Kakanninmu abincin kuraye ne?

Hakkin mallakar hoto Javier TruebaMSFSPL

Alamun haƙora da aka gani a jikin ƙasusuwan ƙwarangal na mutanen da sun nuna cewa kuraye sun riƙa cinye mutane shekaru dubu dari biyar da suka wuce.

Ga nazarin Melissa Hogenboom

Shekaru dubu dari biyar da suka gabata wata kura ta mayar da gawar daya daga cikin kakanninmu na zamanin da.

An gano cewa kurar ta rika yagar gawar mutumin ta wajen kashin cinyarsa, saboda irinalamun da aka gani a tauna a jikin kashin.

An ga ragowar kwarangwal din mutumin ne a wani kogo na wani kauye da ke wajen birnin Casablanca na kasar Morocco, wanda wannan yanki ne da daman ake samun kasusuwa na mutane da dabbobi na zamanin da.

Hakkin mallakar hoto C. Daujeard
Image caption Ga alamun fiƙa da tsaga nan ko'ina a jikin kashin na cinya

An tono kashin gwiwar ne a cikin kasa da ake ganin ta kai shekaru rabin miliyan. A yayin wani aikin tono ne a shekarar 1994 aka gano kashin, amma kuma sai bayan shekara goma daga wannan lokaci aka sake gano shi.

Alamun tsagewa da cizo daban-daban da aka gani a jikin kashin suka sa ake ganin wata babbar dabba mai cin nama ta rika cin mutumin.PICTURE 1

''An lalata kashin, an gutsire shi, sannan kuma an tauna shi,'' in ji Jean-Jacques Hublin na cibiyar nazarin kayan tarihi ta Max Planck Institute for Evolutionary Anthropology wadda ke Leipzig, a Jamus.

Wannan ita ce irin illa ko raunin da ke jikin kashin wanda da farko ma ba a gano cewa kashin jikin irin mutanen da ba ne. Mai binciken ya ce, '' Bayan da muka yi wa kashin nazari na tsanaki sai muka ga cewa kashin cinya ne na mutum.''

Ayarin masanan ya yi wa kashin cikakken nazari na irin alamun hakoran da suka ci mutumin, domin fahimtar irin halin da mutanen na zamanin da suka shiga.

Alamar hakoran da aka gani a jikin kashin ta nuna wata babbar dabba ce mai cin nama ta ci mutumin.

Hakkin mallakar hoto C. Daujeard
Image caption Ana iya ganin alamun cin da dabbar ta yi wa mai ƙashin

Alamar wani kashin na wata dabbar da aka samu a kogon ta nuna cewa wata nau'in kura ce wadda babu ita yanzu a doron kasa, amma dangi ce ta kurar wannan zamanin. Ko da yake ba a lokaci daya da mutanen na zamanin da suka rayu a kogon ita ma dabbar ta zauna a wurin ba.

Hublin ya ce, ''Ga alama mutane da dabbobi masu cin nama sun yi amfani da kogon dukkaninsu, saboda haka akwai kusanci tsakanin halittun biyu.''

Idan aka tsaya aka yi lissafi na natsuwa za a iya cewa wata irin kura ce ta zamanin da ta yi wa kashin wannan illa, kamar yadda ayarin masu binciken ya rubuta a rahotonsa a mujallar PLOS ONE.

Irin yaga da cin kashin da aka gani a jiki ta yi daidai da irin illar da kura ke yi wa kashin dabba ko mutumin da ta ci, in ji jagorar hada rahoton Camilla Daujeard, ta dakin kayan tarihi na Paris a Faransa.

Hakkin mallakar hoto Cicero MoraesCC by 3.0
Image caption Mutanen zamanin da ƙwararrun mafarauta ne

Ba mu sani ba ko kuraye sun rika farauta da cinye mutanen zamanin da ba, ko kuma mutumin ko matar ta mutu ne a sanadiyyar wani abin daban sannan kuma kurayen da ke farautar nama suka samu gawar suka ci.

Babu wata cikakkiyar sheda da za ta nuna an yi gumurzu, kamar wata mummunar karaya ko illa a jikin kashin tsakanin halittun biyu.

''Alamun hakorin wata dabba mai cin nama a jikin kashin mutum bai isa zama hujjar da za ta tabbatar da cewa dabbar ta rika cin mutane a zamanin ba.'' In ji Daujeard.

Abu ne mai ban mamaki da aka gano, in ji masu binciken, saboda kadan ne daga kasusuwan mutanen da wadanda ake ganowa ake ganin alamar da ke nuna, wata babbar dabba ce ta cinye mutanen.

Daujeard ta kara da cewa, ''Duk da dai cewa a zamanin da ana samun gogayya ta sosai, amma babu wata alama ta fada kamar ballewar kashi a jikin kashin da aka tono.''

Hakkin mallakar hoto Javier TruebaMSFSPL
Image caption Mutanen zamanin da na farautar dabbobi suma kuma dabbobin na farautarsu

Hublin ya kara da cewa, ''Ba mutane da yawa a lokacin. Saboda haka kura ko wata damusa za ta fi samun damar cin wani abin daban maimakon mutum, kamar yadda lamarin yake a zamanin yanzu, ballantana ma a wancan lokacin da ba mutane kamar yau.''

Mun san cewa mutanen wancan zamanin, halittu ne masu dabara, wadanda tuni suka saba amfani da kayan farauta, kamar mashi da gatari wajen kashe dabbobin zamanin. Kuma ba shakka dabbobin da suke farauta a lokacin sun hada da kuraye.

Daujeard ta ce, abin da sabon binciken ke nunawa shi ne, su kansu dabbobin da mutanen da din suke farauta, sun isa su yi farauta da kashe mutanen su ma.

Idan mutum ya yi nasarar farauta da kashe wadannan dabbobi masu hadarin gaske a matsayin abincinsa, to hakan kenan ya kasance wata dabara da dan adam ke rayuwa kenan.

Da hakan mutane a lokaci daya suna sama wa kansu abinci da kuma kawar da barazana ga rayuwarsu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The hyena that ate our ancestors