Mun san birnin da cutar AIDS ta fara bayyana

Lokacin da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki, HIV da AIDS ko SIDA suka bayyana, sai aka ga kamar daga sama kawai suke, amma kwayoyin halitta sun gaya mana wuri da kuma lokacin da kwayar cutar ta farashiga cikin mutane.

Colin Barras ya yi nazari

Abu ne mai sauki a ga dalilin da ya sa AIDS ta zama kamar wata cuta da ba a san kanta ba da kuma tayar da hankali lokacin da likitocin Amurka suka fara ganinta shekara 35 da ta wuce.

Cutar ta raba matasa da mutane masu lafiya da kakkarfar garkuwar jikinsu, ta sa suka zama masu rauni. Kuma ta zama kamar ba a san daga inda ta fito ba.

A yau mun kara samun ilimi a kan abin da ya sa da kuma yadda kwayar cutar da ke zama AIDS ko SIDA ta zama annoba a duniya. Ba wani mamaki karuwai sun taka rawa a nan.

Haka kasuwanci da faduwar mulkin mallaka da kuma sauye-sauyen siyasa da zamantakewa da aka samu a karni na 20 dukkaninsu sun taka rawa a bazuwar kwayar cutar.

Hakkin mallakar hoto Science Picture CoSPL
Image caption Kwayar cutar HIV (SIV) da ke shafar birai

A gaskiya kwayar cutar ba wai ba a san daga inda ta bayyana ba. Ana ganin kila ta fara bayyana ne da farko a matsayin kwayar cutar da ke shafar birai a tsakiyar yammacin Afrika.

Daga nan ta ratsa sauran dabbobi har ta kawo kan mutane, kila saboda mutane suna cin naman dabbobin dawa da suka harbu da kwayar cutar.

Wasu mutanen sun kamu da nau'in kwayar cutar da ke da dangantaka sosai da wata wadda aka gani a jikin wasu nau'ukan birai (sooty mangabey).

Amma dai ita kwayar cutar da ta samo asali daga birai ba ta zama matsala a duniya ba.

Mun fi kusanci da manyan birai kamar gwaggon biri a kan kananan birai. To amma ko da kwayar cutar ta watsu daga gwaggon biri da sauran manyan birai zuwa mutum, ba lalle ba ne ta zama annoba a duniya.

Kwayar cutar da ta samo asali daga manyan birai tana rukunin wadda ake kira HIV-1 ne. Wata ana kiranta HIV-1 ta rukunin O, kuma yawancin mutanen da suka kamu da ita a yankin yammacin Afrika ne.

A zahirin gaskiya ma nau'i daya ne na kwayar cutar kadai ya bazu da nisa bayan da ya kama mutum.

Ana ganin wannan nau'in wanda ake zaton ya samo asali daga gwaggon biri, ana kiransa HIV1- group M. Sama da kashi 90 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar suna cikin wannan rukuni ne na M, wanda hakan ya taso da tambayar cewa mene ne na musamman a a game nau'in kwayar ta HIV-group M?

Wani nazari da aka yi a shekara ta 2014 ya samar da wata amsa mai alamun ban mamaki, da ke nuna ga alama ba wani abu na musamman a game da nau'in na rukunin nan M.

Hakkin mallakar hoto Sriram SubramaniamNational Cancer InstituteSPL
Image caption Wani nau'in kwayar cutar da ke sa AIDS ko SIDA

Ba wani yaduwa ta ke yi ba a tsakanin mutane kamar yadda za ka yi tsammani, maimakon haka kamar sabani kawai ake samu tana yaduwa a lokacin da wasu abubuwa ke faruwa, wanda za a dauka ita take sa hakan.

Nuno Faria na jami'ar Oxford ta Biritaniya ya ce, ''abubuwa da suka shafi muhalli ne su ke saurin yada ta maimakon na halittar jiki.''

Malamin da abokan aikinsa sun zana wata nasaba (bishiya) ta iyali ta kwayar ta HIV, ta hanyar duba kwayoyin halittar nau'i daban-daban, wadanda aka debo daga jikin mutanen da suka kamu 800 a tsakiyar Afrika.

Mutumin farko da ya harbu da wannan nau'in kwayar cutar (HIV-1 group M) ana ganin kila ya kamu da ita ne a shekarun 1920.

Kwayoyin halitta sukan sauya yanayi da sauri, saboda haka idan aka hada guda biyu, aka yi bincike za a iya sanin lokacin da suke da asali daya.

Da wannan tsarin binciken ne aka yi amfani har aka gano cewa mutane da birai sun hada asali ne daga shekara miliyan bakwai da ta wuce.

''Kwayoyin cutar bairus (RNA virus) kamar HIV sun sauya yanayi da sauri kusan sau miliyan daya fiye da kwayoyin halittar mutum (DNA),'' in ji Faria.

Ya kara da cewa, ''wannan na nufin agogon kwayoyin da suka hadu suka yi kwayoyin cutar ta HIV yana gudu sosai.''

Yana gudu sosai, ta yadda Faria da abokan aikinsa sun gano cewa kwayoyin halittar kwayar cutar ta HIV dukkaninsu suna da asali daya shekara sama da dari daya da ta gabata.

Annobar kwayar cutar HIV-1 group M ta fara ne a shekarun 1920.

Daga nan kuma sai masanan suka ci gaba da binciken. Saboda sun san inda aka dauko dukkanin nau'ukan kwayar cutar, za su iya sanin sanya kawayar cutar a wani birni, birnin kuwa shi ne Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo.

Hakkin mallakar hoto Zute LightfootAlamy Stock Photo
Image caption Ana ganin birnin Kinshasa ne asalin kwayar cutar AIDS ko CIDA (HIV)

A shekarun 1920 Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo tana karkashin mulkin mallakar kasar Belgium ne.

Kuma a lokacin ba a dade da sanya birnin Kinshasha wanda a lokacin ake kiransa Leopoldville, babban birnin kasar ba.

Birnin ya zama matattara kuma barikin 'yan kwadago maza, masu neman aiki da kuma karuwai.

Nan da nan kwayar cutar ta yadu cikin sauri tsakanin mutanen birnin. Kwayar cutar ba ta tsaya a birnin ba.

Masu binciken sun gano cewa a Afrika, babban birnin na Congo a shekarun 1920 na daya daga cikin birane da ke da hanyoyi na jirgin kasa da na mota na zuwa wasu biranen.

Sakamakon hanyoyin jirgin kasa da ake da su a birnin inda dubun dubatar mutane suke tafiye-tafiye a kowace shekara, an samu bazuwar cutar zuwa biranen da ke da nisan mil 900 daga birnin a cikin shekaru 20 kawai.

Kusan komai ya kammala na bazuwar cutar ta zama annoba a shekarun 1960.

Hakkin mallakar hoto Sebastian KaulitzkiSPL
Image caption Wata kwayar halittar jiki da kwayar cutar AIDS ta kama

Congon ta samu 'yancin kai, sanna kuma ta zama wata kamar aljannar ma'aikata ga masu magana da harshen Faransanci daga sauran sassan duniya, da suka hada da kasar Haiti.

A lokacin da matasan 'yan kasar ta Haiti suka koma gida bayan 'yan shekaru, sai suka kai wani nau'in kwayar cutar na HIV-1 group M, da ake kira nau'inta na biyu (subtype B) zuwa bangaren yamma na tekun Atalantika.

Sai kuma ta isa Amurka a shekarun 1970, a lokacin an samu karuwar zinace-zinace da 'yancin al'adar luwadi a manyan birane irin su New York da San Francisco.

Daga nan ma kuma sai kwayar cutar ta HIV ta kara samun dama ta watsu da sauri a tsakanin Amurka da Turai.

''Babu dalilin da zai sa a ce sauran nau'ukan cutar kanana su ma ba su bazu ba kamar ta farkon (subtype B) idan aka yi la'akari da irin yanayi daya da ita ma ta samu ta bazu,'' in ji Faria.

Labarin bazuwar kwayar cutar AIDS ko CIDA bai kare ba tukuna.

Hakkin mallakar hoto Ami ImagesDartmouth College Louisa HowardSPL
Image caption Kwayar cutar AIDS na kama kwayar halittar jiki

Misali a shekarar 2015, an samu barkewar cutar a jihar Indiana ta Amurka a tsakanin masu allurar miyagun kwayoyi.

Hukumar yaki da bazuwar cutuka masu yaduwa tsakanin mutane ta Amurka tana nazari kan jerin sauyin kwayoyin halittar kwayar cutar ta HIV da tattara bayanai a kan wuri da lokacin da ta yadu, in ji Yonatan Grad na makarantar nazarin harkokin lafiyar jama'a ta Havard a Massachusetts.

Ya ce, ''wadannan bayanan za su taimaka wajen sanin girman annobar, kuma za su taimaka wajen sanin lokaci da matakan da aka dauka na yaki da annobar suka yi aiki.''

Wanna matakin zai iya yin aiki a kan wasu kwayoyin cutar. A shekara ta 2014 Grad da abokin aikinsa Marc Lipstch sun wallafa sakamakon wani bincike na yaduwar wata kwayar cutar sanyi ta jima'i (gonorrhoea), wadda ba ta jin magani a fadin Amurka.

''Saboda muna da nau'in kwayoyin daban-daban daga daidaikun mutane a birane daban-daban kuma a lokaci daban-daban daga masu nau'in jima'i iri-iri, za mu iya nuna cewa an samu bazuwar ne daga yammaci zuwa gabasin kasar,'' in ji Lipstich.

Bayan wannan ma sun kuma iya tabbatar da cewa kwayar cutar sanyin da ke bijire wa magani ga alama ta yadu ne tsakanin yawanci tsakanin maza masu luwadi.

Wannan zai iya sa kara daukar matakan gaggawa na tantance masu cutar a cikin mutanen da ke da hadarin kamuwa da ita, domin rage yaduwarta.

Ma'ana akwai amfani sosai da tasiri a nazarin kwayoyin cuta kamar na HIV (AIDS ko CIDA)da na cutar sanyi a jikin mutane.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. We know the city where HIV first emerged