Kwaron da ya fi jure za fi a duniya

Hakkin mallakar hoto amouroux monalisa prod spl

Kwaron da ya fi jure za fi a duniya, yana rayuwa ne a hamadar Sahara, inda yake fitowa yayin da zafin rana ya kai lamba 70 a ma'aunin digirin Selshiyas (celcius), ya shiga tsintar gawarwakin kwarin da zafin ya hallaka yana ci.

Nick Fleming ya yi nazari kan wannan halitta

Tsananin zafin rana a lokacin da ta take a hamadar Sahara ya fi karfin yawancin dabbobi su iya jurewa.

To amma ba ga wannan nau'in kwaron da ake rayuwa a hamadar Sahara din ba (Cataglyphis bicolor), wanda yake rabewa a inuwar kasar bakin raminsa ba har zuwa lokacin da zafin ya yi tsanani ga sauran kwari.

A wannan lokacin ne shi kuma yake fitowa kiwo inda zai rika kwasar gara da gawarwakin kwarin da zafin ranar ya halla.

Shi wannan kwaro an ce yana iya kiwo a lokacin da zafin ranar ya kai lamba 70 a ma'aunin Selshiyas (celcius), amma ko shi ma na wani dan lokaci ne zai yi kiwon.

Akalla irin kwari uku ne aka san suna iya fitowa su yi kiwo a lokacin da zafin rana ya kai lamba 60 ko sama da haka a ma'aunin Selshiyas, a hamadar Sahara da Nahib da kuma ta Australia.

Cataglyphis yana hamadar Sahara, yayin da Ocymyrmex yake rayuwa a hamadar Nahib wadda ke tsakanin kasar Angola da Afrika ta Kudu, inda shi kuma Melophorus yake zama a hamadar Australia.

Hakkin mallakar hoto Estella Ortega Antweb.org
Image caption Ocymyrmex barbiger ya kusan zama na daya a gasar

Sai dai kuma ba wai jure wa zafi ta yadda kwaro zai iya fitowa ya yi kiwo ba ne na dan lokaci, maunin sanin kwaron da ya fi juriyar zafin ranar a duniya ba.

A lokacin da yake bincike kan kwarin da suka fi wannan bajinta ko baiwa, Van Sherwood, wanda yanzu masanin kwari ne a rundunar sojojin Amurka, ya yi nazari kan yawan zafin da kwaro ba zai iya tsira ba da kansa a dakin kimiyya.

Gwajin da aka yi ya nuna Ocymyrmex barbiger ya suma sakamakon tsananin zafi, bayan da ya kai dakika 25 a zafin da ya kai lambar digiri 55 a ma'aunin Shelshiyas, shi kuwa Melophorus bagoti zai iya jurewa zafin da ya kai lambar digiri 54 a ma'aunin Shelshiyas har zuwa tsawon sa'a daya.

Shi kuwa cataglyphis bicolor, wanda ke rayuwa a hamadar Sahara ya kasance wanda ya fi jure zafi, inda ya iya jure wa zafin da ya kai lambar digiri 55 da digo daya a ma'aunin Selshiyas.

A lokacin da zafi ya fi tsanani da rana yana iya barin raminsa na tsawon wasu 'yan mintina ya je ya yi kiwo, yayin da dabbobin da su kuma su ke farautarsa suke buya a lokacin saboda zafi.

Yadda yake nazarin inda rana take akai-akai da yadda yake kirga sawunsa daga raminsa zuwa duk inda ya je da kuma yadda yake iya jin kanshi da wari da kyau, hakan ke sa ya iya dawo wa raminsa da sauri ba tare da shi ma zafin ranar ya hallaka shi ba.

Hakkin mallakar hoto Martin Rietze
Image caption Hamadar Sahara mai tsananin zafi

Muhimman abubuwa uku ne da dabi'u suke sa wannan kwaro da sauran ire-irensa suke iya harkokinsu a cikin tsananin zafin hamada, wanda zai iya hallaka sauran dabbobi cikin sauri.

Na farko, su wadannan kwari suna da sauri, inda kusan wanda ya yi kusa da su shi ne da yake tafiyar mita daya a dakika daya.

Tsawon kafarsu ya sa zafin da yake a kasa ya ragu da digirin Selshiyas bakwai da wanda yake samunsu a jiki, wato saboda suna nesa da kasa.

Sannan kuma suna iya rabewa a jikin karan ciyayi ko saiwoyi, inda suke rage zafin da ke jikinsu a jikin saiwoyin.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The ant that is the hottest insect in the world