Wa zai tsere wa wani kunkuru ko zomo?

Hakkin mallakar hoto spl

''Ku kalle ni da kyau!' zomo ya gaya wa sauran dabbobi. ''Ku duba yadda nake da gudun tsiya.'' Yadda zomo kenan yake bugun kirji a labarin Aesop,

(wani sarkin labari da tatsuniya na zamanin da a Girka) a tatsuniyar kunkuru da zomo.

Zomo yana da gudu sosai kuma ba shakka ya kwana da sanin haka.

Saboda haka ne lokacin da ya kalubalanci kunkuru a tsere da kunkurun ya yadda su fafata, dukkanin dabbobin da suke wurin ba wanda ko a ransa ya kawo cewa kunkurun zai iya yin nasara.

Wannan ba abin mamaki ba ne, domin yana tafiya a kasa da rabin rana, kuma ma idan har ya yi tafiyar ba ya iya tafiya da sauri ko kadan.

To amma a wannan karon sai reshe ya juye da mujiya, labari ya sha bamban, zomon da ya ci da zuci, sai kawai ya farka ya ga ai tuni har kunkuru ya kai karshen tseren bayan da shi ya dan kishingida ya dan yi barci kafin ya ci gaba da gudun.

Sai dai inda maganar take shi ne, anya hakan za ta iya faruwa a rayuwa ta gaske?

Hakkin mallakar hoto Airwolfhound cc by 2.0
Image caption A tatsuniyar Aesop zomo ne ya yi rashin nasara

Tambayar kenan da muka ga wasu daga cikin ku masu karatun labaranmu domin jin ra'ayinsu.

''Ya dogara ga irin tseren. A tseren tsawon rayuwa zan zabi kunkuru,'' in ji Cal Frame.

''Tseren inkiya ce ta rayuwa. Kunkuru ya fi zomo dadewa a duniya,'' in ji Joshua Taylor.

Ya yi gaskiya, domin wani nau'in kunkurun ya kan kai shekara 150 a duniya, shi kuwa zomo matuka ba ya wuce shekara bakwai, yawanci yana rayuwa ne tsakanin shekara uku zuwa biyar kawai.

Jimmy Dee yana ganin kunkuru zai yi ta tafiya ne a mike ba zai kauce hanya ba in dai ba wani abu ne ya tare masa hanya ba, amma shi kuwa zomo zai yi ta zarya ne nan da can.

Amma fa ba kowa ba ne ya yarda. ''Ow wai BBC na bayar da misali da tsohuwar tatsuniya. Tambayar ta yi harshen damo ina ganin amsoshinta sun fi daya,'' in ji Ty Huynh.

Edmond Theodore Roo shi ko ya yi mana dan lissafi ne kuma yana ganin '' ba wata hanya da kunkuru zai fi zomo sai dai in a tsawon shekarun da suke yi ne a duniya.''

To amma yawancinku kana ganin kunkuru zai yi nasara musamman idan za a yi maganar tseren dogon zango ne.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kunkuru yakan kaura daga inda yake kowace shekara

''Zomo na bukatar karin karfi ya iya kaiwa karshen tseren saboda haka yana bukatar cin abinci da yawa.

Shi kuwa kunkuru yana tafiya ne a hankali kuma tsanake saboda haka ba zai rika tsayawa yana hutuwa sosai ba, a don haka ba zai bukaci wani karin karfi ba.'' Kamar yadda Kenny Wright ya bayyana.

To ko za a iya cewa wadannan bayanai daidai suke? BBC na son samun tartibiyar amsa, saboda haka ne na mika tambayar ga masana.

Da farko dai sai mun duba wane irin tsere ne za su yi. Domin kamar yadda muka sani kowanne irin tsere yana irin bukatarsa da kuma masu tseren.

Idan muka kasa shi gida uku, inji masanin kwayoyin halittu Taylor Edwards na Jami'ar Arizona da ke Amurka dukkaninsu kowanne za a iya samun sakamako daban-daban.

''Kamar yadda a gasar Olimfiks (olympics) ba gasa daya kawai ake da ita ba, kana da ta gajeren zango da kuma ta yada-kanin-wani. To haka abin yake a gasar tsere tsakanin zomo da kunkuru ma.''

Hakkin mallakar hoto Andy Parkinson NPL
Image caption Wasu zomayen suna iya gudun kilomita 60 a sa'a daya

Da farko a gasar tseren wanda ya fi sauri ta gajeren zango kenan wadda za ta kai nisan kilomita 50 zuwa 60 a cikin sa'a daya, wannan ba tantama zomo zai yi nasara.

Na biyu kuwa, idan gasar dogon zango ce wato ta yada-kanin-wani kenan, za a iya yin canjaras, wato za su iya yi zuwa daidai ba wada zai kasa wani.

Domin kunkurun hamada yana iya juriyar tsananin yanayi na zango mai nisa, kamar yadda Edwards ya yi bayani.

Haka shi ma wani zomon dawan, yana da juriyar yanayin hamada, kunnuwansa masu girma na taimaka masa wajen sanyaya jikinsa daga tsananin zafi.

''Sakamakon zai iya kasancewa daidai idan za mu duba su ta fanni daban-daban kan damar da wannan yake da ita da kuma wadda dayan shi ma yake da ita.'' Inji masanin.

Sai kuma tsere na uku wanda Edwards ya tabbatar mini cewa kunkuru ne zai yi nasara idan suka zuba.

Wannan tsere kuwa shi ne na sauyin halitta daga yadda kowanne ya samo asali zuwa yau.

A wannan bangaren, shi zomon daji a kiyasi ya kai shekara miliyan 40 ne matuka, yayin da shi kuwa kunkuru nau'insa ya kai shekara akalla miliyan 200.

To idan ka duba wannan da kuma tsawon rayuwar da yake yi a duniya za ka ga cewa kunkuru zai yi9 wa zomo fintinkau a wannan tseren, ya ce.

Amma kuma akwai wani abin da kuma za mu iya dubawa: tsawon nisan da kowanne ke ci a tsawon rayuwa.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tafiya maganin gari mai nisa

Ganin yadda yake da tsawon rayuwa za a iya cewa kunkuru zai yi tafiya ta zangon da ya fi na zomo? Edwards na ganin ba shakka zai yi. Ga kuma dalilinsa.

Katon kunkuru zai iya tafiya ne matuka tsawon kilomita 10 a wata yana tafiya da saurin dodon kodi na cin mita 60 a sa'a daya.

Shi kuwa zomo zai iya saurin cin sama da kilomita 60 a cikin sa'a daya, amma kuma ba zai fita daga da'ira ko zagayen inda gidansa yake ba, wanda matuka ya kan kama daga murabba'in kilomita daya ne zuwa uku. A tsakanin nan yake zama duk tsawon shekara.

To bisa wannan kiyasin idan katoton kunkuru zai iya tafiyar nisan kilomita 120 a shekara daya, a tsawon misali mu ce shekara dari daya, kenan zai yi tafiyar kilomita 12,000.

Zomo zai buge wannan bajintar a cikin shekara daya idan zai kure gudunsa na tsawon sa'a uku a duk rana. Wannan zai bayar da kilomita 65,000 a shekara.

To amma kuma fa katoton kunkuru ya kan yi kaura a shekara kuma yana da gida a da'irar da ta fi ta gidan zomo, wadda ta kai ta fadin murabba'in kilomita 10 zuwa 40.

Shi kuwa zomo yana rayuwa ne a fadin dan wurin da bai kai na kunkuru ba, kuma ba ya yarda ya yi nisa daga wannan dan tsukukun.

Saboda haka ko da zai yi gudun nisan kilomita 65,000 a shekara, kusan yana kewaye ne kawai amma ba tafiya a mike ba.

Kuma idan har ana maganar cin wani zango ne a gasa sai ka kai wata iyaka ko ka ci wani zango.

Hakkin mallakar hoto A.Davey CC by 2.0
Image caption Sauri ba gurin zuwa

Wannan dalilin ne shi ma Shawn Scholl ya bayyana: ''Gwari-gwari ba wata maganar wani kwatanci ko inkiya ta salon magana, kunkuru ne zai yi nasara a kan zomo.

Dalili? Duk wanda ya taba dadewa a waje ya san cewa zomo yana kewayawa ne kawai da gudu, saboda haka kunkuru ne zai tsere masa.''

Guillaume Bastille-Rousseau na Jami'ar Jihar New York, a Amurka shi ma kwararre ne a kan rayuwar kunkuru.

Shi ma yana ganin abu ne da ya dogara ga tsawon gasar tseren. ''Idan tseren ya wuce na sa'a daya to ba ma za a yi maganar kunkuru ba.''

Amma idan a tsawon rayuwa ne shi ma ba ya shakkun kunkuru, saboda haka a wannan bangaren yana bayansa.

A zahiri abu ne mai wuya ka kwatanta dabbobin biyu. Kuma idan ka yi la'akari da bambance-bambancen da ke tsakaninsu kamar shekaru da tsawon rayuwa da fadin yankin gida ba za ka iya fitar da zakara daya ba kawai.

Amma idan aka duba tsarin halitta akwai alamun gaskiyar maganar tatsuniyar Aesop wadda ke nuna cewa: sannu sannu kwana nesa kuma a kwana a tashi zare kan yanka karfe.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Can a tortoise beat a hare?