Biranyar da ke kula da nakasasshiyar 'yarta

Hakkin mallakar hoto danta delimont alamy

A wani abu da ba a taba ganin irinsa ba, an ga wata tamatar gwaggon biri tana kula da 'yar karamar 'yarta nakasasshiya a daji, maimakon ta yi watsi da ita.

Melissa Hogenboom ta yi mana nazari.

An ga wannan abu ne a gandun dajin tsaunukan Mahale a kasar Tanzania, inda wannan 'yar gwaggon biri wadda aka yi mata inkiya da XT11 ta rayu tsawon wata 23.

Ita ce 'ya ta shida a wurin uwarta mai shekara 36, wadda ake kira da suna Christina.

Hakkin mallakar hoto Michio Nakamura
Image caption Nakasasshiyar daga hagu tare da wata sa'arta

Bisa ga dukkan alamu wannan 'yar biranya wadda ke da nakasa iri-iri a tare da ita, ta rayu ne tsawon dan lokacin da ta kai na wata 23, saboda kulawar da ta samu daga mahaifiyar tata, wadda ba don hakan ba da ba a jin za ta kai wannan lokacin ma.

Masu bincike a wannan rahoto da aka wallafa a mujallar labaran birai mai suna 'primates' sun ce uwar ta rika kula da 'yar wadda take da nakasa sosai, wadda kuma ba ta iya yin wasu abubuwa na kula da kanta.

An ga alama ba ta iya cin 'ya'yan itace ko wasu tsirrai, saboda haka gaba daya ta dogara ne a kan nonon uwar fiye da lokacin da ya kamata a yaye duk wani dan biri.

Hakkin mallakar hoto Michio Nakamura
Image caption Tana da wani kumburi a cikinta

Masu rahoton sun ce, ''muna ganin, rashin cin abincin nata ya kasance ne saboda ba ta iya tafiya sosai, kuma ga alama ta gamu da matsalar rashin abinci mai gina jiki saboda ta dogara ne a kan nono kawai, lokacin da ya kamata ta kara da sauran kayan abinci bayan ruwan nonon.''

Bayan nakasar da take da ita ta zahiri, wannan 'yar biranya tana kuma da kaba a cikinta (kamar yadda za a iya gani a hoto na sama) da matsala a lakarta da kuma karin dan yatsa wanda ba ya aiki a hannunta na hagu.

Idanuwanta kamar ba komai a ciki sannan bakinta ya dan bude, kuma ba ta iya zama ba tare da an tallafe ta ba.

Tana iya rike gashin mahaifiyarta, amma kafarta ba ta da karfin tsayawa, saboda haka galibi a goye take ko kuma ta makale uwar tana reto.

Hakkin mallakar hoto Takuya Matsumoto
Image caption Wani lokaci idon nakasasshiyar kamar ba komai kuma bakinta sai ya dan bude

Kula da wannan nakasasshiyar 'yar tata, ya sa Christina ta sauya dabi'arta, inda ta daina zuwa cin kwari a kan bishiya, saboda ko da yaushe tana rike da 'yar tata.

''Uwar 'yar da take da nakasa sosai tana aikatuwa fiye da sauran uwaye, saboda dole ne ta kula da 'yar matuka,'' in ji masu rahoton.

A wani lokacin yayar nakasasshiyar mai shekara 11 tana taimaka wa uwar, inda take dan wasa da ita, ta rene ta kuma ta rika daukanta.

Akwai ma lokacin da ita uwar ce da kanta take ba yayar kanwar ta kula da ita, wanda wannan ba abu ne da aka saba gani uwa (ta gwaggon biri ) ta yi ba,'' in ji Michio Nakamura, na jami'ar Kyoto ta Japan, wanda aka rubuta rahoton da shi.

''Idan yayar tana kula da kanwar sai uwar ita kuma ta hau bishiya ta na cin 'ya'yan itace,'' kamar yadda ya sheda wa BBC.

To amma locain da ita kuma yayar ta haifi tata jaririyar sai ta daina tallafa wa uwar da wannan reno.

Ba dama dangin ita wannan nakasasshiya su taimaka wajen kula da ita, domin abu ne da ba a saba yi ba a tsakaninsu.

Watakila saboda uwar ta fahimci cewa, ba za su iya bai wa nakasasshiyar kulawar da ta dace ba, domin ba su san irin bukatunta ba.

Ba a san abin da ya yi sanadin mutuwarta ba, amma ana ganin kila matsalar na da nasaba da karancin abinci mai gina jiki ne.

Hakkin mallakar hoto Takuya Matsumoto
Image caption A wani lokaci yayarta ma tana kula da ita

Ko da yake ba wani bakon abu ba ne a haifi biri da nakasa, amma duk da haka sau biyu kawai aka taba ganin an haifi gwaggon biri da wata matsala ta jiki.

Dukkaninsu biyun, uwayensu ne suka yi watsi da su, sai aka tsinto su mutane suka rika kula da su.

Daya ya mutu yana da watanni 17, yayin da dayan ya mutu bayan ya kai watanni 24, bayan an yi ta masa karin jini.

Yadda aka ga wannan dabi'a ta yadda wannan uwa ta kula da 'yar tata mai fama da nakasa, wannan alama ce da ke nuna cewa, dabi'a ce da ta dade a tsakanin halittun da kakannin birai.

'Mun lura cewa yadda yayar ta rika taimaka wa da kula da nakasasshiyar 'yar karamar kanwar tata abu ne da zai iya ba da haske kan yadda kula da nakasassu ta samo asali,'' in ji Nakamura.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The wild chimpanzee who cared for her child with disability