Mutanen da sun fi son cin kan giwaye?

A zamanin mutanen da masu amfani da duwatsu wajen yin kayayyakin amfaninsu na yau da kullum, kan giwa shi ne babban abin da suka fi jin daɗi a matsayin abincinsu saboda amfaninsa ga lafiyarsu.

Matt Walker ya yi mana nazari

Mutanen da suka rayu a zamanin da duniya ba ta da ci gaba sai na yin kayan amfaninsu na rayuwa da duwatsu, sun fi jin dadin kan wata katuwar giwa wadda ba sauran irinta yanzu a doron duniya.

Kamar yadda wani sabon bincike ya nuna mutanen zamanin wadanda aka fi sani da mutanen zamanin dutse, suna farautar giwaye ne domin cinsua a matsayin wani abinci mai daraja da amfani.

Duk da cewa suna cin sauran jikin giwayen amma dai sun fi ba wa sassan kan da suka hada da kwakwalwa da haure da harshe da kashin kai da na haba da sauransu muhimmanci

As well as eating their bodies, they made the most of the animals' huge heads. They scooped out and ate the elephants' brains, but also their trunks, tongues, glands, and even their skulls and lower Wannan shi ne ya bayyana dalilin da ya sa mutanen zamanin suka rika yawo daga wuri zuwa wuri da kawunan giwaye.

Hakkin mallakar hoto Pete Oxfordnaturepl.com
Image caption Ƙashin kan giwa ya kan kai nauyin kilogram 180, kusan buhun siminti hudu

An dai rika yin muhawara mai zafi kan yadda ake ganin mutanen zamanin na cin giwaye. Kuma da dadewa an yarda cewa mutanen zamanin da sun rika farautar giwaye da sauran dabbobi domn samun abinci mai gina jiki.

Wani mai bincike ya wallafa a mujallar Quaternary International cewa cin nama al'ada ce ta mutum tun daga farkon zamani har zuwa yau.

Amma kuma wasu masana kimiyya na ganin kamar giwaye sun yi wa mutum girma sosai a ce yana farautarsu, a maimakon haka suna ganin yana farautar matattun giwaye ne wadanda suka mutu saboda shekaru ko kuma wata dabbar ta kashe su.

To amma yanzu wani sabon bincike da aka yi ya nuna cewa mutanen zamanin da din sun rika farautar giwayen ne, domin ya dauki musamman kansu a matsayin wani abinci mai matukar amfani. Domin amfanin kan ne ma har suke tafiya da shi duk inda za su je.

Aviad Agam da Ran Barkai na jami'ar Tel Aviv da ke Isra'ila sun yi nazarin wasu wuraren da aka gano kayan tarihi inda aka samu kawunan giwayen.

Wadannan wurare da mutanen zamanin da suka rayu sun hada da wadanda suka kai shekara miliyan daya da dubu dari shida da na miliyan daya da dubu dari uku wadanda suke kasar Djibouti a Afrika.

Sai wurare da aka rayu a shekara 800,000 da 500,000 a Isra'ila. Sai kuma masu shekaru 150,000 zuwa13,000a fadin kasar Rasha ta yanzu da kuma sassan Turaiphants.

Misali a wani wuri da ake kira Gesher Benot Ya'aqov, wanda aka rayu a zamanin da wanda yake a kwarin tekun Isra'ila da Jordan, masu binciken kayan tarihi a kasa sun gano kasusuwa da sauran sassan wasu halittu da dama.

Halittun sun hada da kaguwa da kifaye da bareyi da kunkuru tare kuma da wasu kawunan giwaye 154 da suka hada da cikakken kashin kai da 'yan wasu hakora da haure.

Hakkin mallakar hoto John Downernaturepl.com
Image caption A zamanin da ana son cin harshen giwa

Akwai kuma wani kan giwar da aka hako a wurin, wanda an daddatsa wani bangarensa an cire, ga lama mutanen zamanin ne da suka rayu a wurin suka yi masa haka.Nau'in giwar zamanin dai na da mikakken haure ne kuma ta fi ta zamanin yau girma.

Giwar wadda a zamanin ta rayu a yankin Turai da Asiya ta kai duk wata dabba ta wancan zamani girma linki biyar, kuma babbar dabba a lokacin ita ce dorinar ruwa.

Kashin kai da na haba na giwar Afrika ta zamanin yau sun kai nauyin kilogram 180. Hauren ya kai kilogram 110,sai kunne mai nauyin kilogram 44, sai harshe mai nauyin kusan kilogram 14. Kwakwalwarta kuwa za ta kai nauyin kilogram 6.5. Gaba daya kan giwa ta zamanin yau ya fi nauyin kilogram 400.

Masana kimiyya sun ce giwar wancan zamanin na da ta linka ta yanzu biyar a girma

Karin shedar da ta tabbatar cewa mutanen zamanin da sun rika farautar giwa musmman domin nama da kasusuwan kanta a matsayin abinci, an samo ta ne daga kogon Bolomor da ke kwarin Valldigna valley, kusa da Valencia a kasar Spain.

Hakkin mallakar hoto FunkMonkCC by SA 3.0
Image caption Ƙashin ƙwarangwal ɗin giwar zamanin da

A cikin kogon an gano kasusuwan giwaye na zamanin da masu yawa da suka hada da na kai da kuma na kafafuwa. Masu binciken sun ce ba karamin aiki ba ne hawa tsaunin inda kogon yake.

Masu binciken kimiyyar sun kuma yi nazari kan yadda mutanen Afrika na zamanin daruruwan shekarun baya bayan nan suke matukar son kan giwa saboda amfaninsa a matsayin abinci.

Wannan ya nuna yadda mutanen suke fasa kan giwa da kashin mummukenta domin fitar da bargo da tantakwashin da ke ciki. Akwai kuma wani kitse da ake samu a kusa da idon giwar da ta mutu da kuma a wani sashe na jikin namijin giwa wanda ake samu a jikinsa idan yana cikin damuwa da sha'awar jima'i.

Yadda mutane suka yawaita farautar giwaye a zamanin da ya nuna kamar yadda masu bincike suka ce, mutane na da hadin kai, domin sai mutane sun taru da yawa za su iya daukar giwar da suka kashe zuwa cikin koguna.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The people who ate elephant heads