Ka san kare na da kauna amma ba shi da kara?

Hakkin mallakar hoto jane burton npl

Ka gode domin kai ba kare ba ne, saboda shi kare yana da kirki da biyayya da kuma kaunar mutum, sai dai ba ya nuna kara da tausayi ga dan uwansa kare sai fa idan ya san shi daman.

Kamar yadda Kara Segedin ta gano a binciken da ta yi

Ba tantama Zai iya kasancewa babban abokin mutum a cikin dabbobi mai biyayya da mutunta abokansa, amma kuma duk da wannan kare ba ya nuna kara da tausayi ga baki 'yan uwansa karnuka.

Sakamakon wani bincike da aka wallafa a mujallar kimiyya ta 'Scientific Reports', ya nuna cewa karnuka suna iya taimaka wa wani karen da abinci, idan har sun san shi.

Hakkin mallakar hoto Petra WegnerNPL
Image caption Karnuka na taimakon 'yan uwansu na gida daya

Taimakon juna ko taimakekeniya ta kunshi duk wani abu na taimakon kamar bayarwa da ciyayya (ci tare) da kuma hadin kai.

Tuni aka ga wannan dabi'a a tsakanin birai kuma an yi nazarinta a kimiyyance a cikin beraye da wasu tsuntsaye.

Domin gudanar da nazari a kan wannan dabi'a masu bincike sun horar da wasu karnuka kan yada za su ja wani zare, sai wani tire ko faifai ya fito daga wani wuri.

An hada karnukan da wani karen da suka sani (wanda ba a ba shi wannan horo ba), ko kuma da wani karen bako wanda ba shi da fada (kuma jinsinsu; namiji ko mace).

Karnukan da aka ba horon za su iya zabar ko su ba wa bakon nasu faifai mai dauki da abinci ko kuma wanda babu komai a cikinsa (idan sun ja abin da ke fito da faifan).

Abin da karnukan suka yi shi ne, idan aka hada su da bakon karen da suka sani, sai su ba shi abinci (fito da faifan), kusan sau biyu a kan yadda suke ba wa bakon karen da ba su sani ba..

''Ba mu yi mamaki ba da yadda suka ba wa bakin karnukan da suka sani, abin da ya ba mu mamaki kawai shi ne yadda har suka ba wa bakin da ba su sani ba (abinci) dan kadan,'' in ji daya daga cikin wadanda suka rubuta rahoton, Rachel Dale ta jami'ar likitancin dabbobi ta Vienna, da ke Austria ( University of Veterinary Medicine ).

Duk da cewa an gudanar da nazari ko gwajin wannan dabi'a ta taimakon juna (taimakekeniya) tsakanin kare da mutum a baya, Dale ta ce sakamakon da aka rika samu ba shi da tabbas, domin ba za a iya tantancewa ko karnukan suna taimakon ba ne saboda wannan dabi'a ko kuma suna taimakon mutum ne saboda biyayya ta kare da mai shi.

Dale ta ce, ''abu ne mai wuya saboda sun saba da horo da kuma koyon abu daga mutane, dole sai mun yi a hankali, domin kada mu yi wa lamarin bahaguwar fahimta.''

Hakkin mallakar hoto ARCONPL
Image caption Karnuka sun samo asalin dabi'arsu ta taimakon juna ne tun daga asalinsu na dawa (Kerkeci)?

Kafin ka yi mamaki kan yadda kare ya bakon karen da bai sani ba,( sabain abin da ka sani a baya), to ka sani akwai dalilin da ya sa ya yi hakan.

Dale ta ce, ''idan ana magana ne ta gungun karnuka sai a ce hakan na da wata manufa.''

Domin samun hadin kan sauran karnuka, kana bukatar juriya ta cin abincin da kake da shi tare da sauran karnukan da kuke tare, misali, idan gungun karnuka ya kaso wani babbar dabba to akwai bukatar rarraba naman tsakaninsu.

A yanzu haka Dale, tana gudanar da irin wannan nazari a kan wasu kerkeci (karen dawa), domin tana so ta ga ko, kare yana da wannan dabi'a tasa ta taimakon juna ne saboda ya zama dabbar gida yanzu ko kuma dabi'a ce daman ta jinsinsa tun asali, tun yana daji kafin mutum ya kawo shi gida.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Dogs may love us, but they are mean to strangers