Munanan dabbobi 8 da ke bukatar ceto

Hakkin mallakar hoto dbimages alamy

Ba kyawawan zakuna da birai ba ne kadai suke fuskantar barazanar karewa daga doron kasa ba. Su ma wadannan dabbobin da ba su da farin jini suna bukatar taimakonmu, kuma kungiyar masu fafutukar kare munanan dabbobi na kokarin jawo hankali a kansu.

Michael Marshall ya yi mana nazari

Hakkin mallakar hoto no credit

Wannan 'yar karamar dabbar (aye-aye) mai muni a kasar Madagascar kawai ake samunta. Tana neman tsutsa ne da take ci a jikin bishiya.

Tana baro jikin bishiya ne, ta sa dan yatsanta na tsakiya mai tsawo ta kwakwalo tsutsotsi daga ciki ta ci.

Dabbar na fuskantar hadarin karewa a duniya saboda yadda ake sare dazukan da take rayuwa.

Hakkin mallakar hoto Wildscreen

Wannan wani nau'in alade ne da ainahi ake samunsa a Philippines. Yana da wasu abubuwa kamar kuraje ko kari-kari a fuskarsa, wadanda ba a san amfaninsu kawo yanzu.

Aladen na fuskantar barazanar bacewa sosai, domin yawansa ya ragu da kashi 80 cikin dari a tsakanin wa'adin rayuwa uku, (uba da da da jika).

Hakkin mallakar hoto National Geographic Image Collection Alamy

Kada ka bari kamanni ko munin wannan dabba ya yaudare ka, domin nau'i ce na jaba wadda kusan daban take a cikin dabbobi.

Daya ce daga cikin dabbobi biyu masu shayarwa da ke rayuwa zamantakewar tare, inda sarauniya ce a cikinsu kadai take haihuwa, sauran kuma ba sa jima'i, balle su haihu sa dai hidimar aiki kawai suke yi, kamar kudan zuma.

Ma'aikatan suna gina ramuka ne a karkashin kasa masu yawa da hanyoyi masu haduwa da juna, domin neman saiwowi domin ciyar da sauran dabbobin gaba daya.

To ba wannan ba kadai ita wanna jaba ba ta kamuwa da cutar daji, wannan ne ma ya sa masu bincike kan cutar ta daji suke kokarin gano dalili.

Hakkin mallakar hoto imageBROKER Alamy

Wannan kifin mai goshin karo (humphead wrasse) yana neman abincinsa ne a tsakanin duwatsu a cikin tekun Indiya-Pacific. Kifi ne da ke da girma, wanda ke cin sauran kifaye, kuma maza sukan kai tsawon mita biyu.

Yana cin hatta dabbobin ruwa masu guba da masu kaya, amma kuma duk da haka yana cikin hadarin karewa a duniya sabo yawan kama shi da masunta ke yi.

Hakkin mallakar hoto Nature Picture Library Alamy

Wannan wani nau'in kwado ne babba (kwozo) wanda a tafkin Titicaca da ke yankin Latin Amurka kadai ake samunsa.

Yana da tattararriyar fata mai yawa, wadda ke kara masa girma da hakan ke ba shi damar shakar iska da yawa.

Yana fuskantar barazanar karewa daga duniya saboda mutane na cinsa sosai, sannan yana rasa muhallinsa, yayin da kuma dan abin da ya rage na muhallin nasa ma wasu dabbobin na kamawa.

Hakkin mallakar hoto dbimages alamy

Wannan biri mai katon hanci ba a san dalilin da ya sa hancin nasa yake da girma haka ba, sannan na maza ya fi mata girma, abinda kuma ake ganin wani abu ne da ke jan hankalin matan wajen sha'awar namiji, kamar dai gashin dawisu, wurin amfani amma ba kyau ba.

Haka kuma kusan shi kadai ne nau'in birin da ke tukar ganye da 'ya'yan itacen da yake ci.

Yana cikin hadarin gushewar ne daga doron kasa saboda muhallinsa da ake bannatarwa.

Hakkin mallakar hoto Tom McHugh Science Photo Library

Shi wannan kifi na daga cikin dabbobin zamanin da masu kayar baya. Ba kamar sauran kifaye ba, shi wannan ba shi da hakora.

Yana rayuwa ne ta cin gawarwakin dabbobin ruwa da ke nitsewa karkashin teku, inda yake rarake cikin gawar da ya samu ya rika ci daga ciki.

Wannan kifin na tekun Pacific ya kware da haka, saboda shi kadai ne kifi mai kayar baya da yake iya cin abinci kai tsaye ta cikin fatarsa.

Kamar duk sauran nau'ukan kifaye (hagfish) irinsa, yana iya fitar da tarin guba da ke sa sauran dabbobi da ya ke ci su kware, ya kuma kori masu cinsa da wannan guba.

Hakkin mallakar hoto Sandesh Kadur NPL

Jan kwadon Indiya yana rayuwa ne tsawon kusan shekara daya cur a karkashin kasa, inda yake fitowa ta dan lokacin da bai wuce mako biyu ba, da damuna, domin ya yi barbara a ruwan da ya kwanta nan da can.

Saboda yanayin rayuwarsa ta warewa shi kadai, sai a shekara ta 2003 ne aka gano irin shi wannan kwado.

Ana sa wannan kwado cikin rukunin dabbobin da ke fuskantar barazanar bacewa a duniya saboda, a dan wuri karami yake rayuwa, kuma wannan daji da yake rayuwa ana ta sare shi domin yin gonaki.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Eight ugly animals we should save anyway