Yadda biri ke cin zali

Hakkin mallakar hoto Claire Hamilton

Wani biri ya yi bazatta inda ya harzuka saboda sun hada hanya da kunkuru, ya zari sanda ya doki kunkurun kuma ya dauki dutse ya kwada masa.

Melissa Hogenboom ta ga yadda lamarin ya faru ga rahotonta.

A muhallan birai a Afrika ta kudu, yawancin biran jinsin da ake kira capuchin suna zaune lafiya da sauran dabbobi 'yan uwansu, wadanda suka hada da kunkuru.

Sai dai kuma a wani lokacin biran sukan yi dari-dari tare da muzgunawa jinsin kunkurun da ke zamantakewar da su, in ji Claire Hamilton ta hukumar da ke kula da wannan daji na Afrika ta kudu.

Biran sukan mare su, su kwada musu dutse, a wani lokacin ma har sukan zauna a kansu.

Amma kuma da safiyar wata rana a cikin watan Nuwamba na shekara ta 2012, Hamilton ta ga wani abu wanda ba ta taba gani ba, inda wasu birai biyu, mace da namiji, da ke cikin bacin rai suka wuce ta.

Ganin wani kunkuru a hanyar tasu sai biran suka huce haucinsu a kansa.

Tamatar birin ce sai kawai ta zari sanda ta doki kunkurun a kokon bayansa.

Ganin hakan bai yi mata ba sai ta dauki dutse kuma ta kwala masa a kokon bayan, in ji Hamilton.

Jami'ar ta ce wannan shi ne karon farko da na taba ganin biri (capuchin) ya yi amfani da wani abu a matsayin makami.

Dukkan wannan abu ya faru ne cikin dakika 15 kawai. Kuma kokon bayan kunkurun ya dan bantare, inda nan da nan ya ja baya, kuma boye kansa a cikin kokon.

Hamilton wadda ta ga yadda abin ya faru keke da keke ta yi kokarin daukar wadannan hotunan a lokacin.

Hakkin mallakar hoto Claire Hamilton
Image caption Matar birin kenan cike da bacin rai, tana bin mijinta a lokacin da suka hadu da kunkurun
Hakkin mallakar hoto Claire Hamilton
Image caption Kafin ta dauki sandar ta doki kunkurun kenan

Hakkin mallakar hoto Claire Hamilton
Image caption Lokacin da ta doki kunkurun da sanda

Hakkin mallakar hoto Claire Hamilton
Image caption Sandar ba ta sami kunkurun ba sosai, ga alama biranyar na neman wani makamin ne kuma.

Hakkin mallakar hoto Claire Hamilton
Image caption Lokacin da take kwala wa kunkurun dutse

Hakkin mallakar hoto Claire Hamilton
Image caption Ga dutsen nan a gefen dama bayan da ta kwala wa kunkurun, wanda ya mayar da kansa cikin kokon bayan

Hamilton ta ce bacin rai ne kawai ya sa biranyai ta yi wannan abu, amma ba wata mugunta ba, domin ba a san irin wadannan biran da mugunta ba.

Duk da cewa sukan yi amfani da abubuwa amma ba kasafai suke amfani da su a matsayin makami ba.

''Wannan shi ne karon farko da na taba ganin irin wannan birin ko ma duk wani biri, yana amfani da wani abu a matsayin makami na sosai,'' in ji Hamilton.

Ta kara da cewa, ''na kan gan su suna amfani da sanda da dutse domin kwakwalar abinci, kuma sukan yi amfani da su wurin wasa, amma ba domin kare kansu ko kai hari da su ba.''

Abin mamakin ma shi ne, haka kawai ba wani abu da kunkurun ya yi mata ta yi masa wannan duka.

Amma wannan ba yana nufin wannan jinsin birin yana da fada ba ne in ji Hamilton.

Ta ce, ''suna da kokarin kare 'yan uwansu daga hari kuma har ma sukan yi fada sosai idan lamarin ya kai haka, amma ban taba ganin irin wannan birin (capuchin) yana rikici ba, haka kawai ba tare da wani dalili ba.''

An wallafa wannan bayani a mujallar abubuwan da suka shafi birai ta Neotropical Primates.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Monkey hits tortoise with stick then throws rock at it.