Zaben Amurka: Kamfe din Trump hadarin kaka ne?

Hakkin mallakar hoto Wikimedia Commons

Me za mu fahimta daga wani zane wanda ba a kammala ba na shekarar 1794 game da juyin juya hali na Faransa kan kayen da mai neman takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Republican, Donald Trump ya sha a Iowa?

Masaniyar tarihin zane-zane Catherine Ingram ta yi mana bayani.

Mai rai a kan ce ba ya rasa motsi, abin da za a iya kwatanta mai neman takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Republican, Donald Trump da shi kenan a kan karfin halin da yake cigaba da nunawa, bayan kayen da ya sha a zaben fitar da gwani na jam'iyyar tasu a Iowa.

Dokin mai baki ya fi gudu, to haka dokin Trump yake a wannan takara, kuma haka yake tallata kansa a yakin neman zaben da yake yi na fitar da gwanin jam'iyyar.

Yakin neman zabensa gaba daya a game da samun nasara yake yi, shi dai zai yi nasara, har ma an ruwaito shi yana ikirarin cewa da zarar ya yi nasara, Amurka za ta cigaba da nasara a ko da yaushe har ma sai ta gaji da yin nasara.

Nasarar me kuma ta yaya za a yi nasarar? Ba mu san amsar wadannan tambayoyi ba takamaimai, amma dai wannan hoton yana nuna shi ne a wata cibiyar wasanni a New Hampshire, bayan Ted Cruz ya gayar da shi a zaben fitar da gwani na Iowa.

Hakkin mallakar hoto Joe RaedleGetty
Image caption Mai neman takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Republican, Donald Trump na yakin neman zabe ranar 2 ga watan Fabrairun 2016 a Milford, New Hampshire.

To idan muka koma kan maganar zanen barkwancin na siyasa na shekara 1794 na juyin juya halin Faransa, wanda muke kwatanta taron siyasar da ake nuna wa a zanen da taron yakin neman zaben Mista Trump, to za mu ga cewa shi kansa juyin juya halin Faransa ya fara ne daga filin wasa.

Wannan zane na Jacques-Louis David, wanda ba a kammala ba, yana nuna lokacin da jama'ar Faransa suka bijirewa umarnin sarkinsu (a wancan zamani), suka taru a zauren wasan tennis na Versailles inda suka yi alkawarin yin aiki da junansu domin kafa gwamnati ta tsarin mulki.

Idan aka duba za a kamanni tsakanin hoton Trump da zanen da David ya yi; ana iya ganin mutane sun daga hannuwa gaba daya suna nuna mutumin da yake tsakar taron a sama (kan dandamali) yana jawabi.

A zanen David kusan rabin filin taron ba mutane. Saboda haka duk da taron mutanen, akwai iska a dakin. Iskar na bankowa ciki daga tagogin dakin da ke sama, tana kada labule, sanna mutanen ciki na shakarta, wanda hakan ke nuna alama ta lokacin farfado da siyasa a kasar ta Faransa.

Kamar yadda Trump ya yi ikirari, shi ne iska mai dadin da ake matukar bukata a siyasar Amurka. Sai dai kuma ga alama iskar tasa mai dadi ta danganci rashin kwarewa, kamar yadda yake bugun kirji cewa watansa shida kacal a siyasa.

Hakkin mallakar hoto Wikimedia Commons
Image caption Zanen Jacques-Louis David na 1794 na yadda aka fara gangamin juyin juya halin Faransa (Tennis Court Oath)

Abin da ke da muhimmanci shi ne bambancin abin da mutanen da ke tarukan suke yi. Su wadancan mutane (na zane) na taron juyin juya halin Faransa, zuciyarsu daya kuma da gaske suke kan duk abin da suke yi da fada a wurin. Taro ne da ke cike da kuduri da kishin zuci, wanda ya dauki azama, ga Pierre Robespierre (yana tsaye a bangaren dama daga gaba) ya dafe kirjinsa da hannuwansa yana tunanin guguwar da za ta fara kadawa.

A gefe da shi kadan daga dama ga marubuci Emmanuel Joseph Sieyes a zaune kamar an lika shi a kan kujerar, cike da tunani da fargabar abin da rubuce-rubucensa na siyasa za su iya haifarwa. Ga kuma jama'a na nuna goyon baya tare da kira da kumaji na a fita a nemi 'yanci (juyin juya hali).

Sabanin wannan shi kuwa taron Mista Trump na 'yan kallo ne kuma da a haka yake. Mutanenda suka hadu a gangamin wadanda suka mayar da hankalinsu wurin neman daukar hoto, ga alama zuciyarsu ba ta kan abin da aka shirya taron dominsa.

'Yan kallo ne kawai. Gahhanuwa ana dagawa domin a gyara na'urar iPhone ta yadda za a dauki hoto mai kyau, sannan kuma a samu damar daukar hoto mai kyau.

Sai dai abin damuwar shi ne, idan ya kasance mahalatta taro, sun zama 'yan gayyar na ayya (marassa tabuka komai), to fa mun bude fagen soki burutsu kenan.

Siyasar Trump siyasa ce ta jan 'yan kallo kawai, nasararsa kawai ita ce, ya jawo 'yan kallo, domin hatta 'yan jam'iyyar Democrat ma na zuwa wurin yakin neman zabensa domin kashe kwarkwatar idanunsu.

A nan Mista Trump ba ya ba da kunya ko alama, inda yake kalamansa gaba gadi kyamarori na ta daukarsa yana soki burutsunsa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Inglishi latsa nan. What can an 18th-Century painting tell us about Trump?