Dabarar bera ta adana maniyyi don gasa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Bera yana da hanyar da yake adana maniyyinsa ta yadda ba zai tsufa ya baci ba, ko da ba ya saduwa da tamata, har lokacin da za su yi gasa.

Melissa Hogenboom ta bincika mana yadda abin yake

Tsohon maniyyi ba labari ne mai dadi ba.

Yawan dadewar maniyyi a marena yawan lalacewarsa. Kuma 'ya'yan da aka haifa daga wannan maniyyin za su iya gamuwa da matsaloli na lafiya.

Saboda haka abu ne mai muhimmancin gaske maniyyi ya kasance bai tsufa ba a kwalatai.

Dabbobi da dama da ke shayar da 'ya'yansu nono (mammals) suna da hanyoyi ko tsarin yadda suke adana maniyyinsu ba tare da ya tsufa ba.

Misali wasu masana kimiyya suna ganin wasa da mutum ke yi da jikinsa domin biyan bukata ta sha'awar jima'i na daga irin wadan nan hanyoyi, domin zai zubar da maniyyin da ya tara kafin ya fara lalacewa.

A tsakanin dabbobi masu shayar da nono kamar bera akwai abubuwa da dama da ke wakana wajen adana maniyyin.

Hakkin mallakar hoto wikimedia hans hiliwaert
Image caption Sabon maniyyi yana da muhimmanci wajen haihuwar 'ya'ya masu lafiya

Domin gane yadda maniyyi yake lalacewa ko rage inganci idan ba a jima'i sosai ko kuma ma an jima ba a yi ba, masana kimiyya suna gudanar da nazari kan maniyyin beran gida.

Masanan sun duba maniyyin beran da ya kai wata biyu bai yi jima'i ba da kuma wanda ya yi ba dadewa.

Abin da masu binciken suka gano ya ba su mamaki, domin sun ga babu bambanci tsakanin maniyyin berayen biyu a kan sabunta ta bangaren kwayoyin halitta da ke ciki da ma duk sauran wani abu.

To me ya sa haka?

Beraye suna da dabarun da suke yi na tabbatar da maniyyinsu ya kasance da ingancinsa da sabunta idan ba bu tamatan da za su sadu da ita.

Wannan ya hada da inzali a kai a kai da kuma zubar da shi ta fitsari. Ga alama ma akwai hanyar da suke adana shi da sabuntarsa a marenansu.

Hakkin mallakar hoto Stephen DaltonNPL
Image caption Gasa ba illa ba ce

''Hanyar zubar da maniyyin ta yin inzali a kai a kai ba bera ba ne kadai yake yi wasu dabbobin masu shayar da nono ma na yi,'' kamar yadda jagorar binciken Renee Firman ta Jami'ar Western Australia ta bayyana.

An wallafa sakamakon binciken a mujallar Evolutionary Biology.

Haka kuma masanan sun duba bambancin gasar da ake yi tsakanin mazajen beraye ta yawan maniyyi.

A nan ne tamatan bera da take cikin ganiyar lokacin sha'awar jima'i za ta yi ta saduwa da maza daban-daban a dare daya inda kowannensu zai zuba mata maniyyi.

Wannan tarin maniyyin da dukkannin mazajen suka zuba mata ne za su yi gogayya a cikinta inda maniyyin namijin da ya fi kyau zai shiga mahaifarta ta haifi 'ya'ya da shi.

Firman ta ce, a wannan lokacin mazan beraye suka fi kasancewa da maniyyi mai kyau da manyan marena.

Ta ce, ''muna tunanin hakan na kasancewa ne saboda mazan na cikin matsi na ganin sun samu maniyyi mai kyau a wannan lokacin.''

Wannan kamar yazo daidai da yanayin cacar raful (raffle), yawan tikitin da ka saya yawan damarka ta cin cacar. Haka shi ma maniyyi yake.

Akalla a wurin beraye, gasa ba aba ce maras kyau ba. Domin tana abubuwa lalacewa, wato su kasance da sabunta da inganci.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Sperm has evolved to stay fresh