Gwaggwon biri: Na yin ja da baya ga rago

Hakkin mallakar hoto C HOBAITER

Mu mutane muna da dabi'a da ta danganci maganarmu wadda a ko da yaushe muka furta wata kalma yawanci mukan yi hakan ne domin wani yana saurarenmu ko kuma muna so ya saurare mu, ya san abin da muka fada, gwaggwon biri ma na da wannan dabi'a.

Wannan dabi'a ce da 'yan uwanmu ko kuma masu kama da mu na kusa wato birai suke amfani da ita su ma.

A irin hakan ne gwaggwon birin da wani abokin fadansa ya kora, ya kan yi wata kara (waa) da ke nuna cewa bai bayar da kai bori ya hau ba.

Hakkin mallakar hoto APL Alamy
Image caption Gwaggwon biri tun yana yaro yake fara fada

A duk lokacin da uka yi satar sauraron karar da birai ke yi za mu gane cewa suna yinta ne domin amfanin abokansu da kuma makiya ko abokan fadansu. Sukan duba wanene ke saurarensu kafin su yi wani kuka.

Haka kuma kowane irin abinci akwai irin kara ko kukan da suke yi domin sa, kuma ana iya gane su da irin karar da suke yi a lokacin da suke fada.

Wannan na faruwa ne kusan a ko da yaushe, domin gwaggwon biri yana da fada sosai musamman ma mazaje.

Amma kuma duk wanda ake kwara idan suna fada ba kasafai yake bayar da kai ba ya gudu, domin ya kan yi kara domin neman taimako daga wani dan uwansa.

Hakkin mallakar hoto Zute LightfootAlamy
Image caption Bayan fada sukan share wa juna jikinsu

Har sukan iya zuzuta karar ma idan har suka san dan uwan nasu yana kusa domin ya dauka ana cutarsa sosai ya yi saurin taimaka masa.

Masu bincike yanzu suna ganin sun gano yadda za su iya fayyaci bambancin kararsu daban-daban, tare da bayyana yadda gwaggon biri ke kokarin yaudara ko shawo kan dan uwansa.

Wannan kara da suke yi kowacce tana da irin amfaninta, wanda ya dogara ga wanda suke nufi ya ji ta.

Karar ta hada da ta mika wuya (idan an fi karfinsa), ko shan alwashin daukar fansa ko kuma neman taimako daga na kusa.

Amma a wasu lokutan gwaggwon birin da wani abokin fadan ya kwara yakan yi kuka tare da wata kara wadda ake kira ''waa''. Kuma ba wanda ya san amfani ko ma'anar karar.

Domin gano dalilinta, Pawel Fedurek na jami'ar Neuchatel da ke Switzerland da abokan aikinsa sun saurari karar tarin birai 54 a dajin Budongo na Uganda.

A nan ne suka lura cewa a duk lokacin da gwaggwon biri ya yi kuka, bayan kara uku zai yi wannan kuka ko kara ''waa''.

Duk birin da ya yi wannan kara kuwa ga alama zai rama abin da abokin fadansa ya yi masa ne, maimakon neman sasantawa.

Hakkin mallakar hoto C HOBATTER
Image caption Suna magana da junansu

''Wannan dabi'ar za ta iya nuna cewa wannan birin da aka kwara a lokacin da suka yi fada, ba zai ba da kai bori ya hau ba a wurin wanda suka yi fadan, wanda kuma hakan ka iya daukaka matsayinsa a cikin sauran birrai,'' in ji Fedurek.

Duk da cewa sasantawa na da muhimmanci sosai a zamantakewar birrai, to amma samun matsayi saboda karfi ma wani abu ne mai muhimmanci.

Saboda haka wannan kara ta ''waa'' ka iya sa biri ya kai wannan matsayi na iko a cikin birai.

Sai dai kuma wanda aka fi karfin ba lalle ba ne ya yi wannan kara (waa) ta neman taimako daga 'yan uwa, idan wanda ya ci zalin nasa ko ya doke shi, yana da matsayi na iko a tsakaninsu, saboda haka wannan ne zai sa, ko ya mika wuya ko kuma ya ki.

Wadannan kara masu dan bambanci da biran ke yi, ka iya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da yadda karshen wannan fada zai kasance, kamar yadda Fedurek ya ce.

An wallafa sakamakon wannan bincike ne a mujallar halayyar dabbobi ta Animal Behaviour.

Image caption Gwaggwon biri kan yi kirari (kara) domin nuna ya isa

Kamar yadda Fedurek ya fahimta, yayin fada karar da gwaggwon birin da aka fi karfi yake yi, yana yi ne domin ya jawo hankalin 'yan uwansa da ke kusa domin su kawo masa agaji, amma kuma idan aka ji ya yi karar ''waa'' to yana yi ne domin ya kori wanda yake cutarsa ne.

Yawan karar da gwaggwon biri yake yi kusan tana da iyaka, ba zai iya yawan wadda mutane ke yi ba.

Amma wannan binciken ya sa ana ganin cewa sadarwarsu tana da wuyar fahimta fiye da yadda aka dauka a da.

Kamar dai mu mutane gwaggwon biri zai iya amfani da kuka ko kara mai sauki domin sadar da sako fiye da daya.

''Ga alama akwai dangantaka ta asali ga sanadin harshe da mutum yake amfani da shi da kuma dangantakar biri da mutum,'' in ji Fedurek

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Down but not out, a beaten chimp utters a "waa bark"