Wurin da aka fi walkiya da tsawa a duniya

Hakkin mallakar hoto Kent Wood SPL

A yankin wani tafki a kasar Venezuela ana walkiya sau 28 a minti daya kuma ga dubban tsawa da cida. Ella Davies ta bincika yadda lamarin yake.

Watakila kasan maganar nan da ake yi cewa ba a walkiya fiye da sau daya a wuri daya a lokaci daya? To ka bar wannan magana. Domin dai a yanzu an gano yankin wani tafki a Venezuela da a dare daya kawai yake samun dubban walkiya a kowace sa'a.

Wannan wuri inda kogin Catatumbo ya hadu da tafkin Maracaibo akalla ana samun kwanaki 260 da ake zuba walkiya da tsawa ba kakkautawa a cikin shekara.

Da dare tsawon sa'o'i tara hasken dubban walkiya da ake yi ke haskaka samaniyar yankin.

Hakkin mallakar hoto Bernard Castelein NPL
Image caption Kafin ruwan sama da walkiya da tsawa a kogin Brahmaputra na Indiya

Wasunmu sun san yadda ake tsananin walkiya da tsawa a yankunan da layin da ya raba duniya biyu ya ratsa (equator), inda ke da tsananin zafin rana kuma a duk tsawon shekara ake jin rugugin samaniya.

An dauki Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo da ke tsakiyar Afrika a matsayin babban birnin cida ko tsawa na duniya.

Kuma kauyen Kifuka da ke kan tsauni a kasar wanda ake samun walkiya sau 158 a fadin wuri mai murabba'in kilomita daya a kowace shekara yake zaman wurin da aka fi walkiya a duniya.

Wannan shi ne bayanin farko da ake da shi kafin a sake nazarin bayanan wasu wuraren a duniya.

Ko ka san cewa: kusan a ce ba yi walkiya ko da sau daya ba a yankin kusurwar duniya na arewa da kuma na kudu a shekara ta 2014.

Kuma kamar yadda alkaluman hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka NASA, suka nuna yankin kwarin Brahmaputra na gabashin Indiya mai nisa ya fi samun yawan walkiya a cikin wata tsakanin watan Afrilu da na Mayu a lokacin da ake samun cida da tsawa sosai a yankin.

Sai dai kuma yankin tafkin Maracaibo na kasar Venezuela ya samu gurbi a littafin bajinta na duniya (Guiness Book of World Records), saboda samun walkiya fiye da ko ina, inda ake yin walkiyar sau 250 a fadin murabba'in kilomita daya a kowace shekara.

Walkiyar na raguwa a lokacin watannin rani na Janairu da Fabrairu kuma ta fi tsanani a lokacin da damuna ta fi karfi a watan Oktoba.

A wannan lokaci ne na shekara za ka iya ganin an yi walkiya akalla sau 28 a cikin duk miniti daya.

Hakkin mallakar hoto ben cc by 2.0
Image caption Gabar teku mai kusurwa-kusurwa kan haddasa walkiya da tsawa sosai

Tsawon shekara da shekaru masana suna ta kokarin gano dalilan da suka sa aka fi samun tsananin walkiya da cida da tsawa a wannan yankin.

A shekarun 1960 an dauka yawan ma'adanin karfen yuraniyom (uranium) da ke karkashin kasa a yankin shi ke jawo yawan walkiya.

A kwanan nan kuma sai masana kimiyya suke ganin sinadarin methane na mai da ke karkashin kasa a yankin shi ya kara wa iskar da ke kan tafkin yanayin da ke sa ta jawo haduwar sauran abubuwa da ke haddasa walkiya da tsawa ko cida.

Duk da cewa ba daya daga cikin wadannan dalilan biyu da aka tabbatar su ne ke haddasa wannan abu.

Amma dai ana ci gaba da danganta lamarin ga yanayin kasa da ya kunshi tsaunuka da gabar teku mai kusurwa-kusurwa da kuma na iskar yankin, kamar yadda Dakta Daniel Cecil na hukumar kula da yanayi da karkashin kasa da ta duniya (Global Hydrology and Climate).

Hakkin mallakar hoto nasa
Image caption Taswirar wuraren da aka samu walkiya daga 1995 zuwa 2013

''Samun irin wannan yanayi na daban a bangaren kasa da iska abu ne da zai iya samar da yanayin iska da kuma na sanyi da zafi da zai iya karfafa yanayin da za a samu cida da tsawa da walkiya.''

A arewa maso yammacin Venezuela tafkin da ya fi kwarara a kudancin Amurka wato Latin Amurka yana bi ne ta birnin Maracaibo ya shiga tekun Karebiyan (carribbean).

Idan gari ya waye ranar da ake da ita mai zafi a yankin sai ta sa ruwan tafkin da na wuraren kusa da shi masu dausayi ya yi zafi turirinsa ya rika tashi sama.

Idan kuma dare ya yi iskar teku sai ta rika tura wannan iska mai dumi ta hadu da iska mai sanyi da take fitowa daga tsaunuka.

Wannan iska mai zafi sai ta tashi ta haifar da gagarumin hadari da yake kai wa kusan tsawon kilomita 12 a sama.

Daga waje za a iya ganin wannan bakin hadari a kamar tarin gajimare kawai kawai amma a cikinsa abubuwa na ta wakana ana gumurzu.

Inda kwayoyin ruwa da ke cikin iska mai sanyi ko tiririn da ke tashi na hadarin suke karo da kwayoyin kankara a cikin iska mai sanyi, sai a samu haduwar sinadaran lantarki da ke haddasa wannan kara ta cida da tsawa da kuma walkiya.

Hakkin mallakar hoto nasa
Image caption Hoton lokacin da walkiya ta faru wanda tashar tattara bayanan samaniya ta dauka

Bayan wannan kara ta tsawa da kuma hasken walkiya da ake gani idan an samu wannan gumurzu na kwayoyin ruwa da kankara da iska a cikin wannan gagarumin hadari sai a ga tasirin hakan na zubar ruwan sama da kankara sun biyo baya.

Hasken wannan walkiyar da ake gani a wannan wuri yana iya kaiwa har nisan kilomita 400 kuma an ce a masu tukin jirgin ruwa na zamanin mulkin mallaka suna amfani da hasken walkiyar wajen ganin hanya.

Karfi da tsawon lokacin wannan ruwa da tsawa da walkiya sun sa an samu labarai iri daban-daban.

Hakkin mallakar hoto Robert Harding World Amagery Alamy
Image caption Arizona wuri ne da ake walkiya sosai

Tsawon shekara 17 hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka da hadin gwiwar takwararta ta Japan suka samar da na'urorin tattara bayanai da nazarin walkiya da tsawa da ke wakana a doron kasa a duniya.

Da bayanan da ake tattarawa ta wannan hanya ne masana kimiyya suka iya gano wuraren da aka fi samun tsananin walkiya da tsawa a duniya.

Dakta Cecil ya ce, ''ina ganin mataki na gaba na samar da tauraron dan-adam na nazarin yanayi abu ne da zai bayar da sha'awa,'' domin man da shirin auna yawan ruwan sama a yankuna masu zafi na hadin gwiwa tsakanin Amurka da Japan yake gudanar da aikinsa a samaniya ya kare yanzu ya dawo doron duniya.

A 'yan shekaru masu zuwa za a samar da tsare-tsare na samar da kayayyakin aikin nazarin wuraren da ake walkiya a tauraron dan-adam a sassa daban-daban na diuniya.

Wannan zai ba mu damar sanin abubuwan da ke wakana game da walkiya akai akai fiye da yadda muke samun bayanai a yanzu.

Muhimmancin sanin hanyoyin hasashen walkiya da tsawa na kara karuwa yayin da jama'ar duniya ke kara karuwa musamman a kasashe masu tasowa, inda yuwuwar mutane su yi aiki a waje ke karuwa kuma ga shi ba su da wadatattun kayan kariya daga daga illar walkiya da tsawa.

Hakkin mallakar hoto Rob Hill
Image caption Walkiya a Monument Valley a Amurka

Aikin nazarin walkiya na duniya (WWLLN) ya kunshi na'urori 70 da da aka kakkafa a jami'o'i da cibiyoyin bincike wadanda ke nadara duk wani motsi na walkiya.

Farfesa Robert H. Holzworth wanda ke jagorancin shirin daga Jami'ar Washington ya ce, cibiyoyin da ke kasa suna taimaka wa bayanan taurarin dan-adam da ke samaniya.

Tashar tattara bayanai ta kasa za ta iya ganin duniya baki daya ba tare da wani bata lokaci ba kuma a kai a kai, wanda wannan abu ne da ba wata tashar tauraron dan-adam da za ta iya a nan gaba ko ta yi a baya.

A daya bangaren, idan har ana son nadar bayanan walkiya ta hanya kamar irin ta iskar rediyo, hakan na bukatar kayayyakin da suka fi na yanzu.

Saboda haka tashoshin da suke a watse a doron duniya ba za su iya ganin kowane ziri na walkiya ba idan mitsitsi ne a cikin hadari, wanda kuma tauraron dan-adam zai iya gani.

Ga duk wanda yake da burin bin diddigin walkiya da tsawa, shirin tattara bayanai na tashoshin da ke sassan duniya (WWLLN) ya sani suna samar da taswirar wuraren da ake walkiya a duniya.

Duk wanda yake da kwarin gwiwa da karfin hali zai iya kai ziyarar bude ido tafkin Maracaibo wanda yana nan har yanzun nan domin ganin yawan walkiya da tsawar da ake yi a wurin.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The most electric place on Earth