Abubuwan da ba ka sani ba game da kura

Hakkin mallakar hoto chris gomersall alamy

Ba kamar yadda aka dauka ba, kura dabba ce da ke neman na kanta, ba cima-zaune ba ce, ko 'yar kalen naman da wasu dabbobi suka ci suka rage ba, duk da irin maganganun da watakila ka ji a kanta. Kuma dabba ce mai basira sosai.

Henry Nicholls ya yi mana nazari.

Yadda ake daukanta: Kura ta yi kaurin suna na cewa tana cin abubuwan da suka mutu ne kawai, wani lokacin zaki, wani lokacin ma har mutum. Takan fashe da dariya. An tsane ta. Kuma mata-maza ce, duka wannan ba haka ba ne?

Gaskiyar yadda take: Kura dabbar dawa ce da ke bukatar mutuntawa ba tsana ba. Yawanci tana farautar dabbobi ne da kanta a matsayin abincinta amma ba kalen abin da wasu suka kashe suka ci suka bari ba.

Kura tana da basira sosai, da katuwar kwakwalwarta kuma tana daya daga cikin dabbobi masu cin nama da ke da tsarin zamantakewa wanda ba kowane jinsi yake da shi ba.

Mata sun fi maza iko kuma matan ba su da kofar farji, sai wata halitta da za a iya cewa dan-tsaka amma kuma mai kama da cikakken mikakken azzakari. Menene ba za a so ba?

Hakkin mallakar hoto heather paul

Wannan rubutun na yi shi ne domin surukata (babar matata). A 'yan makwannin da suka wuce ta biyo ta gidanmu, sai na ji ta fara maganganu na batanci a kan kura, tana cewa halitta ce da ba ta da wani amfani.

Kamar yadda duk wani da na kirki zai yi, sai na kwantar mata da hankali tare da nuna mata akasin yadda ta dauki wannan dabbar dawa.

Ina ganin wannan mummunan kallo da ake yi wa kura zai iya hana mu fahimtar yadda kura take a zahiri.

Daya daga cikin maganganun batanci da ake yi a kan kura shi ne, ita dabba ce da take cin abincin da aka rage, ko satar yawancin abincinta daga wasu dabbobin kamar zakuna kuma a wani lokacin tana tone kabari domin neman gawar mtane.

Wannan ba haka yake ba, akalla a game da kura. Masanin harkokin gidan namun daji Hans Kruuk, wanda ya yi aiki a gandun naman daji na Ngorogoro da ke Tanzania tun a shekarun 1970, ya gano cewa zaki shi ne ma ya fi kale ko neman dabbar da kura ta kashe domin ya ci, sabanin yadda ake dauka.

''Babu wasu dabbobi ko ina a fadin Afrika, inda ba sa farautar kashi 50 cikin dari na abincinsu,'' in ji kwararriyar masaniya a kan kura mai rodi-rodi, Kay Holekamp ta jami'ar jihar Michigan a East Lansing da ke Amurka.

Za a iya cewa dai nau'ukan kura mai ratsi-ratsi ko kuma mai fata launin kasa, wadanda yawanci suke cin mushe su ne suke kalen abincinsu daga abin da wasu manyan dabbobin dajin suka kashe amma ba, nau'in kura mai rodi-rodi ba, wadda tana iya kama dabbar da ta linka ta hudu girma.

Hakkin mallakar hoto uwe skrzypczak
Image caption Kura ta fafari garken jakin dawa

Mun san wannan ne saboda Holekamp da abokan aikinta sun yi nazari a na'urar daukar hoton kokon kai na kuraye da yawa. Wannan ya kuma bayyana cewa nau'in kura mai rodi-rodi suna da babbar kwakwalwa a goshinsu, bangaren da a kai yake da tasiri wajen yanke hukunci ko nuna basira.

Wannan yana da muhimmanci domin ana samun wannan nau'in kura a tare garke-garke kuma da yawa.

Dan karimin garken kura mai rodi-rodi da za a gani ya kai babban garken zakuna ko kerkeci ko karen dawa.

Hakkin mallakar hoto blickwinkel alamy
Image caption Kuraye suna da manya-manyan garke kuma suna da tsarin zamantakewa na daban a tsakaninsu

''Garke mafi girma da da muka taba gani ya kunshi kuraye 72,'' in ji Holekamp.

Wani garken kuma da take nazari a kai kuma ya kunshi kuraye 130, ko da yake ba ga wani garken mai wannan yawan ba a wuri daya a lokaci guda kuma.

''Wannan ya fi girma idan aka yi la'akari da yawa, fiye da duk wani garke na wata dabba mai cin nama.''

Idan aka yi la'akari da wannan, ba za a yi mamaki ba ganin yadda muryar kukan kura mai rodi-rodi sosai ta fi ta sauran nau'ukan kuraye ko ma zakuna.

Daya daga cikin fitattun kukanta shi ne ''whoop''. Ga wanda ba shi da ilimi a kanta zai dauka wannan kuka ne da ke da wata manufa maras kyau ko aikata wani mugun abu, musamman idan ta yi shi a cikin dare a Afrika.

To amma ga wadanda suka san ta, sun san cewa hanya ce kawai ta sanar da 'yan uwanta ga inda take.

Kowace kura tana amfani da sauti da wari da kuma kamanni wajen gane wata da ke danginsu.

''Ka duba yadda hakan za ta auku a tsakanin kuraye daban-daban guda 130,'' in ji Holekamp.

Wannan ba karamin aiki ba ne na basira, amma kuma haka suke yi ba tare da wata matsala ba.''

Wanene namiji?

An san yadda mata suka fi maza iko a cikin jinsin kura mai rodi-rodi, wanda kuma ba haka abin yake ba a tsakanin sauran jinsinan kurar biyu, wato mai ratsi-ratsi da kuma mai fatarta launin ruwan kasa kawai.

A tsakanin matayen kuraye masu rodi-rodin, akwai tsarin girmamawa mai tsanani.

Mace da take matsayin babba, wato wadda tafi iko a dangi ko garke ita ce ke samun kaso mafi girma na duk wani nama da aka kaso, wanda hakan zai taimaka mata haihuwa da sauri ba tare da wata matsala ba fiye da sauran matan da suke kasa da ita.

Amma kila abin da zai ba da mamaki a game da matayen jinsin kurar mai rodi-rodi shi ne yadda farjinta yake.

Daga can cikinta dai babu wani bambanci tsakanin matan da sauran matan dabbobi masu shayar da nono.

Amma idan aka kalli matancinsu daga waje abin ya sha bamban matuka da na sauran dabbobi.

Hakkin mallakar hoto danita delimont alamy
Image caption Kura tana da farji mai kama da azzakarin da ya mike

''Matan ba su da kofar farji kamar na sauran dabbobi, sai abin da za a iya cewa dan-tsaka wanda ya yi kama da azzakarin da ya mike sosai, wanda ta kofarsa ne suke fitsari da saduwa da kuma haihuwa,'' in ji Holekamp.

Wannan wata jumla ce da ta taba fada karara, saboda ta furta min kalmomin ne cikin kasa da dakika takwas kacal.

''ita ce macen wata dabba da ke shayarwa kadai da ba ta da kofar farji,'' ta kara da cewa, domin ta kara rudar da ni kawai. ''Wannan abu ne da yake na daban.''

Ba mace ba namiji?

Yanayinsu ya fita daban, domin tsawon daruruwan shekaru mutane sun dauka cewa wannan nau'i na kuraye mata-maza ne (ba mace ba namiji).

Ta wani fannin wannan abu ne da za a iya fahimta. Idan ka ga wannan kura mai rodi-rodi tana komawa cikin raminta da nunuwa da suka ciko, watakila za ka dauka mace ce.

Idan kuma wannan kurar da nonuwanta suka ciko ta sake fitowa ta tarbi wata daga cikin danginta da katon azzakari da ya mike kila ka sauya tunani.

''Wannan ya dade yana rikitar da mutane tsawon lokaci,'' in ji Holekamp.

A yayin saduwa (jima'i), wannan halitta mai kama da azzakari sai ta kwanta, amma duk da haka sai kuren (namiji) ya cusa azzakarinsa ciki.

Idan kana ganin wannan abu ne mai wuya, to ka yi tunanin yadda dan kurar da ya kai nauyin kilogram daya da rabi zai fito ta wannan 'yar kofa kuma.

Hakkin mallakar hoto blickwinkel alamy
Image caption Kuraye na saduwa

To wai ma menene ya sa wannan farji ya kasance haka? Mutane masu wayo da dabara da da yawa sun dade suna tunani mai zurfi a kan wannan tambaya.

Amma ''ba wanda ya fahimci muhimmancin kasancewar farjin a haka,'' in ji Holekamp.

Wani hasashe shi ne, watakila kasancewarsa haka yana taimaka wa dangi gane junansu.

Saboda za ka ga wannan nau'i na kura suna wata gaisuwa, inda biyu ke tsayawa kusa da kusa kai da kafa suna shinshina wannan halitta mai zaman farjin (azzakarin) junansu.

Amma ana ganin wannan ba lalle ya zama hakan ba, domin idan har kura za ta iya gane 'yar uwarta ko danginta ta hanyar amfani da hankalinta (hanci da ido) me zai sa ta bukaci wannan abu mai kama da azzakari?

'Yan mata da ransu ya baci

Wani abu kuma da ake ganin ko shi ne zai fi dacewa, shi ne, tamata tana da girma da kuma fada.

Saboda haka ana ganin a lokacin da suke girma suna samun yawan kwayoyin halitta na jima'i na namiji, wanda a dalilin hakan wannan halitta take girma sosai.

Haka kuma ana tunanin wannan farji na daban yana bai wa mace iko a kan baban 'ya'yanta.

Bayan kalubalen da namiji yake gamuwa da shi wajen cusa azzakarinsa ta kofar wannan halitta, ta nan ne tamatar take fitsari kuma.

Saboda haka tamatar da ba ta dade da saduwa da wani kure ba, za ta iya sauya ra'ayinta.

''Tana da damar zubar da maniyyin kuren gaba daya,'' in ji masaniya Holekamp.

Hakkin mallakar hoto imageBroker alamy
Image caption Akwai tambaya ne?

Ko da za ka tsaya kana mamaki, to kasan dai cewa dukkanin wannan bayani da na yi ban gaya wa babar matata ba, wadda idan ka tuna ita ta taso da wannan zance lokacin da ta zo tana kushe kura.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The truth about spotted hyenas