Uban da ke kashe jariransa maza

Hakkin mallakar hoto blickwinkel alamy

wani sabon bincike ya gano cewa iyaye maza na wani nau'in biri mai siffar gizo-gizo suna kashe jariransu maza domin kishi da hana gasar saduwa.

Ga nazarin da Melissa Hogenboom ta yi.

Ta'adar iyaye su kashe jaririnsu maza da gangan a tsakanin dabbobi masu shayarwa ba wani sabon abu ba ne, haka kuma za su iya kashe dansu namiji ko mace.

Sai dai wani sabon bincike da aka yi a kan wani nau'in biri mai siffar gizo-gizo (spider monkey) ya gano cewa jarirai maza ne kawai iyaye suke kashewa.

Kuma wani abin mamaki shi ne uban da zai kashe jaririn shi ne ya ubansa fa ba ma ta maganar nau'i ba.

Sama da nau'in dabbobi masu shayar da 'ya'yansu nono 119 ne suke da ta'adar kashe 'ya'yansu na cikinsu, kuma wadannan dabbobi sun hada da nau'in birai 35.

Sai dai a tsakanin nau'in birran masu kama da gizo-gizo, sau biyar ne kadai a baya aka ga irin wannan ta'ada a tsakaninsu.

Amma yanzu a wani sabon nazari da aka yi a daji da ya dauki dogon lokaci an sake gano wuri uku inda aka ga wannan abu ya faru.

Yanzu masu binciken suna ganin bisa ga dukkan alamu abu ne da yake faruwa sama da yadda aka yi tsammani a baya.

Rahoton wanda aka wallafa a mujallar labaran birrai (Primate Journal), ya nuna cewa iyaye maza hallaka 'ya'yansu maza saboda fargabar gasar jima'i tsakanin mazajen da ke garken.

Idan akwai sabbin jarirai maza da yawa, gasar za ta yi tsanani. Haka kuma binciken ya nuna cewa, wannan abin da aka gano zai iya fayyace abin da ya sa ake samun bambancin yawan maza da mata a tsakanin wannan nau'i na biri.

Hakkin mallakar hoto Natureworld Alamy
Image caption Uwaye mata suna cikin firgici idan aka kai wa 'ya'yansu maza hari

Abu ne mai wahala a ga lokacin kisan jariran maza, abin da kuma yana bukatar nazari na tsawon lokaci a dawa.

Masu bincike na bukatar sanin yadda kowace dabba take zamantakewa da sauran 'yan uwanta na garken, domin sanin muhimmancin 'yan uwantaka a tsakaninsu.

A binciken na yanzu Sarah Alvarez daga jami'ar Complutense ta Madrid a Spaniya da abokan aikinta sun yi nazari a kan wasu nau'i uku na birran masu siffar gizo-gizo a Ecuador da Colombia da kuma Belize.

Dukkanan gungun wadannan birai sun saba da kasancewar masu bincike a muhallinsu, kuma dukkanin biran sun san su.

An ga wani lokaci daya da aka ga wani namiji yana dukan wata uwa mai suna Kuao wadda take da dan jariri.

Ko da yake ba a ga namijin birin ya yi wani abu na kokarin kuntatawa jaririn ba a lokacin, amma bayan kwana bakwai an gan shi a yashe yana kuka da rauni da yawa a jikinsa.

Bayan kwana daya kuma sai ya mutu saboda raunukan da aka ji masa, amma ba a gano wanda ya kashe shi ba.

Bayan wata tara kuma sai aka sake ganin wannan matar biri Kuao da wani sabon jaririn, abin da ke nuna kila jim kadan bayan kashe wancan jaririn ta sake daukar ciki.

Hakkin mallakar hoto Murat Ceven Alamy
Image caption An samu kisan 'ya'ya maza sau takwas yanzu

A wani lamarin kuma an ga wani jaririn birin an barshi har ya mutu bayan wani mummunan hari da aka kai masa, ita kanta uwar da daya daga cikin sauran mazajen su ma da raunuka a jikinsu, abin da ke nuna cewa an yi gumurzu ne.

Masu binciken sun kuma ga wata uwar tana rike da wani jaririn da ba shi da uwa, wanda kuma daga baya masu binciken suka ceci wannan jari da suka gano uwarsa suka ba ta abinta.

Sun ce ba don sun cece shi ba da watakila ya mutu saboda raunukan da ke jikinsa suna da yawa.

Masu nazarin suka ce ba za a kawar da tsammanin cewa wasu dabbobin suna kai musu hari ba, amma kuma irin yanayin raunin da suke gani a jikin jariran kusan iri daya ne da na wadanda suka gani na irin wadannan nau'in birai.

Kisan jariran maza yana sa uwa ta koma saduwa da namiji, amma idan ba haka ba ita tamatar wannan biri (spider monkey) yawanci tana haihuwa ne bayan shekara uku amma kuma hakan yana raguwa zuwa wata tara zuwa goma idan danta ya mutu.

Wannan bayani ne da ya danganci nazariyyar da aka yi a kan kisan 'ya'ya. A wani bincike na kwanan nan wanda aka wallafa a mujallar kimiyya ta Science masu nazari sun duba dalilan da iyaye maza suke kashe jarirai maza.

A wani cikakken rahoto kan nau'in dabbobi masu shayar da nono 260, da suka hada da nau'i 119 da aka sani suna wannan dabi'a.

Ayarin masanan sun yanke shawarar cewa a yawancin lokaci biran maza suna kashe jariran 'ya'yansu maza idan suna fuskantar gasa wajen samun matan da za su sadu da su.

Hakkin mallakar hoto Elise Huchard
Image caption Gwaggon biri namiji ma ya kan kashe 'ya'ya maza

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan These spider monkeys kill their male infants