Gwagwarmayar kunkurun da ya birkice

Hakkin mallakar hoto rubberball alamy

A rayuwa ta duk wani abu mai rai a kan samu wani babban kalubale ko matsala da ke zama alakakai ga wannan halitta, wadda a kwana a tashi ta kan iya samo hanyar yaki da wannan matsala.

Matt Walker ya yi nazari a kan kalubalen kunkurun da ya birkice.

A duniyar nan idan akwai wani kalubale da ya fi damun kunkuru shi ne yadda zai iya juyewa ya dawo kan kafafunsa idan wani hatsari ya kai shi ga birkicewa kafafunsa suka koma sama ya zauna da bayansa.

Ya danganta ga fahimtarka amma wannan tana daya cikin manyan tambayoyi na rayuwa.

Ta yaya kunkurun da ya birkicewa zai iya juyawa ya komawa kan kafafunsa?

Ba wai tambaya ce ta salon magana wadda ba ta bukatar amsa ba kuma ta wuce a ce tambaya ce ta zaurance ko wasa kwakwalwa ko kuma muhawara ba.

A wurin kunkuru magana ce ta daya daga cikin babbar gwagwarmayarsa a rayuwa, ko a mutu ko a yi rai.

A yanzu masana kimiyya sun yi bincike kan wannan jan aiki domin su gani ko wannan halitta ta shawo kan wannan gwagwarmaya, idan kuma ta yi ta yaya?

Hakkin mallakar hoto other

Dakta Ana Golubovic ta Jami'ar Belgrade a Serbia tare da abokan aikinta sun yi nazarin wutsultsulawar da kunkuru yake yi a hankali idan ya juye, domin ganin yadda siffar kwokwon bayansa za ta iya sa ya juye ya dawo kan kafafunsa.

Dabbobi masu silke ba su da wahalar faduwa su juye a bayansu, yadda za a iya cutar da su ko ma su kai ga har tsananin yunwa ya kama su su kai ga mutuwa.

Kunkuru na fadawa cikin hadari ta yadda idan ya birkice ba zai iya dawowa kan kafafunsa ba sai dai kawai ya rika wutsul-wutsul a cikin kokonsa.

Duk da cewa masana sun dade suna ganin cewa tsawo da tudun kokon za su iya taimaka masa ya juya ba wanda ya taba tunanin duba tasirin girma da yanayin kokon a kan kukuru mai rai wajen iya yin hakan.

Dakta Gulovic da abokan aikinta sun yi nazari a kan wasu kunkuraye 118 ( mata 54 da maza 64), inda suka ajiye kowanne a birkice.

Daga nan kuma suka rika auna tsawon lokacin da kowane kunkuru daga cikinsu ya dauka yana wutsul-wutsul da kafa da kai da kuma jela na kokarin ya juye tare da danganta lokacin da girman kokon kunkurun.

Bayan wannan sai suka gano cewa nazarin yana bukatar fadadawaa shigo da wasu abubuwa ciki kamar yanayin dumin jiki na dabbar.

Kasancewar kunkuru dabba ce da ba ta da dimin jiki sosai dole ne sai ta yi fafutukar samun kuzarin da za ta iya wannan birkicewa, wanda wannan abu ne da ya kamata a kawar da shi a nazarin.

Sun kuma gano cewa daidai girman kunkuru daidai karfin iya juyewarsa, inda maza suka fi mata a wannan kokari.

Macen kunkuru tana girma fiye da namiji saboda watakila yawan girman yana da tasiri wajen samar da 'ya'ya masu lafiya sosai, wanda wannan wata dama ce da ta fi ta iya juyewa idan aka birkice.

Hakkin mallakar hoto z

Namijin kunkuru yana da matsalar da ke damunsa ta daban

Mazan da suke kanana sun fi kuzari kuma yawan zirga-zirgarsu ka iya ba su damar saduwa da mata da yawa.

To amma kuma fa namijin kunkuru yana son fada sosai, inda yake kokarin birkice abokin fadansa.

To a nan kuma amfanin girman jiki ya zo, domin wanda yake da nauyi sosai da wuya a iya birkice shi, sai dai ma shi ya yi nasara.

Hakkin mallakar hoto rubberball alamy

Ta yaya zan fita daga wannan hali?

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The upside down tortoise enigma