Biri yana dariya da fara'a kamar mutum

Wani lokaci murmushin mutun ya fi maganar da zai yi ma'ana. Mu kan yi murmushi a hankali kuma mu yi dariya a bayyane ta yadda kowa zai ji. Wannan duka na nuna yadda muke amfani da fuskokinmu wajen mu'amullarmu ta yau da kullum.

A duk lokacin da muka yi murmushi, abubuwa da dama a fuskarmu suna sauyawa.

Mu kan yi murmushi ba tare da mun yi magana ba ko dariya.

To sai dai wani abu da ba a san ya yake ba game da murmushi shi ne yad da ya samo asali.

A tsawon lokaci an yi amanna cewa dariya da mutum kan yi ta samo asali ne daga yanayi na tsoro ko yake da kakanninmu(na farkon halittar mutum da biri) kan yi a sanadiyyar tsoro.

To amma kuma nazarin da aka yi na dariyar da birrai ke yi idan suna wasa ya kawar da wannan tunani, inda wannan ke nuna cewa su ma birrai suna dariya domin wani abu na jin dadi ta hanyar amfani da lebensu na sama kamar yadda mu 'yan adam muke yi

Hakkin mallakar hoto AFP

Lalle ne kam birrai suna dariya a lokacin da suke guje-guje da tsalle-tsalle to amma idan aka duba yanayin fuskarsu sosai za a ga cewa ta yi kama da tamu a lokacin da mu ma muke dariya.

Wannan ya nuna ke nan dariya ta samo asali tun kafin a samu mutum ko biri kamar yadda ake da su a yau, wato abu ne da ya fara tun daga halittar da ta juye ta zama biri da kuma mutum a yau.

Hakan na nufin ga alamu murmushinka ya samo asali ne tun bayan sama da shekara miliyan biyar kamar yadda wani sabon bincike wanda aka wallafa a mujallar PloS One, ya nuna.

Ayarin wasu masana sun yi nazari akan yanayin fuskar wasu birrai 46 a lokacin da suke wasa.

Birran kuma an zabo su ne daga wurare daban daban a kasar Zambia da ke Afrika, domin lura da wani bambanci da za a iya samu daga kowannensu.

Hakkin mallakar hoto

An gano cewa suna amfani da wani tsari na musamman da ke nuna wani sauyi a yanayin motsin fuskarsu, wanda hakan ke nufin za a iya kamanta su da yadda dan adam shi ma yake murmushinsa.

Ayarin masu binciken ya kuma gano cewa birrai za su iya murmushi ba tare da sun yi wani sauti ba.

Wannan kuma ya nuna cewa suna motsa fuskarsu a lokacin da suke murmushi fiye da yad da a da aka dauka.

Marina Davila-Ross, jagorar binciken daga jami'ar Portsmouth da ke Birtaniya, ta ce yadda muke murmushi yana da muhimmanci da amfani a yanayi na bayyane da kuma hanyoyi da dama.

Ta ce, '' da ba mu san cewa su ma birrai suna iya yin haka ba ta irin wannan hanya.''

Ta kara da cewa,'' tsawon shekara arba'in masu bincike suna nuna cewa murmushin da biri ke yi ba wani abu ba ne tsoro ne kawai. Kuma shedarsu ita ce birrai ba sa daga lebensu na sama idan suna dariya.

To amma cikakken binciken da muka yi ya nuna mana cewa su ma birran suna yi.''

A don haka murmushinmu (mutum da biri) ya samo asali ne daga yadda kakanninmu suke yi amma ba daga tsoro ba.

Marubutan suka ce, ''duk da cewa watakila murmushi da dariya sun samo asali ne daga wasa to amma yad da dariya ta zama wani muhimmin bangare na rayuwarmu ta yau da kullum a yanzu ta wuce haka, ta zama wani ginshiki na harshe ko yare da basirar nuna yanayin mutum.''

Hakkin mallakar hoto PA

An yi wannan binciken ne bayan da aka gano cewa birrai sun san yadda za su hada barasa da ruwan ganyayyaki su sha kuma su bugu, kuma suna iya yin girki.

Davila-Ross ta kara da cewa, '' idan muka ci gaba da bincike akan kamanninmu da abubuwan da muke yi iri daya da birrai za mu iya kara gano su.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Chimpanzees can laugh and smile like us