Hoton da ya ɗauki hankalin duniya

Hakkin mallakar hoto GirlAboutThames

Hoton 'yan sandan birnin Landan suna sumbata da rungumar junansu a yayin baikon aurensu na 'yan luwaɗi a bainar jama'a ya karaɗe duniya a shafukan intanet.

Kelly Grovier ya yi nazari kan yadda hoton ya tabbatar da zanen hasashen da fitaccen mai zanen nan na Burtaniya Banksy ya taba yi shekaru da dama da suka gabata.

Ka yi tunanin yanayin da za a ce ga masu zanga-zanga da suka rufe fuskokinsu suna jifa da furanni maimakon duwatsu da kwalabe. Ka yi tunanin fagen yakin da za a ce gawata 'yan kananan yara mata sun tsare sojoji sun kwace makamansu. Haka kuma ka yi tunanin yadda za ta kasance abin da masu zanen barkwanci ke yi ya juye ya zama gaskiya.

Duk wanda ya shiga shafukan sada zumunta da muhawara na intanet a kwankin hutun makon karshe na watan Yuni na wannan shekara, wato watan da ya gabata kenan, zai iya ganin kusan sauyi irin na duk wadancan abubuwa da muka gabatar na kamar reshe ya juye da mujiya, ko mai dokar barci ya buge da gyangyadi.

Hoton soyayya na wasu 'yan sanda dake sumbatar junansu a bainar jama'a a lokacin gangamin masu neman jinsi daya, wato 'yan luwadi da madigo da akja yi a birnin Landan, ya zarta fitattun hotuna na zanen da kwararren mai zanen nan na Landan Banksy ya yi.

Fitaccen zanen da ya yi na wasu 'yan sanda maza suna sumbatar junansu kamar mata da miji, zanen da aka fi sani da 'kissing Coppers' wanda ya kawata wani bango a Brighton a 2004 a karshe dai an sayar da shi a shekara ta 2014 a kan kudi fan dubu 345 ko dala 463,500.

Hakkin mallakar hoto Paul Lovichi PhotographyAlamy Stock Photo
Image caption Zanen Banksy na 2004 a Brighton wanda aka fi sani da Kissing Coppers

Kamar da kasa wannan zane da Banksy ya yi ya tabbata, abin da ya sa 'yan kallo suka sha matukar mamaki da jimami, abin da ke nuna cewa wannan hali (na rungumar juna) abu ne da bai dace da 'yan sanda ba, kamar yadda za a dauki yanayin da za a ga masu bore suna jifa da furanni maimakon duwatsu da wasu muggan abubuwa.

Hoton bidiyon da aka gani na wani dan sanda yana kulla aure tsakaninsa da wani dan sandan a bainar dubban masu kallon jerin gwanon 'yan luwadi da madigo, ya yi kasuwa a shafukan sada zumunta na intanet, inda aka kalle shi sama da miliyan 14.

Hoton ya ci kasuwa ne a daidai lokacin da labaran nuna kyama da tsangwamar masu neman jinsi suka mamaye kafafen yada labarai, daga harin da aka kai kan 'yan luwadi a Orlando da ke Florida a Amurka, zuwa karin hare-haren kyama a kan baki a Burtaniya bayan sakamakon kuri'ar raba gardama ta Burtaniya.

A cikin irin wannan yanayi na tashin tashina da bore yadda jama'a ke daukar 'yan sanda, jami'an da ke da alhakin tabbatar da doka, shi kansa ya shiga wani hali.

Kodayake tuni aka kalubalanci kallon da ake yi wa 'yan sanda a matsayin mutane masu karfin tsiya, a fagen mawaka kama daga kungiyar 'Village People' da George Micheal, ganin dan sanda a matsayin alamar dan luwadi ya zama kamar wata shigar wasan kwaikwayo ce, wato wata shiga ce ta barkwanci ta nufin wasa da hankalin jama'a. Kafin yanzu kenan.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The proposal that went viral