Tsuntsayen da ke tsoron mutuwa

Hakkin mallakar hoto alamy
Image caption Suna kallonka

Su dai wadannan tsuntsaye bakake masu girma kamar kurciya ko hankaka za ka ga sun kewaye dan uwansu da ya mutu. Dalilin da ya sa suke hakan, abu ne mai daure kai.

Melissa Hogenboom ta yi nazari.

An san wadannan irin tsuntsaye da yin wata dabi'a ta daban a kusa da dan uwansu da ya mutu, inda sukan tattaru a inda ya mutu suna ta kara ko kuka da karfi a kusa da shi.

Ana ganin hakan wani nau'i ne na makoki ko jana'izar wanda ya mutum a al'adar wannan tsuntsu.

Duk da haka wannan abin da suke yi ba a kai ga gane shi ba, domin masana kimiyya ba su da wani abu da za su dogara da shi cewa ga ma'anar wannan dabia' in ban da kawai shedar yin wannan dabi'a.

A don haka ne wasu masana suka dukufa yanzu domin gano abin da ya sa wadannan tsuntsaye suke yi wa mamacinsu haka.

Hakkin mallakar hoto neil demaster cc by 2.0
Image caption Yana dubawa ko akwai wata barazana a inda yake

Domin yin hakan sun shirya wani nazari inda suka bullo wa binciken ta abin da ya sa tsuntsayen ba sa manta fuskar wani abu da ya zama barazana a gare su.

An gano wannan ne daman tun a baya a wasu nazarce-nazarce da aka yi. A tarin binciken da John Marzluff na Jami'ar Washington da ke Seattle a Amurka ya jagoranta sun nuna wannan tsuntsu yana gane mutumin da yake zaman hadari a wurinsa.

Daga nan kuma sai su koya wa sauran 'yan uwansu su rika kara ko kuka da karfi da zarar sun ga wannan fuska.

Hakan na nufin daga wannan lokacin dukkanin wadannan tsuntsaye da suke yankin ba za su taba yarda da wannan fuska ba har tsawon shekaru.

Abin da masu binciken suka yi domin gudun kaurin suna a wurin tsuntsayen, sai suka yi amfani da fuskar batar da kama.

Hakkin mallakar hoto design pics inc alamy
Image caption Wadan nan tsuntsaye suna iya gane fuskar mutum

Ta hanyar amfani da wannan dabara ta batar da kama, masu bincike sun yi amfani da wata mata daya da ta sanya fuskar roba ta tsaya a inda tsuntsayen suka saba zuwa mai binciken, Kaeli Swift shi ma daga Jami'ar Washington yana ajiye musu abinci.

Zuwan matar wurin da abinci abin so ne ga tsuntsayen amma kuma zuwan matar da fuska a rufe rike da gawar irin tsuntsun a hannu ta tsaya a wurin tsawon minti 30.

''Na saba da tsuntsayen saboda ina kawo musu abinci ba wanda yake tsorona,'' inji Swift.

''Zan mika musu abinci, daga nan kuma sai wata mata mai sanye da fuskar roba (bad da kama) ita ma ta zo ta tsaya har tsawon minti 30.

''Matar za ta zo wurin ne kawai rike da gawar tsuntsun kawai kamar za ta sa ta a shara, ta mika hannu kamar tana rike da kwanan abinci.''

Hakkin mallakar hoto kaeli swift
Image caption Masu bincilken sun sanya fuskar bad da kama

A ranar farko da wadda ta sa fuskar robar ta bayyana a wurintsuntsayen sai suka kauce wa abincin suka ki matsowa kusa amma sun taru.

Maimakon su zo wuin abincin sai suka koma gefe suna wani kuka na alamun bacin rai da kuma neman yin fada, kamar yadda suke yi idan sun taru da yawa a wurin wani da suke gani abokin gabarsu ne ko kuma mai cutar da su ne.

A wannan lokacin wannan dabi'a da suke nunawa ta yin fada za ta iya kasancewa sun yi ta ne domin sama da abu daya, kamar yadda masu binciken suka wallafa.

Za ta iya kasancewa ''nuna tsana ga abin da ba sa ga maciji da shi, wato mai kawo musu hari ko nuna iko da karfinsu a kan wurin ko kuma mutumin da ke zaman barazana a gare su''.

Idan aka ajiye shaho a kusa da wannan irin tsuntsu za ma su fi kin zuwa kusa da abincin, wanda ke nuna sun san cewa shaho hadari ga rayuwarsu.

Da wadda ta sa fuskar roban nan ta sake dawowa washegari duk da cewa ba ta dauke da gawar wannan irin tsuntsu wato dan uwa nasu, duk da haka sun ki zuwa wurin abincin wato ba su yarda da ita ba saboda sun gane wannan fuska kuma sun dauke ta a matsayin ta abokin gaba.

Wannan sakamakon ya nuna cewa wadannan irin tsuntsaye suna kin wuri ko abin da duk suka dauka hadari ne ga ire-irensu.

A takaice sun san mece ce mutuwa sun kuma san yadda za su guje ta.

Hakkin mallakar hoto kevin ebi alamy
Image caption Tsuntsayen sukan ankarar da junansu game da wani hadari ko barazana

''Wannan ya nuna mana cewa akalla wadannan tsuntsaye sun dauki mutuwa a matsayin wani darasi. Ala ce ta hadari, kuma duk abin da yake na hadari abu ne da za a guje shi,'' kamar yadda Swift ya bayyana.

Wannan tsoro na wani yanayi mai hadari a gare su ya ci gaba da kasancewa da su. Hatta bayan sati shida daga yin wannan gwaji aure sama da 65 na tsuntsayen sun ci gaba da halayyar da suke ta nuna kin yarda da kaucewa abincin.

Wannan nazari wanda aka wallafa a mujullar dabi'ar dabbobi (Animal Behaviour), kari ne daga binciken da ake yi na fahimtar yadda dabbobi suke yi idan wani nasu ya mutu.

Akwai wani tsuntsun (jays) shi ma wanda kusan dangi ne na wannan (scrow) tsuntsun, shi ma an gano yana yin wani abu da za a iya cewa jana'iza idan ya ga wani nasa ya mutu.

Yayin da shi wannan daya tsuntsun da ake kira jay a Ingilishi yake daukar mutuwar duk wani tsuntsu mai daidai girmansa kamar ta dan uwansa, shi kuwa wancan na farko da muka fara da bayaninsa mai suna scrow da Ingilishin ba ya damuwa domin mutuwar wani da ba danginsa ba.

Idan wannan da ta sa fuskar roba ta rike gawar kuciya maimakon ta irin shi wannan tsuntsun sai a ga bai damu ba.

Hakkin mallakar hoto kaeli swift
Image caption Wadda ta yi bad da kama ta rike gawar irin tsuntsun tsawon minti 30

Wannan binciken ya nuna yadda wadan nan tsuntsayen suke bayar da muhimmanci wajen ganewa da kuma haddace kamannin fuskar mutum.

Wannan wani ilimi ne da ke taimaka musu bambance mutanen da suke zaman hadari ko barazana ga rayuwarsu da kuma wadanda ba za su cutar da su ba.

''Wannan nazarin ya nuna yadda wannan tsuntsu (crow) ya iya rayuwa da a cikinmu,'' in ji Swift

''Za su iya gane fuskokinmu kuma ta hanyoyi da yanayi da dama ciki har da lokacin da muka yi bad da kama a matsayin masu cutar da su ta hanyar ganawa da wani nasu da ya mutu,''

Wadannan tsun tsaye (crows) su ne na baya bayan nan daga cikin kananan dabbobi wadanda suke iya gane dan uwansu da ya mutu ko ma yi masa jana'iza.

Giwaye da rakuman dawa da birai da kuma sauran nau'in dabbobi da yawa suna tattaruwa da kai kawo a kusa da gawar wani dan uwansu da bai dade da mutuwa ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The birds that fear death