Hanyoyi shida da dabbobi ke amfani da ido na bogi

Hakkin mallakar hoto john flannery cc by 2.0

Idanuwa za su iya kasancewa masu kyau. Ababan ban mamaki. Masu jan hankali. Za kuma su iya kasancewa masu yaudara, musamman ma a tsakanin dabbobi, inda wasu da dama ke bayyana ido na bogi a jikinsu.

Lesley Evans Ogden ta yi bincike

Wurare masu kama da ido, wadanda ake gani a jikin kifaye da kwadi da malam-buda-mana-littafi da tsuntsaye da kwari da makamantansu, sun dade suna daukar hankalin masana tarihi, tsawon daruruwan shekaru, kuma wani sabon nazari a kan wannan abu ya bayyana sabbin abubuwan ban mamaki.

Hakkin mallakar hoto John Flannery CC by 2.0
Image caption Me ya sa wannan tsutsa ke kama da miciji
Tsutsa mai kama da kan miciji

Ko da yake an san cewa halittu kan yi amfani da irin wannan alama ta idanu domin hana wasu kwarin masu kai musu hari shammatarsu, amma ba a san me ya sa hakan ba, kuma me ya sa ake da irin idanuwan na bogi iri daban-daban.

Da farko dai har yanzu ba a san yadda dabbobin suke kwaikwayon idanuwan gaskiyar ba, da kuma ko sauran dabbobi suna daukar wannan alama mai kama da ido kamar yadda mutum yake ganinta.

Halittu da yawa suna amfani da wannan alama ta ido a matsayin wani gargadi ga wasu halittun da ke kai musu hari suna cinye su, su kare kansu daga gare su, ko su jinkirta harin.

Wannan zai iya kasancewa saboda masu kai musu harin ba su san siffar wannan alama ba, ko kuma saboda masu kai harin suna ganin kamar wata halitta ce suke kallo wadda ta fi su girma ko ta fi su hadari.

Amma wasu masu binciken sun yi nazari sosai ba tare da sanya ra'ayin yadda mu mutane muke daukar wannan alama ta idanu ba.

Dakta John Skelhorn na jami'ar Newcastle ta Birtaniya ya lura da yadda tsuntsaye suke yi a lokacin da tsutsar da ake kira katafila (caterpillar) da Ingilishi ke yaudararsu ta yin irin wannan alama ta idanu, inda take yi kamar idan miciji.

Nau'in irin wannan tsutsa da dama suna yin wannan alama ta idanu, saboda haka ne Dakta Skelhorn da abokan aikinsa suka yi kamar tsutsar (da kayan abincin), sannan suka yi mata fenti na irin wannan alama ta idanu a sassa daban-daban na jikinta.

Suna ganin tsuntsaye za su ji tsoron kai hari kan tsutsar da ke da wannan alama ta ido a kanta saboda za su dauka miciji ne.

Haka abin ya kasance, domin tsutsar da ke da wannan alama ta idanu a wasu sassa na jikinta ba kanta ba, ba ta tsoratar da tsuntsayen ba.

Wannan binciken ya tabbatar da nazariyyarsu cewa, tsuntsaye na tsoron kai hari kan tsutsar da ke da irin wannan alama a kanta, wadda ke sa ta yi kama da miciji.

Hakkin mallakar hoto Robert Pittman CC by 2.0
Image caption Wadannan idanuwa ne ko wata alama ce kawai
Malam-buda-mana-littafi wanda ke kwaikwayon idonsa

Sai dai wadansu binciken da aka yi an gano akasi ko kishiyar hakan, domin malam-buda-mana-littafi suna yin wannan alama ta ido, wadda ke fitowa karara, da wani zane na daman da ke karya wa halittun da ke kama shi gwiwa su kama shi maimakon kwaikwayon idon wasu halittun.

Abin mamaki ana ganin wannan alama ta ido sosai a jikin fukafikin malam-buda-mana-littafi. Kuma girmansu daban-daban da kuma haskensu amma kuma ba a san me ya sa hakan ba.

Domin binciken wannan Dakta Martin Stevens a jami'ar Exeter ta Birtaniya, ya yi nazari kan yadda tsuntsaye a zahiri suke ganin malam-buda-mana-littafi wanda yawanci suke ci.

Domin sauy yadda tsuntsaye suke kallon wannan alama, ayarin Dakta Stevens ya lillika malam-buda-mana-littafi na bogi masu zane da launi na alamar idanuwan iri-iri daban-daban a jikin bishiyoyi,

Masanan sun yi hasashen cewa idan har kwaikwayon idanu abu ne mai muhimmanci, tsuntsaye za su kiyaye da duk wata alama da ke da launin baki a tsakiya da fari a kewaye idan aka kwatanta da yadda za su kalli alamar da ke da launin fari a tsakiya baki kuma a kewaye.

Masu binciken sun ga tsuntsayen sun kauracewa dukkanin alamar biyu.

Daga nan kuma sai masu binciken suka sauya siffar alamar idanuwan daga kewayayya zuwa mai kama da gida-gida amma kuma ba su sauya launin ba, nan ma dai babu bambanci kan yadda tsuntsayen suka kaurace.

Nazarin ya nuna cewa bayyanar abu karara ne, ba lalle kwaikwayon alamar ido ba ke da muhimmanci.

''Amma duk da haka ba mu gano lamarin ba gaba daya har yanzu,'' in ji Stevens

Binciken nasa an yi shi ne da malam-buda-mana-littafi na bogi, maras motsi kuma alamar idon ana ta ganinsu a bayyane.

Masanin ya ce, a yanayi na gaske, malam-buda-mana-littafi yawanci yana bude fukafikinsa ya nuna wannan alama ta idanu, ''kuma kawo yanzu ba wanda ya iya yin wani gwaji na hakan,''

Amma nazarinsa ya nuna cewa tsuntsaye za su guji wata alamar da ta bayyana sosai da girma da kuma bambanci da yawa amma kuma siffar alamar ba abar damuwa ba ce a wurin tsuntsayen.

''Wannan alama ta ido ta jawo bincike da dama, amma har yanzu akwai abubuwa da yawa da ba a fahmta a kai ba, da kuma abin da ya sa alamr ke da bambanci da yawa tsakanin dabbobi ko halittu,'' in ji Stevens.

Hakkin mallakar hoto Photoshot Holdings Ltd Alamy
Image caption Wannan nau'in kwadon yana da alamar idanuwa na yaudara a bayan kafarsa
Kwado da wannan alama ta yaudara

Bayan yin manyan idanu, wasu dabbobin za su iya kumbura wannan alama ta idanu, domin tsoratarwa da kuma harzuka abokan gabarsu.

Wani kwado da ake samu a kasar Brazil wanda ake kira da Ingilishi Physaalaemus nattereri ko Eupemphix nattereri yana da wani zane mai kama da alamar idanuwa a saman kafafuwansa na baya.

Wannan alama tana da amfani a lokacin da tsuntsaye ke neman kai wa kwadon hari ko kuma wani kwaron ruwa da ke iya cin kwadon.

A duk lokacin da wadannan dabbobi suka tun kari kwadon sai ya daga kafafuwansa na baya ya bayyana wannan ido na bogi.

Wannan ido na bogi wani bangare ne dabarar fada na kwadon.

A tsakiyar wannan alama ta ido akwai wani bakin faifai wanda yake dauke da guba.

Gubar na da karfi sosai ta yadda wadda kofa daya da za ta fitar da ita, za ta iya kashe beraye 150, kuma an san yadda mujiya take amayo kwado gaba dayansa, saboda wannan guba.

Saboda haka idan wadannan idanuwa na bogi ba su kori dabbar da za ta kawo wa kwadon hari ba, gubar da ke cikinsa za ta iya.

Hakkin mallakar hoto Malcolm Schuyl Alamy
Image caption Alamun ido abu ne da ake yawan gani a jikin kifaye
Kifin da ke yi wa abokan gabarsa shashatau

Sabbin abubuwan da aka gano a kan abin da ya sa dabbobi suke amfani da wannan alama ta ido ba sun tsaya ba ne a kan wadanda za mu iya gani a saukake.

Kuma suna nuna cewa idanuwan na bogi ba kawai suna kare hari ba ne, suna ma iya yi wa abokin gaba shashatau ( su kauce su bi wani wurin).

Kifi yana amfani da wannan alama ta idon bogi da yawa, yawanci a can karshen bayan idanuwansa na gaske.

Kafin yanzu bincike kadan ne aka yi kan sanin amfanin wannan alama ta ido a cikin ruwa.

Wani abu da aka gano shi ne kifayen suna amfani da wannan alamun ido wajen karkatar da hankalin wata dabba da za ta kawo musu hari, ko dai gaba daya ko kuma karkatar da dabbar zuwa wani sashe na jikin kifin maras rauni.

Duk da cewa an kai ksan shekara dari da aka gano wannan bayani to amma har yanzu babu wata sheda mai karfi a kan hakan.

Wannan dan lokaci da kifin zai yaudari dabbar da ke son kawo masa hari, zai ba si dama ya kauce wa hari wato ya tsere.

A shekara ta 2013 Dakta Sami Merilaita, na jami'ar Abo Akademi da ke Turku a Finland ya jarraba hakan.

Kifayen suna kirkirar wata alama ce ta kifi na bogi mai wannan alama ta ido a wani sashe na jikin kifin na bogi, dayan ya kasance ba abin da ya same shi domin ganin yadda kifin zai mayar da martani.

Masana sun gano cewa a yawancin lokaci kifin yana kai hari ne kan idon na bogi

Masanan suna ganin alamar idon tana sa wanda ya kawo harin ya kai hari wannan wuri da alamar idon na bogi take bisa tunanin cewa ainahin kan kifin yake kai harin.

Idan alamun idon suka sa mai kai harin ya dauka kan kifin da yake son kaiwa harin ne, mai kai harin zai sa ran wanda ya kaiwa harin ya gudu ta hanya daya, wanda kuma a zahiri yana guduwa ne ta daya hanyar .

Wannan yaudara ta dan lokaci za ta iya ba wa kifin da aka kai wa harin dama ta dan lokaci ya gudu, in ji Merilaita.

Hakkin mallakar hoto Jurgen Otto
Image caption Idanuwan bogi na gizo-gizo mai siffar dawisu
Kyakyawar siffar gizo-gizo mai kamannin dawisu

Wannan alama ta idanuwan bogi ba kawai tana amfani ba ne wajen kare hari, halittu suna amfani da ita wajen jan hankali domin saduwa (jima'i).

Nau'ukan gizo-gizo suna da idanuwa da yawa. Amma wani guda daya yana da wannan ido na bogi da yawa a sashen baya na jikinsa.

Kamar dai dawisu da aka kwatanta wannan gizo-gizo da shi saboda kamannin launinsa, shi wannan gizo-gizo da ake samu a Australiya yana da wadannan alamu na ido kuma masu launi mai kyau, inda yake amfani da su wajen jan hankalin mata.

Wannan nau'i na gizo-gizo ba kawai yana bayyana wanna alama mai kama da idanuwa ba ce wajen jan hankalin mata kada, yana da wata rawa da yake yi mai ban sha'awa da birgewa duka domin jan hankalin mace.

Dakta Madeline Girard ta jami'ar Berkeley a Amurka da abokan aikinta a jami'ar New South Wales a Sydney da ke Australiya sun yi nazari kan wannan kwarkwasa a dakin binciken kimiyya.

Wannan nau'i na gizo-gizo ya kan dauki kusan minti 50 yana kwarkwasar jan hankalin mace, da salo iri-iri kafin su ki ga saduwa.

''Abin da ke ban mamaki shi ne mutane ba sa tsammanin ganin irin wannan rawa da kwarkwasa a tsakanin wannan 'yar karamar halitta,'' in ji Dakta David E. Hill editan mujallar Peckhamia, ta bayanan irin wannan nau'i na gizo-gizo.

Hakkin mallakar hoto Rose Mendoza by 2.0
Image caption Abin da ya fi jan hankalin tamatar dawisu a jikin namiji?
Rodi-rodin kwarkwasa na jelar dawisu

Ba za mu iya maganar wannan gizo-gizo da ake kamantawa da dawisu ba, ba tare da ambatar shi kansa dawisun ba, dabbar da ake ganin ita ce ta fi amfani da wannan alama ta ido na bogi .

Haka shi ma dawisun kamar wannan gizo-gizo yana amfani da wannan halitta wajen jawo hankalin mace domin saduwa.

Dawisu yana da sama da gashi 150 wanda kowanne kuma yana da irin wannan alama ta ido mai daukar hankali da ban sha'awa.

Masana sun yi nazari kan mazaje 34 da ke neman mace, inda suka duba damar da kowanne yake da ita ta nasarar shawo kan matar ta amince da shi, inda suka duba abin da ke daukar hankali mace a wannan alama da ke gashin nasa har ta yarda da shi.

Binciken ya nuna idan wannan alamar ido ta jikin gashin na dawisu (namiji) har kusan 170 ta kasance tana da rodi-rodin launin baki ko fari, farin jinin namiji a wurin mace ba shi da yawa sosai.

Idan ana son karanta wannan a harshen Ingilishi a latsa nan Six ways animals use fake eyes