Mene ne amfanin haɓar mutum?

Hakkin mallakar hoto SPL

Akwai bayanai da yawa da suke ƙoƙarin bayyana dalilin da ya sa muke da haɓa, amma babu ɗaya daga ciki da aka tabbatar da ingancinsa. Anya za mu iya gano wannan lamari?

Melissa Hogenboom ta yi bincike

Dukkaninmu muna da haɓa, wadda ga ta nan a ƙasan fuskar kowannenmu ba tare da wani sanannen amfaninta ba. Wasu za ka ga haɓar tasu ta fito sosai wasu kuwa ba sosai ake ganinta ba.

Duk da yadda wannan halitta take a jikinka da ma kowa, idan aka sa ka a gaba aka ce ka bayyana amfaninta, kana jin za ka iya bayar da wata amsa mai gamsarwa? Ga alama ba wanda yake amfani da haɓarsa domin yin wani abu mai amfani takamaimai.

James Pampush na jami'ar Duke a North Carolina ta Amurka, wanda ya jima yana gudanar da bincike tsawon shekaru a kan haɓar ta mutum, ya ce ba wanda ya taɓa gabatar da wani kyakkyawan bayani kan dalilin da ya sa mutane ne kadai a cikin halittu ( dabbobi) suke da haɓa. Saboda haka ne ya duƙufa neman yadda zai warware wannan siddabaru a wani nazari da ya yi a baya bayan nan.

Hakkin mallakar hoto Fiona RogersNaturepl.com
Image caption Hatta biri ba shi da haɓa

Dukkanninmu muna da kyakkyawan sanin mece ce haɓa, amma inda gizo ke saƙar shi ne sanin amfaninta. Ita dai haɓa babu wata dabba ko halitta bayan mutum da take da ita, hatta birai wannan ƙashin da yake zaman haɓa nasu ciki ya yi ba waje ba kamar yadda na mutane yake.

Ko da yake ba wanda zai iya tabbatar maka cewa ga dalilin da ya sa mutum yake da haɓa, akwai bayanai guda uku fitattu da aka daɗe ana bayarwa na dalilinta.

Na farko shi ne an daɗe ana bayyana cewa ana ganin haɓa tana taimaka mana ne wajen tauna abinci, inda wannan nazariyya ke bayyana cewa muna buƙatar ƙarin wani ƙashi da zai ƙara wa muƙamuƙinmu ƙarfi domin jurewa tauna.

To amma wannan dalilin za ka ga ba shi da tushe balle makama, idan ka kwatanta mu da sauran birai masu muƙamuƙi irin namu (waɗanda su kuma ba su da haɓa).

Hakkin mallakar hoto Ian MilesFlashpoint PicturesAlamy
Image caption Ga alama haɓarmu ba ta taimaka mana wajen tauna abinci

Za ka ga cewa idan muna tauna ƙashin muƙamukinmu na rabuwa kuma yawan girman bude baki shi zai sa wadannan kasusuwa na mukamuki su gaji. Saboda haka idan har muna bukatar kare kanmu daga gajiyar tauna, to za mu bukaci karin kashi ne a kusa da jikin kashin mukamuƙinmu can kusa da harshe amma ba a ƙasan muƙamuƙin ba.

Wannan shi ne yadda halittar wasu birai take, suna da wannan ƙarin ƙashi a bakinsu wanda mutane ba su da shi. Saboda haka wannan ƙarin ƙashi wanda ya ake kira haɓa a jikin mutum ba shi da wani amfani wajen ƙara mana ƙarfin tauna.

Wani ƙarin bayani da Pampush yake son yi kuma shi ne, ba ma shan wata wahala wajen tauna ma ai, domin yawancin abincin da muke ci yana da laushi, musamman wanda aka dafa. Ya ce, ''wannan shi ne dalilin da ya sa ba za a ce haɓa ta samu a jikin mutum ba ne domin tauna.''

Flora Groening ta jami'ar Aberdeen a Biritaniya ita ma ta yarda da wannan bayani, inda shekara biyar baya ta gudanar da wani gwaji da kwamfuta a kan yadda mutum ke tauna, ta ga babu wani dalili da zai sa a ce, amfanin haɓa ya shafi tauna abinci.

Hakkin mallakar hoto Jeroen Hendriks Alamy
Image caption Wannan nau'in birin ba shi da haɓa amma yana da faifan fuska da ke jan hankalin mata

Wasu masanan kuma suna ganin haɓa tana taimaka mana ne wajen yin magana, saboda haka harshenmu na son ƙarin ƙarfi da wani ƙashi a kasan muƙamuƙinmu wato haɓa kenan.

To amma kuma shi wannan dalili ko bayani, shi ma an ƙalubalance shi domin, ba ma buƙatar wani ƙarin ƙarfi ko tallafi na wani ƙashi (haɓa) wajen yin magana. Kuma idan ma muna buƙatar wannan ƙashi to zai yi amfani ne a cikin muƙamuƙinmu, a kusa da harshe, amma ba a ƙasan muƙamuƙin ba.

Dalili na uku kuwa shi ne, wasu na cewa wai haɓa ba ta da wani amfani na kai tsaye illa ƙarin kyau ga wani jinsi, inda suka kwatanta ta da wani abu mai kama da faifai a ƙuncin wani nau'in biri (orangtuan faces), wanda wannan abin yana sa wa wannan biri kyau, domin yana jan hankalin mata (birai) da shi.

To a nan ma maganar ba ta samu gindin zama ba, domin ai maza da mata suna da haɓa, ba namiji ba ne kaɗai yake da ita balle a ce zai ja hankalin mace da haɓar.

Pampush ya ƙara da cewa, ''a tsakanin dukkanin dabbobi ko halittu masu shayar da nono (mammals) jinsi ɗaya ne, mace ko kuma namiji, shi ne za ka ga yana da wani abu na jan hankalin dayan, amma kuma sai ga shi ita wannan halitta haɓa, namiji yana da ita mace ma kuma tana da ita.''

Saboda haka dukkanin waɗannan bayanai uku da aka gabatar na dalili ko amfanin haɓa a jikin mutum ba su da makama in ji Pampush.

Ya ma ƙara da cewa, ''a zahirin gaskiya a yanzu ba mutumin da zai iya ce maka ga dalilin da ya sa muke da haɓa, duk wanda ya ce maka ya sani to ƙarya yake yi maka.''

Wasu masana kimiyya Stephen J. Gould da Richard Lewontin a shekarar 1979 sun bayyana cewa, suna ganin haɓa ka iya kasancewa wata alamace ta inda halittar ƙashin kai ta faro, kamar yadda za a iya gani a ƙasan wasu hasumiyoyi kamar na coci, waɗanda za a ga kamar daga nan aka fara ginin hasumiyar.

Nathan Holton na jami'ar Iowa a Amurka, yana ganin yadda ƙashin kanmu ke raguwa idan aka kwatanta da na mutanen da, shi ne ya haifar da haɓa. Yadda kakanninmu suka gano wuta suke amfani da ita wajen dafa abinci, ba sa buƙatar muƙamuƙi mai ƙarfi wajen tauna abinci, wannan ya sa ƙarfin muƙamuƙin ya ragu gaba ɗaya saboda haka ya ragu, sai aka samu haɓa, a ganin masu wannan fahimta.

Saboda haka idan har ba ko ɗaya daga cikin bayanan da aka gabatar na dalilin samun haɓa a fuskar mutum, za ka yi mamakin yadda Pampush ya ɗauki tsawon lokaci yana gudanar da bincike a kan haɓar.

Ko ba komai nazarin ya ƙara sa buƙatar faɗaɗa bincike da kuma fahimtar irin sarƙaƙiyar da ke tattare da halittar mutum. Kuma wannan ya nuna yadda wata halitta ta jikin mutum take daban.

Halitta da dama da mutum yake da, wasu dabbobin ma suna da. Yadda haɓar mutum ta yo gaba, kuma idan muka duba yadda ta yi hakan ka iya taimaka mana mu fahimci ƙarin wani abin na yadda halittarmu ta kasance.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Chins are a bit useless so why do we have them?