Kitcat, shugaban kamfanin aikin akanta na intanet na Crunch,a Burtaniya. ''Wasu kuwa za su bukaci karin tsare-tsare.''

Tun da a baya kana bukatar fitar da wani tsari na yadda za ka yi kasuwancin da yin bincike na farashin kayan ka yi tunanin wadanda za ka sayar wa kayan da kuma yadda za ka rika kaiwa garesu.

Bayan wannan to ba ka bukatar a ce lalle sai ka tsara komai ya daidaita kashi dari bisa dari kafin ka fara.

''Na dauka sai na koyi komai a game da shafin zumunta na intanet, kafin na nemi aiki da wani,'' in ji Smith. ''To amma daman tuni ina da kwarewa a fannin rubutu da aikin edita. Abubuwa kodayaushe za su iya sauyawa, saboda haka kawai ka fara abin da za ka yi.

Asalin hoton, alamy

Bayanan hoto,

Tauna taura biyu ba abu ne mai sauki ba

Ka yi abin yanzu: Ka tabbatar akwai wanda zai sayi kayan naka. ''Mutane ba sa yin cikakken bincike kan cewa ko abin da za su yi yana da kasuwa wadda za ta dore ,'' in ji Robert Gerrish, wanda ya kirkiro harkar kasuwanci ta Flying Solo a Australiya wanda kuma da su suka rubuta littafin Flying Solo

ya ce abokai da iyalai sukan ce 'wannan dabara ce mai kyau,' amma a yawancin lokaci ba a daukar lokaci isasshe a yi bincike a wanna muhimmin mataki na yin kasuwancin.''

Akwai hanyoyi da dama da za ka fito da wani abu da kake son yin kasuwancinsa ta yadda mutane za su san shi. Za ka iya rarraba shi kafin ka fara sayarwa. Za ka iya sanya shi a wani shafi na intanet ana dan nuna shi lokaci zuwa lokaci kuma ka karbi adireshin email na jama'a.

''Akwai hanyoyi da dayawa da za ka iya auna sha'awar mutane ta kayan kafin ka mayar da hankalinka sosai a kansa,'' in ji " McIntire.

Ka duba ka tsara wanda kake son ya sayi kayan naka. Wanene mutumin da zai sayi kayanka?

''Daya daga cikin hanyoyin da ke taimaka wa ita ce ka gano takamaimai wadanda kake hari,'' in ji Lukomski. ''Misali mutumin sunansa Chris, kuma kana so ka bullo da wani abu da zai taimake shi. To za ka iya samun mutumin. Hakan ya fi ka ce, 'zan hari mata ne masu shekara 35 zuwa 55.'''

Ka duba takardara yarjejeniyar daukarka aiki. Idan aikinka na cikakken lokaci ne wato ba na wucin-gadi ba ne, (na wasu 'yan lokuta). To idan cikakken aiki ne ba ka so kuma ka jefa kanka cikin wata dambarwa ta hanyar saba wata ka'ida.

"za ka iya samun wani bangare da ya haramta maka aiki da yamma ko lokacin hutun mako," in ji Kitcat. " Me zai hana ka tuntubi sashen kula da ma'aikata game da lamarin?

''Na damu matuka yadda zan cike takardun rasiti da biyan masu aikin wucin-gadi da na dauka aiki da kuma yadda zan iya kirkirar shafina na intanet duka gaba daya, '' in ji Tess Frame, wadda ta fara gudanar da shafinta na intanet ta kuma fara tafiyar da dan kamfaninta.

Ta ce, ''abin da ya kamata in mayar da hankali a kai shi ne samun masu sayen abubuwan da nake yi maimakon mayar da hankali kan neman karin masu sayen. Ba ka bukatar shafin intanet idan ba ka da masu sayen kayanka ko abin da kake yi.

Asalin hoton, alamy

Bayanan hoto,

Idan kana da kyakkyawan aiki na dindindin a hannunka kada ka yi wasa da shi

Kada ka yi ta wasa. "ka tsara lokacinka da kyau za ka ga yadda mutane za su yi ta rububin sayen kayanka,'' Kitcat said. "ka tambayi kanka abin da kake son ka cimma a cikin kwanaki 60 masu zuwa ko kuma ka tsara abubuwan da kake son ka cimma daga mako zuwa mako." Wannan zai sa ka kasance a kan hanya, kuma hakan zai kare ka daga yawan shiga intanet a lokacin da ya kamata a ce kana aiki.

Ka yi abin a gaba. Kada ka manta cewa kana fa da aikinka a hannu. '' Kada ka je kana yi wa mutane alkawari da yawa kokuma ka karbi kwastomomi da yawa a lokaci daya, ko kuma ka yi ta fafutukar kokarin biyan bukatu na hanzari,'' in ji Kitcat said.

"kada ka boye wa masu mu'amulla da kai ko masu sayen kayanka hidimomin da ke gabanka don kada ransu ya baci idan ka kasa yi musu aikin da suke bukata daga gareka a lokacin aikinka." Ka shirya biyan haraji.

Kana samun kudi? To da kyau! Kila ana binka haraji a kan kudaden da kake samut. A Burtaniya misali kana bukatar sheda wa hukumar HMRC da sauran hukumomi, idan za ka fara wani kasuwanci domin ka san harajin da ya kamata ka rika biya na kudaden da za ka samu daga harkar da kuma wasu karin bayanai," in ji Kitcat.

Kada ka sa buri a ranka. Kada ka yi tsammanin kasuwancinka zai bunkasa cikin dare daya. ''Mutane da yawa suna sa buri sosai a ransu na yadda suke son su ga abubuwansu na gudana yadda suke so cikin dan lokaci," in ji Gerrish. "Ba su san cewa yawanci sai abin ya dauki lokaci mai tsawo ba."

Ka yi abin da gaske: Kada ka manta ka yi yadda za ka ji dadin abin kai kanka. Fara wata harka ta kasuwanci ko aiki wanda ke zaman na ribar kafa, magana ce ta samun karin kudi. " Amfaninsa yana da yawa sosai," In ji McIntire. Ya ce, '' da farko za ka samu 'yanci, sannan za ka gina wani abu, kuma za ka mallaki harkar - duka wadannan abubuwa ne da za su karfafa wa mutum guiwa."

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to make a side gig work for you