Ka san kwayoyin cuta masu amfani?

Hakkin mallakar hoto NIH spl

Wasu daga cikin kwayoyin cutar da ake dauka a lokacin jima'i za su iya kasancewa masu amfani garemu, ko yawancinmu suna asararsu?

Niki Wilson ta yi mana nazari

Hukumar lafiya ta duniya tana ganin sama da mutane miliyan daya ne ke kamuwa da cutar da ake samu ta hanyar jima'i a duk rana. Saboda haka wasu ke gani bin matakai na kaucewa kamuwa da cutukan shawara ce mai kyau.

Wasu daga cikin wadannan cutuka za su iya hana ka samun haihuwa, wasu ma za su iya haifar da matsalolin da suka fi hakan. Akwai dai dalilai da dama da ya kamata ka kare jikinka daga wadannan kwayoyin cuta.

Saboda irin illar da wadannan kwayoyin cuta suke da, kila shi ya sa ba a damuwa ko la'akari da cewa wasu kwayoyin da suke yaduwa tsakanin mutane a lokacin jima'i suna da amfani.

To ya kuma idan a kokarin kare kanmu daga kwayoyin da muka san suna yada cuta, muka rasa wadanda za su iya taimaka wa jikinmu?

Shedu da dama na nuna cewa akwai matukar bukatar mu lura d wannan, domin cin moriyar kwayoyin da suke da amfani.

Hakkin mallakar hoto Nano Art LtdSPL
Image caption Kwayar cutar yist (yeast) ta farji

Ba sabon labri ba ne yanzu ka ji cewa kwayoyin halittu kamar su bakteriya da bairus (bacteria, virus), suna da matukar amfani ga lafiyarmu.

A cikin kowannenmu akwai hadakar kwayoyin halittu masu cutarwa da kuma masu amfani, saboda idan aka samu sabani kan yawan yadda kowanne ya kamata ya zama, to hkan zi iya haifar da matsala.

Misali akwai kwayar halittar (candida) da ke samuwa a cikin farji, wadda wata kwayar halitta ta bakteriya (lactobacillus) ta ke sanya wa ido ko, kuma take yaki da ita, idan wani abu ya hana wannan bakteriya aikinta, sai a samu yawan waccan kwayar halittar ta farko (yeast) a cikin farji, wadda ita kuma za ta sanya wa mace cuta.

Jikinmu cike yake da kwari

Halittar jikinmu ta kunshi tarin kwayoyin halittu masu rai. Wadannan kwayoyi (bacteria, fungi, virus) suna kan fatarmu, da cikin hanjinmu da kuma wani bangare na farjinmu (mata da maza).

Duk da cewa ba abu ne mai dadi ba ka yi tunanin cewa akwai kwayoyin halittu (bakteriya) suna ta kai komo a cikin 'yan hanjinmu, amma kuma abu ne da ke kara bayyana cewa wadannan kwayoyin halitta suna taka muhimmiyar rawa a jikinmu.

Matakin farko na sanin irin rawar da wadannan kwayoyin halitta ke takawa shi ne a fara gano su, daga nan ne kuma idan aka yi nazari a kansu za a san amfaninsu.

Akwai kwaron da ke shan ruwan jikin tsirrai, wand da hk yke rayuwa, kuma ana dangant nasarar dorewar rayuwarsa ga wasu 'yan kwayoyin hlittu da suke zuba wa junansu yayin da suke jima'i.

Anfanin wadannan 'yan halittu da suke zuba wa junansu ya hada da garkuwa daga wasu kwayoyin masu kisa ko hana mai masauki yada kwayoyin haihuwa, jure wa zafi da kuma damar rayuwa kan wasu tsirran da ba su da irin ruwan da yake sh ya rayu, har zuwa lokcin da zai samu tsirran da suke ci ko shan ruwansu.

Haka kuma wasu nau'ukan sauro suna da wata kwayar halitta ta bakteriya da ke cikinsa da marenansa da kuma saman kwansa lokacin yake zama kwai.

Ana ganin wannan bakteriya da take rufe samn kwan, tana samar da tsutsar da tke sa kwan ya yi saurin zama cikakken kwai a cikin kwana biyu zuwa hudu fiye da wadanda ba su da wannan kwayar bakteriya.

To yaya su kuma mutane abin yake a wurinsu? Yanzu dai mun san cewa akwai wani misali da ke nuna mana amfanin kwayoyin halitta da ake yadawa ta jima'i, wadanda ke iya amfani ga jikinmu.

Akwai kwayar halitta da ake yadawa ta jima'i (GBV-C) wadda a karan kanta ba ta yada wata cuta, ko da yake ana samunta da wasu kwayoyin halittar bairus da ke haddasa cuta kamar HIV.

Wani nazari da aka yi na wasu bincike-bincike guda shida ya gano cewa ita wannan kwayar halitta (GBV-C) tana rage karfin kwayar cutar bairus ta HIV mai haddasa kanjamau, ta yadda ba za ta iya yi wa garkuwar jikinmu illa ba sosai.

Haka kuma tana kara karfafa sauran bangarorin garkuwar jikinmu ta yadda za su iya yakar cutar da kyau.

Sannan za a iya yada wannan kwayar halitta daga uwa zuwa jariri, wanda wannan kyakkyawan labari ne, domin za ta iya rage damar yada kwayar cutar HIV daga uwa zuwa da.

A kwanakin nan ma an gano cewa ita wannan kwayar halitta (GBV-C) tana iya rage illar kwayar cutar Ebola a jikin wadanda Ebolan ta kama, wand hakan zai rage tasirin Ebolan a jikin mutum.

Hakkin mallakar hoto TEMSPL
Image caption Ba a san yawan kwayoyin cuta masu amfani da ake yadawa ba lokacin jima'i

Gano muhimmin abu kamar wannan zai sa mu yi tunanin wadanna abubuwan kuma muke asara a rashin saninmu da amfnin wadannan kwayoyin halitta da ke yaduwa ta jima'i, in ji Betsy Foxman, ta jami'ar Michigan ta Amurka.

Ta ce a baya an dauka cewa duk wata kwayar halitta da ake yadawa ta jima'i ba ta da kyau. Matakan da muke dauka na kare kanmu daga wadannan kwayoyi, ka iya kasancewa illa garemu wajen samun masu amfani daga cikin kwayoyin.

Foxman na ganin akwai bukatar kara bincike domin gano muhimmancin wasu kwayoyin da suke cakuduwa da wasu, domin sanin bin da jikinmu zai iya yi d ita wanda jikin zai kara amfana ta yadda zai samu karin lafiya.

Zai iya kasancewa ma akwai kwayoyin da za su iya taimaka wa wajen yaki da wasu kwayoyin cutar in ji Foxman. Idan har da akwai su to ba shakka za su sa mu rage dogaro da magunguna (antibiotics).

Yawanci suna kashe kwayoyin halittu da dama domin kawar da wadda ke haifar da matsala.

Ba mu da tabbas kan wace kwayar halitta ce da ake yadawa ta jima'i take da amfani, amma Foxman tana ganin Lactobacillus ce, wadda ake samu a madarar yogot (yoghurt), wadda daman tana daya daga cikin wadanda ke samu a jikin dan adam.

Ta kara da cewa zai iya kasancewa akwai karin wasu halittun ma masu amfni wadanda ba a kai g gano su ba.

Hakkin mallakar hoto MedicImageAlamy
Image caption Kororon roba hanya daya ce ta kariya daga kwayoyin cuta

Akwai matsala guda daya. Idan ta jima'i muke samun wadannan kwayoyin halitta masu amfani, to hakan zai sa mu rika samun masu cutarwa su ma.

Watakila a nan gaba za a iya gano hnyoyin da za a iya samunsu na daban ba sai lalle ta jima'i ba. Da zarar masana kimiyya sun gano kwayar halittar jima'i mai amfani to sai masanan su duba hanyar da za a iya samunta a jikin mutum ba tare da hadarin jima'i ba kariya ba.

Akwai abubuwa da ke nuna cewa ko kai kadangare ne ko tsuntsu ko wata dabba ko kuma mutum, to fa ba kai kadai ba ne da abokiyar saduwarka.

Akwai watakila wasu dubban 'yan kananan halittu da ke jiran a samu wannan saduwa kawai sai su rarrabu tsakanin jikinka da jikin abokiyar saduwarka, kuma watakila ma har su yadu tsakanin al'umma.

Kila nan gaba kadan za mu san wasu daga cikinsu Masanin kimiyya Chad Smith, ya ce yadda ake samun krin sha'awa da kuma bincike a kan wadannan kwayoyin halitta, a yanzu akwai sabbin hanyoyi na bincike na gano amfaninsu, wadanda ba mu da su shekara goma da ta wuce.

Amma dai a yanzu idan za a sadu a yi ta yadda ba za a kamu da kwayoyin cuta ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Surprising benefits of sexually transmitted infections