Ko ka san asalin kudin cizo?

Hakkin mallakar hoto science photo library

Wani sabon nazari da aka yi a kan kudin cizo a tsakanin kasashen Turai ya nuna cewa asali mutum ya same shi ne daga jemage.

Melissa Hogenboom ta bincika yadda lamarin yake.

Akwai salon maganar da ake yi a wasu wuraren da ke cewa, ''ka kintsa wurin barcinka kada ka bari kudin cizo ya cije ka,'' To sai dai abin takaicin kididdiga ta nuna cewa wannan dan kwaro yana galaba a kanka, domin kusan yana nan a ko ina.

Abu ne mai wuya a kasashen duniya ka ji an ce ga satin da ya wuce ba tare da labarin mugun kwaron ya gallibi wani wuri ba.

Amma kuma duk da haka ba a nazari a kansa sosai, in ji Warren Booth na jami'ar Tulsa da ke Oklahoma a Amurka.

Booth dfa abokan aikinsa sun yi nazarin asalin kwayoyin halitta domin gano asalin inda kudin cizo ya samo asali.

A binciken sun gano cewa kwaron yana da asali biyu a Turai. Kuma ya kasu da yawa, kusan iri biyu.

Babban abin dai shi ne kwaron ya samo asali ne daga jemage.

Binciken wanda aka wallafa a mujallar 'molecular Ecology' ta bayar da sheda ta farko ta kwayoyn halitta da ke nuna cewa jemagu ne asalin wadanda suke dauke da kudin cizon da a yau ya addabi gidajen mutane.

Kudin cizo ya dade a duniya, kamar yadda alakarsa da mutum ta dade.

Akwai bayanan da ke nuni da su a tsoffin littattafan tarihi na Masar na da, kuma hatta masu tono abubuwan tarihi na da a karkashin kasa, sun gano abin da yake kamar birbishinsa na zamanin da, da ake ganin ya kai shekara 3,500.

Tamatar kudin cizo mai cikin guda daya za ta iya yada zuriya a babban gida gaba daya ba tare da wata matsala ba.

Abin da suke bukata su hayayyafa kawai shi ne mutum, wanda zai biya musu bukatarsu ta jininsa da suke rayuwa da shi.

To amma a shekarun 1950, kusan wannan kwaro ya bata bat daga gidajenmu da kuma otal-otal da sauran wuraren jama'a, saboda gagarumin yaki da aka yi da shi da maganin kashe kwari.

Sai dai kuma shekara 15 bayan wannan galaba da aka yi a kansa, sai ya sake damara ya dawo domin ramuwa.

Ya kasance akwai wuya a ce an iya kawar da shi, domin ya kai kashi 90 cikin dari na nau'in kwaron a yanzu ba ya na bijire wa magungunan kashe kwari.

Hakkin mallakar hoto NPLAlamy
Image caption Ana kyautata zaton a zamanin da mutane da jemagu sun zauna tare a kogo

Booth da abokan aikinsa sun samo daruruwan nau'in kudin cizo daga wuraren zaman jama'a da jemagu daga kasashe 13 a kasashen Turai.

Nazarin da aka yi na kwayoyin halittarsu (DNA) ya nuna babu musaya ko kamanceceniya ta kwayoyin halitta tsakanin nau'in kudin cizon da ke wirin dan adam da kuma wanda yake muhallin jemage.

Wannan kuwa ya kasance haka duk da cewa jemagu kan zauna a wuraren tattaruwar jama'a kamar, wuraren ibada da saman dakuna, inda ta haka kuidin zai iya samun mutum.

Ana ganin watakila alakar kudin cizon wurin jemage da wanda ke muhallin mutum ta kasance ne tun a zamanin da mutum da jemage suke rayuwa a kogo in ji Booth.

Hatta a yau din nan nau'in wanda jemage yake da shi yana da nau'i daban-daban fiye da irin wanda mutum ke fama da shi.

Biyun suna da bambanci domin ko a baya da aka hada su aure a dakin kimiyya, 'ya'yan da suka kyankyashe ba sa iya haihuwa kamar iyayen.

Hakkin mallakar hoto Natural History MuseumAlamy
Image caption Ka da ka sake ya cije ka

Duk da cewa ba a san cizonsu da yada wata cuta ba, amma ya kan sa jikin mutum ya yi burda-burda da kaikayi, ba ya ga kyamar da ake yi wa mutumin da aka ga kudin a jikinsa, ko kuma wanda ya fito daga inda aka san akwai kudin.

Booth ya ce,''a yayin da kake barci da daddare shi kuwa kudin cizo sai ya samu jininka ya yi ta dabdala, wanda hakan ka iya haddasa wa mutum damuwa mai yawa.

Masanin ya ce akwai mutane iri biyu, ''wadanda suka yi fama da kudin cizo da kuma mutanen da za su yi fama da su. Muna rayuwa ne a lokacin da kudin cizo yake bazuwa a ko'ina.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Origin of bed bugs revealed