An gano katon kada na zamanin da a Tunisiya

Hakkin mallakar hoto httpwww.bbc.comearthstory20160114foundanancientcrocodileaslongasabus

An gano wani shirgegen kada da ke rayuwa a ruwa a Tunisia, wanda tsawonsa ya fi na katon kifin nan ''shark'' kuma kokon kansa ya kai girman mutum.

Ga bayanin Melissa Hogenboom

An gano wani sabon nau'in kada da ke rayuwa a ruwa a kasar Tunisia da ke arewacin Afrika.

Kadan ya rayu ne kusan shekara miliyan 130 da ta wuce, a farkon zamanin da ake kira ''Cretaceous'' da Ingilishi. A lokacin jibga-jibagan halittun nan masu kama da kada (dinosaurs) su ne suka mamaye tudu kuma manyan halittu kamar kadoji su kuma su ke a ruwa.

Ana ganin an bai wa wannan halitta sunan da ya dace 'Machimosaurus rex' wanda ke nufin ''sarkin kadangare mai fada''.

Tsawonsa ya kai kafa 30 (mita10) kusan girman babbar motar bas. Kuma tsawon kokon kansa kadai ya kai sama da kafa biyar (mita 1.6).

Hakkin mallakar hoto Federico Fanti
Image caption Masu binciken ba su yi ma wata haka ba suka ga kwarangwal din kadan

Wannan ya sa kadan ya zama dabba irinta mafi girma da aka taba samu, daga cikin irinsu wadanda suka bace a duniya, wadanda kuma suke da kamanni da kada irin na zamanin yau.

Kusan zai iya cinye duk abin da ya gani. Kadoji a yau 'yan ta-fadi-gasassa ne, kuma daya daga cikin jagororin masu binciken da suka gano kadan Federico Fanti na jami'ar Bologna ta Italiya ya ce shi ma wannan kadan da zai zama kamar na yau din wajen neman abinci.

''Ba tantama wannan dabbar abincinta abin a-zo-a-gani ne, halittar hakoranta ta cin abubuwa masu karfi ne,'' in ji Fanti.

Ya ce, ''duk abin da ya kasance kusa da hakoranta to ya zamana bincinta ta ko yaya. Idan muka yi la'akari da wadannan hakora na shi to lalle za ka ga ba dabba ce mai saukin kai ba.''

Fanti da abokan aikinsa sun bayar da bayanin yadda wannan dabba take a mujallar binciken dabbobin zamanin da na miliyoyin shekaru (cretaceous).

Hakkin mallakar hoto Federico Fanti
Image caption Kokon kan kadan ya kai girman mutum

Ayarin masanan yana bincike ne a yankin na kasar ta Tunisia tsawon shekara bakwai. Fanti ya yi mamaki yadda suka samu kokon kawuna na zamanin da, domin an fi samun ragowar 'yan kananan kasusuwa ko hakora.

Mun ga alamar jikin dabbar a cikin kasa kuma mun kirga fiye da daya,'' in ji Fanti.

Ga alama akwai irinta kusan guda hudu, kuma ayarin ma'aikatan Fantin ya dauki kokon kai daya ya yi nazari a kansa.

Duk da cewa kusan ana iya ganin kwarangwal din dabbar a fili amma ba wanda ya taba binciken kasusuwan halittun zamanin da a wannan yanki na kasar ta Tunisia, in ji Fanti.

Wannan sabon abu da aka gano zai iya sauya fahimtarmu ta yadda aka samu sauyi na halittu a zamanin da na daruruwan miliyoyin shekaru (Jurassic zuwa Cretaceous).

Hakkin mallakar hoto Federico Fanti
Image caption Bisa yadda siffar kokon kansa take ana ganin jikin kadan zai iya zama kamar wannan

Ana ganin an samu bacewar halittu da yawa daga doron kasa a wadancan zamani, ''amma wannan abin da aka gano zai sauya wannan tunani,'' kamar yadda Fanti ya ce.

Wannan kuwa domin manyan dabbobi da dama nau'in kada sun bace daga doron kasa a kusan karshen wancan zamanin (jurassic) na farko, amma bisa ga wannan sheda ita wannan dabba ta cigaba da rayuwa ta wata karin shekara miliyan 20.

''Muna ganin ba mu mayar da hankalinmu ba a kan batan dabbobi daga doron duniya gaba daya, sai dai kawai batan wasu dabbobin daban-daban, ''in ji Fanti.

Ya ce, ''abin ya dogara ne kawai ga bangaren da kake haka kawai a duniya, za ka samu wasu dabbobin sun rayu wasu kuma ba su rayu ba.''

Hakkin mallakar hoto Federico Fanti
Image caption Ana samun guntayen kasusuwan halittun zamanin da a Tunisia a ko ina

Kwamitin kula da harkokin bincike na kasa na Amurka (National Geographic Society Committee for Research and Exploration) shi ne yake daukar nauyin aikin binciken.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Found: an ancient crocodile as long as a bus