Gwaggon birin da ya fi girma a duniya

Hakkin mallakar hoto Gordon Buchanan BBC

Wannan kakkarfan jinsi ne na gwaggon biri shi ne nau'in birin da ya fi kowane biri girma a duniya. Amma kuma ba kowa ya ma san da shi ba duk da wannan matsayi na shi, wanda kuma a dajin Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo kadai ake samunsa.

Hakkin mallakar hoto Gordon Buchanan BBC
Image caption Jami'an kula da namun dajin na sanya ido sosai a kan manyan wannan jinsi na biri wadanda ake kira Mugaruka.

Manyan mazajen wannan nau'in biri su kan kai nauyin kilogram 225 kuma sun lillinka mutum karfi.

Hakkin mallakar hoto Gordon Buchanan BBC
Image caption Wata uwa mai suna Chimanuka da danta na hutuwa

Duk da cewa an san gwaggon biri da yin abubuwa na razanarwa da nuna karfi, har ya kan buga kirjinsa domin nuna ya isa tare da ihu da fada, amma shi wannan biri yawanci akwai kwanciyar hankali a wurin da yake.

Hakkin mallakar hoto Julie Moniere BBC
Image caption Wani dan karamin gwaggon biri da ake kira Karibu kenan. ma'anar sunansa a Swahili barka da zuwa

Yawanci wannan jinsi na biri yana cin tsirrai ne da 'ya'yan itatuwa, kuma a wani lokacin ya kan ci kwari. Iyalan wannan nau'in biri yawanci sukan kunshi mata da matasa karkashin jagorancin babban namiji daya.

Dan abu kadan aka sani game da wannan biri idan aka kwatanta da danginsa, wato gwaggon birin da ke rayuwa a kan duwatsu, kuma ba a san guda nawa ne ma suka rage a dawa ba.

Hakkin mallakar hoto Patrick Evans BBC
Image caption 'Yan kauye na tara itace domin yin gawayi a kusa da gandun dajin Kahuzi-Biega

Ana ganin yawansu ya ragu sosai a 'yan shekarun nan sakamakon farautarsu da mutane ke yi da kuma kawar da dazuka da ake yi, wanda dukkanin wadannan abubuwa ne da suka karu sosai a yayin yakin basasa na Jamhuriyar Dumokradiyyar Kongo.

Hakkin mallakar hoto Julie Moniere BBC
Image caption Jami'an kula da gandun daji da dabbobin dawa

Tarin jami'an kula da gandun daji na sintirin kare biran daga mafarauta a dajin Kahuzi-Biega

Hakkin mallakar hoto Julie Moniere BBC
Image caption Wata uwa daga jinsin gwaggon birin na Mpungwe

Wasu masana na ganin cewa ta hanyar yawan bude idanu na kare muhalli da dabbobin dawa ne kadai za a tabbatar da dorewar wannan nau'i na gwaggon biri a dawa.

Hakkin mallakar hoto Gordon Buchanan BBC
Image caption Matashin gwaggon biri mai suna Pori yana cikin tunani

Wasu daga cikin gwaggon biran da ke dajin Kahuzi-Biega tuni suka saba da mutane, yayin da masu kula da namun daji na kokarin ganin biran sun saba da kasancewar mutane a kusa da su.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The elusive giants living deep in the forests of DR Congo