Abin da ba ka sani ba game da giwaye

Hakkin mallakar hoto DenisHuotNPL

Ga wasu abubuwa uku da ake cewa game da giwa: akan ce tana jin tsoron bera, sannan ba ta manta abu da wuri, kuma wai giwaye suna da makabarta. Daya daga cikin wadannan maganganu shakka babu gaskiya ce. Ko ka san na almara a ciki ?

Henry Nicholls ya bincika

Shaci fadin da ake yi game da giwa: Giwa na jin tsoron bera. Giwa tana iya gane kusan duk wani abu na wata giwar musamman danginta ko bayan mutuwa. A kan ce idan lokacin mutuwarta ya yi ta na kai kanta makabarta. Wai suna zaman makoki.

Kuma wai giwa na da dangantaka ta halitta da wata 'yar karamar dabba kamar zomo wadda wasu ke kiranta rema ko agwada (hyrax).

Gaskiyar magana game da giwa : Giwa tana tsoron kudan zuma.

Tana da kwakwalwa (hadda ) da ta ke sani da tuna abubuwa sosai. Maganar cewa giwaye na da makabarta ba al'amara ce, amma dai ba shakka giwaye na abin da za a iya cewa makoki idan wata ta mutu.

Kuma ba giwa ba kadai duk abubuwa masu rai suna da dangantaka da ita wannan 'yar karamar dabba mai kama da zomo (hyrax).

Hakkin mallakar hoto Chris MattisonNPL
Image caption Dabbar da wasu ke cewa tana da dangantaka ta asali da giwa (hyrax da Ingilishi)

Ko kasan cewa giwa na da alaka da wannan dabba (da muka yi maganarta a baya mai suna hyrax da Ingilishi) mai kama da zomo da ake samu a wasu kasashen Afrika? Wannan na daya daga cikin maganganun da mutane ke son yadawa game da giwa?

Wannan dai nazari ne kawai ba wani mai zurfi ko wata kwakkwarar sheda ba. Domin ai kusan komai ma na da alaka da wannan halitta.

Dalilin musanta wannan alaka da giwar da wannan 'ay karamar dabba shi ne; farko dai maganar na nuna dangin giwa ce ta zamanin da ta nan kusa kusa. Amma kuma ga shi dabbobin biyu kusan kowa hanyarsa daban (a dangantaka) kusan tsawon shekara miliyan 65.

Na biyu kuma shi ne kila maganar alakar tasu ba daidai take ba, domin nazarin kamannin tsarin kwayoyin halitta ya nuna cewa giwa ta fi kusanci da wasu madaidatan halittu biyu na ruwa (dugongs, manatees), wadanda ko daga kamanni suna da siffar giwa, maimakon ita waccan dabba mai kusan kama da zomo.

Hakkin mallakar hoto Jurgen FreundNPL
Image caption Idan za a fadi gaskiya wannan dabbar (dugongs) ta fi kama da giwa amma ba waccan mai kama da zomo (hyrax) ba

Ra'ayinmu na son danganta abin da yake babba da wani karami, shi ne kuma ya sa muka yarda cewa giwa na tsoron beraye.

Wannan magana za ta iya kasance ta samo asali ne tun zamanin Pliny the Elder (marubuci kuma masanin falsafa na zamanin daular Rumawa), wanda a littafinsa mai suna 'The Natural History, ya ce ''a dukkanin dabbobi ba abin da giwaye ba sa so kamar bera.''

Walt Disney ya dauki wannan fahimta inda a wasan dabbobin (circus) da yake yi da ake cewa Dumbo, inda beran da yake kira TimothyQ. Ya tayar da hankalin giwar da ake wasan da ita, kafin daga baya ya zama abokinta.

To amma a nan idan muka yi nazari mene ne ya jawo wannan tunani namu da muke cewa wai giwa tana tsoron bera?

Craig Bruce na kungiyar Landan ta kare dabbobin dawa a duniya ya ce, ''akwai duk irin wadannan labaran kanzon-kurege da almara da ake yi, na cewa wai bera ya hau kan toron giwa da gudu, amma sai ka ga babu wata cikakkiyar sheda ta tsoron beran da ake cewa giwa na yi.

Abin da yake tabbas shi ne giwa ba ta kaunar kudan zuma.

Hakkin mallakar hoto Karl AmmannNPL
Image caption ''Zuma?Zuma? a'a a'a ba zan tsaya ba !''

A lokacin da aka sanya wa wasu tarin giwaye da ke hutawa a karkashin wata bishiya kukan gungun kudan zuma ta lasifika (amsa kuwwa), sai aka ga giwayen suna sulalewa ko kuma ma su gudu.

An yi wannan ne da kuma sauran wasu abubuwan da aka gano, domin wani shiri na duba ko za a iya amfani da kudan zuma wajen hana giwaye banna a gonaki a Afrika.

To ya kuma maganar cewa giwa ba ta manta abu (tana da kwakwalwa)?

To a game da wannan lalle giwa ba ma haddace inda wasu muhimman abubuwa suke a hanya ba da kuma hanyar da ta saba bi, hatta 'yan uwanta ba ta manta su kuma tana mu'amulla ta zamantakewa a garkenta sosai.

Masu bincike a gandun namun daji na Amboseli na Kenya, a shekarun 1990, sun yi amfani da muryar rediyo (ta kukan giwaye) domin gano yadda giwaye suke sadarwa a tsakaninsu.

Hakkin mallakar hoto DenisHuotNPL
Image caption Giwa ba ta tsoron bera

Daga cikin abubuwan da suka yi, sun kunna wa iyalan wata giwa da ta mutu kusan shekaru biyu da suka wuce (murya ta rukoda) kukanta ta lasifika.

Sai giwayen suka taru a kusa da lasifikar su ma suna mayar da martanin kukan, wanda wannan alama ce ta zamantakewa mai karfi.

A wani wurin kuma wata giwar da ta bar danginta ta koma wani garke, danginta na farkon da ta bari suna amsa kiranta (kuka) shekaru 12 bayan ta barsu.

Game da maganar cewa giwaye suna da makabarta inda tsoffinsu suke zuwa su mutu, to wannan babu wani dalili ko sheda da za su sa a yarda da hakan.

Gaskiya ne a kan ga tarin kasusuwan giwaye a wuri daya, a nan kuwa masana na ganin fari (rashin abinci) da farauta ka iya zama sanadin hakan.

Akwai kyakkyawar sheda daga gwajin da aka yi da kuma lura da rayuwar giwayen, wadda ke tabbatar da cewa giwaye na makokin 'yan uwansu idan sun mutu.

Hakkin mallakar hoto iony.head npl
Image caption Wata giwa na duba 'yar uwarta da rai ya yi halinsa

A littafinta na nazarin yadda giwa ta ke iya rike abu a kanta ba tare da ta manta ba, har zuwa tsawon lokaci, mai suna 'Elephant Memories', wata mai rajin kare dabbobin dawa Cynthia Moss, ta tuna da yadda ta dauko wani kashin mukamuki na wata giwa, uwar garke da ba ta dade da mutuwa ba ta kawo shi sansaninta.

Bayan kwanaki da yawa, iyalan wannan giwar, wata rana sun zo wucewa ta ksa da sansanin sai suka ga wannan kashi, inda suka tsaya suka duba shi.

Daga cikinsu dan marigayiyar mai shekara bakwai shi ne ya tsaya, ya dade yana duba kashin bayan da sauran suka cigaba da tafiya.

Daga nan sai Moss da abokan aikinta suka shirya wasu gwaje-gwaje na nazarin wannan basira ko kwakwalwa ta giwaye domin fahimtar lamarin sosai.

Da aka jera musu abubuwa uku da suka hada da, katako da kokon kai na giwa da kuma wani dan bantaren hauren giwa, giwayen da aka shiryawa wannan gwaji, sun mayar da hankalinsu a kan guntun hauren, bayan shi kuma sun fi nazarin kashin kokon kan fiye da katokan.

Duk da cewa masu binciken ba su iya gudanar da wani nazari ko gwaji da zai nuna cewa giwaye sun fi damuwa da gawa ko bangaren jikin wani danginsu fiye da na wadanda ba 'yan uwansu ba, sun ayyana cewa ta hanyar jin kanshi ko sansana ko kuma tabawa, giwaye za su iya tantance kashin hauren giwar da suka saba da ita tana raye.

Hakkin mallakar hoto Jenny E. RossNPL
Image caption Mazan giwaye suna da dogon azzakari wanda suke iya makale matansu

Duka wadannan sun tabbatar da cewa giwaye dabbobi ne na daban, masu basira da kuma matukar sanin yanayi da halin da 'yan uwansu ke ciki da kuma damuwa da juna.

Akwai shedar jerin abubuwa na zahiri game da giwaye da za su iya kara ba ka mamaki har yanzu.

Wannan ya kuwa ya danganci mahaifar giwar ne, wadda daga kusan mita uku daga farko zuwa karshen mahaifar, kusan wannan ita ce mahaifa mafi tsawo ta duk wata dabba mai shayarwa ta kan tudun kasa.

Duk da yadda namijin giwa yake da tsawon azzakari ba ya shiga farjinta domin kofar farjin tana can cikin giwar ne a nisan mita daya da digo uku (1.3m).

Wannan tsarin mahaifa ko farji mai ban mamaki ana samunsa a jikin dabbobin ruwa.

Masana na ganin hakan zai iya kasancewa giwa ta samu wannan halitta ce saboda yadda take da dangantaka tun asali da dabbobin ruwa, domin ta wannan tsarin farjin ruwa ba zai shiga cikin kororon mahaifa ba a lokacin saduwa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The truth about elephants