Hadari mai kama da dunkulen wuta ya bayyana

Hakkin mallakar hoto Rogerio Pacheco

A kwanan nan ne aka ga wannan hadarin da ya yi kama da dunkulen wuta a sararin samaniyar tsibirin Madeira na kasar Portugal, me ya sa ya yi kama da dunkulen wuta?

Melissa Hogenboom ta bincika.

Gajimaran wanda ya yi kama da dunkulen wuta yana ta kai kawo ne a samaniyar tsibirin a cikin kwanakin nan, har mai daukar hoto kuma mai yada bayanai na yanayi ta intanet, Rogerio Pacheco ya yi dace ya dauki hotonsa, inda ya sanya shi a shafin nasa.

Mun tattauna da masaniyar yanayi ta BBC Aisling Creevey, domin sanin yadda aka yi wannan hadari wanda ba a saba ganin irinsa ba ya bayyana a samaniya.

Hakkin mallakar hoto Caters News Agency

Ta ce, abu ne da za I ba ka mamaki cewa irin wannan hadari ba wani sabon abu ba ne, amma ba kasafai muke iya samun damar ganinsa ba kamar yadda ya bayyana a yanzu.

Dalilin da ya sa aka gan shi kamar haka, saboda hasken da ya fito daga rana ne ya gamu da wani hadari ne da ke kasa-kasa a daidai lokacin da hasken ya kuma hadu da wani hadarin a sama da na kasan.

Masaniyar ta ce akwai shinfida hawa uku ta hadari, kuma wannan alamun dunkulen wuta kamar yana haduwa da wasu daga cikin shimfidun. Misali baki-bakin da ke cikin hadarin ga alama hadari ne da ke tsakiya, wanda yake tsakanin mita 2,400 zuwa 6,100 daga kasa.

Kila irin wannan hadarin zai iya kasancewa a samanmu kusan a ko da yaushe, to amma galibi ba ma iya bambancewa sosai tsakanin launukan hadari.

Creevy ta ce, ''wannan hadarin ba shi da wani bambanci da hadarin da muka saba gani, kawai dai an dace da daukar hotonsa ne a dai dai lokacin da ya yi kicibis da hasken rana.

Hakkin mallakar hoto Rogerio Pacheco

Wata masaniyar yanayin, Emma Sharples, daga hukumar kula da yanayi ta Biritaniya ita ma ta yarda da wannan bayanin, tana mai cewa, ''ina ganin kasancewar hasken rana ne ya sa aka gan shi haka, kamar hadarin wuta, ba kamar yadda shi kadai hadarin zai iya kasancewa ba idan da ba hasken ranar.

Muna tunanin ya zama wannan gagarumin hadari ne wanda an saba ganinsa amma yanayin haske ya sa ya zama daban.''

Creevy ta ce, ''Pacheco ya yi sa'ar ganin hadarin a wannan yanayi, domin ba zai kasance a wannan launi ba na dadadden lokaci, wanda bai wuce 'yan mintina ba.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The cloud that resembles a fireball in the sky