Gyaren da ya mayar da kan ruwa kamar doron kasa

Hakkin mallakar hoto Nature Picture LibraryAlamy Stock Photo
Image caption Wani kwaro na gudu a kan ruwa

Tafiya a kan ruwa ba karamar baiwa ba ce da halitu kadan ne suke da ita, to amma a wurin wani gyare kan ruwan kamar doron kasa ne. Ko ta yaya ya lakanci wannan siddabaru?

Alex Riley ya yi nazarin wannan baiwa

Malcolm Burrows yana cin abincinsa na rana a birnin Cape Town na Afrika ta Kudu, a lokacin ya ji wani kara. Thwack! Yana zaune ne a kusa da wani dan tafki da ke zagaye da 'yan tsirrai. Karan ya ci gaba. Thwack! Yana ta cigaba. Thwack! Thwack! Thwack!

Daga kan ruwan ne wannan kara ya ke fitowa. Da ya matsa kusa ya duba, sai ya ga, a saman ruwan da ke daukar ido ga wasu 'yan bakaken abubuwa, kowan ne yana tsalle da sauri daga nan zuwa can.

Wadannan kwari wani nau'i ne na gyare da ake samu a yankuna masu dumi na Florida da Afrika ta Kudu da Australiya.

Daga nan sai Burrows da abokan aikinsa suka samo ragar kamun kifi suka kama kadan daga cikin kwarin, suka kai su wani dakin binciken kimiyya da ke kusa, suka fara daukar hotunansu da wata kyamara mai saurin daukar hoto kamar walkiya.

Da wannan kyamara masu binciken sun iya gano yadda kwarin suke iya tsalle a kan ruwa (kamar a kasa) ba tare da sun nitse ba.

To ta yaya kwarin suke iya wannan tsalle a kan ruwa, kuma mai yasa suka lakanci wannan abu sosai haka?

Hakkin mallakar hoto malclm burrows
Image caption Wani kawro na gudu a kan ruwa

Za mu fuskanci tambaya ta buye ne da farko. Kamar dai yadda watakila aka gani a wani shirin talabijin na BBC mai suna ''Life'', akwai manyan dabbobi kamar wata agwagwa (grebe) da wani nau'in kadangare (basilisk ko Jesus Lizard) dukkanninsu suna iya gudu a kan ruwa zuwa dan takaitaccen wuri.

Sai dai ainahin kwararrun masu tafiya a kan ruwan 'yan kananan halittu ne kamar kwari, wadanda suka hada da sauro, wadanda sukan iya tafiya da gudu da wasu ma har har da nutso, na tsawon lokaci.

Ko da yake su kwari ba sa iya tsalle daga cikin ruwa, ma'ana su daka tsalle daga kan ruwan su tashi.

Saboda darewar da ruwan ke yi, samansa kamar danko ne a wurin wadannan halittu. Kwari suna fafutuka ne su cire kafarsu daga wannan danko.

To amma shi wannan nau'in gyare, wanda ke tsalle a ruwa, lamarin ba haka yake ba a wurinsa, domin shi yana da wata halitta da ruwa ba ya iya masa haka.

Hakkin mallakar hoto plumedbasiliskrunsonwater

To wani abin rikitarwa kuma wannan kwaro ba ma gyare ba ne idan aka tsaya aka lura da halittarsa sosai.

''Abin kamar wata shashantarwa ce da batar da mutum,'' in ji Burrows. Ya ce, wadannan kwari sun fi kama da fara. Amma dai ba shakka 'yan mitsi-mitsi ne, domin tsawonsu kusan rabin santimita ne kawai (centi metre).

Tun da suna zaune ne a ramuka da ke kusa da kududdufi da koramai, a yanayin rayuwarsu ta da kafin sauyin halittarsu zuwa yadda suke yanzu ba shakka sun gamu da matsin lamba na neman tsira daga ruwa.

''Suna cikin rayuwa ta hadari,'' in ji Burrows. '' Ambaliya za ta iya cin gidajensu (rami) idan ba su yi hankali ba.''

Amma kuma babban hadarinsu shi ne makwabtansu. ''Suna makwabtaka ne da tsutsar da ke juyewa ta zama wani kwaro kamar hangara, wadda ke cin kwari ba sassauci,'' kamar yadda Burrow ya bayyana.

Saboda ba su da fukafuki da ke aiki kamar na sauran kwari, ba za su iya tashi su gudu ba. To amma saurara za su iya tsalle! Kokarin guje wa wannan tsutsa yawanci ya kan kai su ga fadawa kan ruwa.

To idan suka fada kan ruwan, ta yaya suke kauce wa, wannan danko na kan ruwa da ke kokarin rike kafafun sauran halittu?

Kamar fari danginsu na tudu wadannan kwari, kafafunsu na baya suna da kauri saboda yin tsalle. Saboda girman kafar ta su ta baya ba za su iya amfani da ita ba wurin tafiya ta yau da kullum.

Suna nade kafar ne daga gwiwa, amma za ka ganta can a dage ba ta taba kasa, har sai lokacin amfaninta ya zo - tsalle a ruwa.

Wanna na nufin shi wanna nau'in gyare yana amfani da kafafunsa hudu ne daga cikin shida, idan yana tafiya ne a kasa.

Wadannan kafafuwa na baya ba kamar na sauran fari suke ba. Suna zaman amfani ne a cikin ruwa.

Kamar yadda kyamarar Burrows ta nuna a hotunan da ya dauka na bidiyo,, idan kafafuwan suka tokari saman ruwa sai daga can kasan kafar wasu abubuwa kamar takalmi mai fadi su bude.

''Wadannan abubuwa sai su zama kamar takalmi a kafar tasu,'' in ji Burrows.

Kamar itacen tukin kwale-kwale, idan ya yunkura zai yi tsalle, saboda fadin da suka yi a kan ruwan sai ya samu damar yunkurawa da karfi ta yadda zai iya tsallen sosai, (zai zama kamar yana dogara abin ne a saman ruwan).

Bayan ya taso sama daga kan ruwan da gudun zuwa sama da tsawon mita biyu a cikin dakika daya, sai wani abu kamar roba ya nade wannan takalmi da ya fito a kafar tasa tare da sauran sangalalin kafar daga gwiwarsa.Ya zamanto kafar ta koma sama a dage.

Da zarar sun tashi sama sai su rika kada wa baya kuma za su iya kaiwa sama da tsawon santimita goma a tsallen.

Za a ga wannan kamar ba wani tsawo ba ne, amma kamar mutum ne ya yi tsallen sama da kafa 100 daga inda ya ke a tsaye.

Kuma a tuna fa daga wurin da kusan a ce yana kokarin dawo da su kasa ne ya hana su tashi (saman ruwa).

Ta yaya wannan dan karamin kwaro yake iya yin wannan tsalle da karfi haka?

Wannan duka ya dogara ne ga motsin da naman kafarsa ke yi ne a hankali, kamar dai yadda maharbi ya ke jan bakansa a hankali.

To kamar haka ne kwaron yake janye kafarsa a hankali ya tattara tsokarta, ya tara karfin a wurin gwiwarsa sannan ya watso kafar baya da karfi.

Burrows ya ce, ''abin kamar yadda maharbi yake ne, idan ya hada danyen itace da busashshe ya yi baka, to irin wannan bakan ya fi kwari domin ba ya karyewa.''

Saboda haka ne idan gyaren ya harba kafar sai ya tashi da karfi sosai, kuma wannan shi ne irin abin da ke faruwa da harshen hawainiya.

Inda ta ke fitar da harshe da karfi kuma kamar walkiya idan za ta kama kwaro.

Kankantar jikinsu da gabobinsu (kirar jikinsu) masu karfi da kuma rashin tsarin hanyoyin gudanar jini kamar na mutane, su ke kare su daga samun wata illa yayin tashi saman.

Burrows ya ce ''yadda wadannan kwari suke wannan tsalle a ruwa ba karamin abin mamaki ba ne.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Forget walking on water, this insect jumps on it