Lauyan da 'yan sanda suka casa a kotu

Hakkin mallakar hoto Wu Liangshu

Hoton wani lauya ɗan ƙasar Chana wanda ake zargin 'yan sanda sun casa a cikin kotu ya yaɗu kamar wutar daji a shafukan sada zumunta da muwara na duniya a lokacin da aka bayyana shi.

A kan hakan Kelly Grovier ya duba tarihin kekketa tufafin mutum.

Wannan dai abu ne da kusan ya zama al'ada wanda aka yi bitarsa sau shurin masaki a allunan zanen al'adu da wuraren wasan kwaiwayo na zamanin da, inda za a ga jami'an hukuma marassa tausayi sun yi wa mutum tsirara, a gaban shari'a.

To sai dai a wannan karon hoton ba na zamanin da ba ne ba kuma na zamanin bayyanar addini ba ne, kuma ba wanda za a gani ba ne a jikin bangon gidan adana kayan tarihi ko coci na yammacin duniya ba ne.

Maimakon duka wadannan, shi wannan hoto na wani lauya dan kasar China ne wanda ake zargin 'yan sanda sun kekketa masa kaya har suka kusan yi masa tsirara a cikin watan Yuni, a gaban wasu alkalai na lardi a China.

Hoton wanda ya watsu ta shafukan sada zumunta da muhawara na intanet, ya jefa jama'a cikin matukar mamaki na wannan ta'addanci na kotu.

Hakkin mallakar hoto Wu Liangshu
Image caption Lauya Wu Liangshu bayan 'yan sanda sun casa shi

An dauki hoton ne a Nanning da ke Guangxi a kasar ta China jim kadan bayan da aka gaya wa lauyan Wu Liangshu cewa an yi watsi da bukatarsa ta shigar da wata kara.

Lauyan wanda aka zarga da nadar bayanan abubuwan da ke wakana na shari'a a kotu da wayarsa, ya ki bayar da wayar tasa a duba a lokacin da aka bukace shi ya yi hakan, saboda haka ne sai, ya ce jami'an kotu suka rika casa shihar suka kusa yi masa tsirara.

Sanin cewa bayyanarsa a wannan hali da yagaggun tufafi zai jawo hankalin duniya kan zalincin hukumomi a China fiye da duk wani rubutu ko magana da zai yi, sai lauya Wu, ya fito daga harabar kotun ya tsaya a gaban tarin 'yan jarida masu daukar hoto da suke dako a wurin.

Sakamakon da hakan ya haifar shi ne wani hoto mai ban mamaki, wanda a tsarin adabi na yammacin duniya, ke cike da bayanai na nuna mutumin da za a ce ana gab da gicciyewa, an kama shi, sannan an yi masa dukan tsiya, kuma an sa shi ya yi tsallen kwado har zuwa gaban babban mai shari'a da zai yanke masa hukunci.

Duk da cewa hoton lauyan a wannan yanayi ba shi da alaka da wani addini, amma yadda aka kekketa masa tufafi a gaban hukuma musamman ta shari'a, ya sa ya zama wani abu da ke tuna yadda aka yi hoton Yesu a zamanin karni na biyar zuwa 15 zuwa na 20.

Hakkin mallakar hoto Wikimedia
Image caption Zanen hoton Yesu a gaban alkali Pilate, wanda ke nuna gana akuba da yi wa mutum zigidir

Hoton ya fi jan hankali idan aka ajiye shi kusa da hoton zanen karni na 17 na Yesu a gaban alkali Pilate wanda ya yanke masa hukuncin gicciyewa.

Zanen wanda ake dangantawa da kwararren mai zanen nan na kasar Holland Nicolaes Maes, ya nuna Yesu wanda aka kwace tufafinsa, yana dingishi saboda akuba da ya sha, amma kuma yana cike da karfin hali kuma ba alamar karaya a tare da shi.

Akwai babban sabani tsakanin hoton Wu tsaye da yagaggun tufafi da alamar karfin adalcin shari'a a kasar ta China, wanda aka alamta da duwatsun bangon da ya tsaya gabasna aka dauke shi hoton.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The man who had his clothes torn off