Me zai faru da kai idan maganadisun kasa ya daina aiki?

Hakkin mallakar hoto Room Alamy

Idan a ce an wayi gari rana daya aka ga maganadisun kasa ya daina aiki, shawagi da mutane za su rika yi kamar takarda a sama kadan ne daga cikin matsalolinka.

Colin Barras ta yi mana bincike

Dukkanninmu mun san amfanin maganadisun kasa. Shi ne abin da ke faruwa da kai idan ka yi tsalle sama. Ko kuma kamar yadda ake cewa komai nisan jifa kasa zai dawo.

To me zai faru idan muka tsayar da wannan maganadisu?

Kimiyya ba ta ma damu ba, ko ma a ce ba ruwanta da wannan magana, domin a wurinta abu ne ma da bai zai taba faruwa ba. Amma kuma hakan ba shi zai hana mutane tunanin faruwar hakan ba.

Bisa tunani da fahimtar masana da dama, mun tattara irin abubuwan da muke ganin za su iya faruwa a kanka idan kwatsam maganadisun kasar ya bace.

Hakkin mallakar hoto Agencja Fotograficzna CaroAlamy
Image caption Duk abin da ya je sama kasa zai dawo

Jay Buckey masanin kimiyya kuma tsohon dan sama jannatin hukumar kula da sararin samaniyar Amurka, NASA, ya duba yadda rashin maganadisun zai iya shafar jikin mutum.

Buckey ya ce, jikinmu ya riga ya saba da doron duniyar da yake da maganadisun, saboda haka idan muka je wurin da babu maganadisun, kamar tashar sama jannati, jikinmu zai sauya.

A yanzu dai abu ne da aka sani cewa 'yan sama jannati ba su da nauyin kashi da kuma karfin tsokar jiki a duk lokacin da suka je sararin samaniya, inda babu maganadisun, kuma yanayin yadda kwakwalwarsu ke sarrafa jikinsu kan yadda mutum ke rayuwa a doron kasa ba tare da ya fadi ba duk suna rasa shi idan sun je can samaniya.

Rashin maganadisun na kuma kawo wasu matsalolin kamar yadda Kevin Fong ya bayyana. Ya ce, bisa wasu dalilai da ba a sani ba kawo yanzu, yawan jininmu a sararin samaniya (inda ba maganadisun kasa) yana raguwa, inda mutum ka samu abin da za a iya cewa ''cutar karancin jini ta samaniya''.

Rauni yakan dauki lokaci mai yawa kafin ya warke sannan kuma karfin garkuwar jikinmu yana raguwa. Hatta barcinmu ya kan gamu da matsala idan ba maganadisun kasar mai karfi ko kuma ma babu shi gaba daya.

Wannan shi ne abin da ke faruwa ga mutum idan ya kai ziyara ko ya je samaniya na dan wani lokaci. ''To idan kuma a ce mutum ya girma inda babu maganadisun ne gaba daya kuma fa?'' Buckey ya yi tambaya.

''Ina kuma maganar abin da ya dogara ga maganadisun, kamar tsokar jikinka, ko kuma abin da ke sa ka iya tsayuwa ko ka yi tafiya ba tare da ka fadi ko tangadi ba, ko ma zuciyarka ko jijiyoyin jininka?''

Akwai dalilin da ke tabbatar da cewa lallai kam idan ba maganadisun kasa to da jikin mutum zai zama daban.

Hakkin mallakar hoto NASAScience Photo Library
Image caption Rayuwa inda ba maganadisun kasa na shafar yanayin jikinka

Buckey ya yi nuni da wani gwaji da aka yi, inda wata mage ta girma da ido daya a rufe a ko da yaushe. Sai ya kasance daya idon nata ba ya gani sam-sam saboda rufe shin da aka yi, domin abin da zai hada kwakwalwar da idon su rika aiki tare bai yi aiki ba saboda idon ba ya ganin komai ballantana a samu bukatar yin wannan aiki.

Wannan misali ne na maganar da akan yi cewa, ''yi amfani da abu ko kuma ka rasa shi''.

Ga alama dukkanin jikinmmu mu ma haka zai iya yi. Idan babu wannan maganadisu na kasa da zuciyarma da tsoka da jijiyoyin jikinmu za su amfana da shi, to ba shakka kayayyakin jikinmu za su zama daban ne.

Masaniyar ilimin sama jannati, Karen Masters ta jami'ar Portsmouth da ke Biritaniya ta bayyana irin illar da za a iya samu idan babu maganadisun, a littafinta mai suna , ''Ask an Astronomer''.

Matsala ta farko ita ce, duniya dai tana gewayawa ne da gudu, kamar yadda za ka daura wani abu a jikin zare, ka daura zaren a kanka ka yi ta kada abin yana kewaya kanka.

Ta ce, ''Tsayar da maganadisun kasa daidai yake da cire zaren nan daga kanka, ya tafi da abin da ka kulle din nan,'' in ji Masters. Ta ce, ''Abubuwan da ba a jikin kasa suke ba za su yi ta tashi ne zuwa sama a mikakken layi ta yadda za su bar sararin duniyar nan.''

Hakkin mallakar hoto AdriankoAlamy Stock Photo
Image caption Kasancewa a cikin gida mataki ne na kariya daga tashi sama idan maganadisun ta tsaya da aiki a duniya

Duk wanda ya kasance yana waje a lokacin da hakan ta kasance to nan da nan zai bace, zai yi sama ya bar doron kasa. Mutanen da ke cikin gida za su tsira domin gidaje a kafe suke a kasa, ta yadda za su iya kasancewa a daram ko da ba maganadisun, akalla zuwa wani lokaci, kamar yadda Masters ta rubuta.

Duk wani abu da ba a kafe yake ba, to zai tashi sama ne. Yankin da iskar duniya yake da tekuna da rafuka da koguna duka ruwansu zai yi sama ne.

''Ai ba shakka dukkanninmu ma za mu mutune kawai,'' Jolene Creighton ta rubuta.

Illar rashin maganadisu a karshe za ta bayyana a duniyarmu, in ji Masyters, ta kara da cewa, ''Ita kanta duniya mai yuwuwa ta tarwatse buraguzan su yi sama.''

Haka ita ma rana abin da zai iya samunta ke nan. Idan ba maganadisun kasa da zai sa ta cigaba da zama a dunkule, tsananin nauyin da ke tsakiyarta zai sa ta tarwatse.

Dukkanin sauran taurari ma haka za su tarwatse. Sai dai tun da suna nesa da mu ne sosai, za a dauki lokaci kafin baraguzansu su zo inda mu ke.

A karshe dai zai kasance babu alamar wani abu, kamar taurari ko duniyoyi a ko ina. Sai kawai kwayoyin da ke haduwa a samu halittar wani abu ne ko kamannin abubuwan da muke gani a duniya za a ga suna ta yawo ba sa komai.

Hakkin mallakar hoto Oliver BurstonAlamy Stock Photo

Wannan abu wanda kamar yadda muka bayyana a baya cewa ba zai taba faruwa ba, ya nuna muhimmancin da maganadisun kasa yake da shi a yadda duniya ke aiki.

Idan ba tare da shi ba babu wani abu mai muhimmanci kamar duniyoyi ko shafin intanet na BBC da za su kasance.

Maganadisun kasa na daya daga cikin muhimman abubuwa guda hudu da ke tafiyar da yadda duniyar nan da sauran duniyoyi da rana da wata da taurari da abubuwan da ke ciki da tsakaninsu ke wanzuwa.

Sauran ukun ma suna da muhimmanci kamar shi maganadisun na kasa, domin idan ba maganadisun lantarki (electromagnetism) da na nukiliya mai karfi da maras karfi 'yan mitsimitsin abubuwan da ke haduwa su tabbatar da wanzuwar duk abubuwan da muke gani a duniyar nan da waje da ita za su wargaje.

Sai dai maganadisun kasa shi ne guda daya daga cikinsu da aka fi sani, wanda kila wannan shi ne ya sa muka fi damuwa da sanin abin da zai iya faruwa idan babu shi maganadisun na kasa, da kuma abin da ya sa gano tururin maganadisun yake ba mu sha'awa duk da cewa ba ta taba shafara rayuwarmu ba kai tsaye.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What would happen to you if gravity stopped working?