Za mu iya hasashen lokacin mutuwarmu?

Hakkin mallakar hoto Jared TarbellCC by 2.0

Tuni masana kimiyya suka gano yadda za su san ranar da kuda zai mutu. To ko hakan na nufin za su iya kintacen ranar da mutum ma zai bar duniya?

Ga nazarin Colin Barras

Mutuwa ba ta da makawa, amma kuma aba ce da za a iya hasashenta? Wasu masana kimiyya suna ganin za a iya hasashenta.

Masu binciken sun ce wasu gwaje-gwaje da suka yi da kuda sun gano wani sabo kuma matakin rayuwa na daban wanda ke nuna matsowar mutuwa. Mataki ne na rayuwa da masanan ke gani mutane ma za su iya samunshi.

Baya da shekara da 25 da ta wuce masana ilimin halitta sun dauka cewa matakin rayuwa biyu ne kawai, na yarinta da kuma na manyanta. Wadannan matakai ne da dukkaninmu kowa ya sani.

Yarinta mataki ne na saurin girma da bunkasa, wato lokacin da ba mu balaga ba. A lokacin wannan rayuwa ko mataki ba a kawo mutuwa kusa. Matakin manyanta ya fara ne da lokacin da muka balaga.

Harwayau a nan ma ba kasafai ake kawo ma mutum mutuwa a wannan lokaci, domin lokaci ne da muke ganiyar rayuwarmu, inda za mu haifi yara.

To amma yayin da muke shekaru sai jikinmu ya fara tsufa da raguwa. A Duk shekara mutuwa na matso mana. Da farko a hankali a hankali amma muna kara shekara tana kara matso mana da sauri da sauri.

Hakkin mallakar hoto Weestock ImagesAlamy
Image caption Yarinta na tattare da saurin girma

A farkon shekarun 1990 masu bincike sun gano cewa rayuwa na kunshe da wannan mataki da a da ba a gano ba, wanda mataki ne da mutanen da suka manyanta ko tsufa sosai suke ratsawa.

Abin da ya bambanta wannan mataki na uku na rayuwa wanda tsofaffi ke kaiwa da kuma mataki na girma, wato na bayan balaga, shi ne, yanayinsa na kusantar da mutum ko rai ga mutuwa.

Yanayin hauhawar yuwuwar mutuwa daga shekara zuwa shekara a yayin da mutum yake matakin manyanta na bayan balaga, babu shi a wannan mataki na uku da masanan suka gano.

Yadda yuwuwar mutuwa ke kan mai shekara 60 ta fi ta mai shekara 50, shi mai shekara 90 da mia shekara 100 kusan yuwuwar mutuwarsu daya ce.

Har zuwa yau ana muhawara a kan yadda wannan karuwa ta yuwuwar mutuwa ke kasancewa, domin babu bayani daya da za a ce kowa ya yarda da shi.

Domin karin haske a kan matsalar, Laurence Mueller na jami'ar California a Irvine da abokin aikinsa Micheal Rose sai suka fara duba wasu abubuwan da a rayuwar halitta da suke nuna irin wannan yanayi na kamar yadda kusantar mutuwar ke nunawa na zama daya wato daidai iadn aka kai wannan mataki na karshen rayuwa.

Ya ce suna son ganin ko yuwuwa ko damar haihuwa ita ma tana bin irin wannan tsari ne na yuwuwar mutuwa. Daga nan ne suka fara nazari a kan wani nau'in kuda da ke bin kayan marmari na 'yan itace.

Mueller ya ce, ''daga nan ne sai muka tara matan wannan kuda 2,828, suka ware kowace mace suka hada ta da maza biyu, kulluma sai mu dauke mace daya, mu ware ta zuwa wani wuri na daban, mu kuma kiraga saura kwai nawa ya rage ta yi. Haka muka rika yi har sai da duka suka mutu.''

Bayan duka wannan sai sakamakon ya nuna alamun babu wani abin a-zo-a-gani. Yawa ko damar haihuwa ba ta nuna daidaito ba a lokacin da kudajen suka shiga matakin karshen na kusa da mutuwa.

Hakkin mallakar hoto Solvin Zanklnaturepl.com
Image caption Kudan da ke bin kayan marmari na nuna alamun lokacin da zai mutu

A zahiri ma lokacin da masu binciken suka yi nazarin bayanan da suka tattara sai suka gano wani abu ne daban ma yake faruwa.

Mueller ya ce, ''idan na ware matan da suka kusa mutuwa, kuma na kwatanta su da matan da suke kusan kwanakin haihuwa daya da su, wadanda kuma na san suna da sauran makonni da za su rayu, sai na na ga suna da bambancin damar haihuwa.''

A takaice dai abin da suka gano shi ne, yawan kwayayen da matar kudan ke yi yana raguwa a makwanni biyu da suka rage mata ta mutu.

Wani abu da wannan raguwa ta yawan kwai shi ne, ko da matar da ta kusa mutuwar 'yar kwana 60 ce, yawan kwan da take yi yana raguwa idan ta kusa mutuwa, haka ma idan 'yar kwana 15 ta kusa mutuwar ita ma yawan kwan da take yi yana raguwa.

A shekara ta 2012, misali sun gano cewa shi ma kudan (namiji) yana shiga irin wannan yanayi na raguwar damar haihuwa idan ya kusa mutuwa.

Mueller ya ce, ''to amma idan namiji ya kusa mutuwa ko yaro ne ko tsaka-tsakiya ne ko tsoho ne, damarsa ta haihuwa tana raguwa kasa da mazan da suke sa'o'insa wadanda za su rayu ta wasu karin makonnin da yawa.''

A kwana kwanan nan, a 2016, Mueller da Rose sun tattara bayanai daga wasu jerin gwaje-gwaje da wasu masu binciken daban, suka yi har a wurare hudu, kuma a nan ma sun gano wannan alamu na mutuwa.

Hakkin mallakar hoto Bernard Castleleinnaturepl.com
Image caption Haihuwa ma na da irin kalubalenta

Masu binciken biyu da abokan aikinsu har ma sun gano cewa, za a iya hasashen ranar da wani kuda zai mutu, ta hanyar duba yanayin damar haihuwarsa kwanaki uku da suka gabata, tare da yin watsi da duk wasu bayanai kamar kwanakin kudan a duniya. Mueller, ya ce, kusan kashi 80 cikin dari hasashensu na mutuwar yana yin daidai.''

Rose da Mueller ba su kadai ba ne suka alakanta haihuwa da mutuwa, domin James Curtsinger a jami'ar Minnesota shi ma ya yi ta gudanar da irin wannan bincike, wanda shi ma ya samu irin sakamakon nasu.

Sai dai an dan samu bambanci tsakanin binciken na Curtsinger da na su Mueller ta wani fannin. Shi ba ya ganin abubuwan da aka gano sheda ce ta wani mataki na daban a rayuwa.

Shi bai yarda cewa mutum da sauran halittu wadanda bdaban suke da wannan kuda za su iya samun yanayin raguwar haihuwa daya ba. Kuma ya nuna rashin yardarshi da wannan mataki na mutuwa, inda ya kawo tashi fahimtar wadda yake ganin masana kimiyyar halitta za su amfana da ita.

Ya ce, ''lokacin da nake dan shekara 20 da wani abu abin da na mayar da hankali a kansa wurin bincike shi ne bambanci tsakanin yawan maza da mata, a lokacin da na kai shekara 40 da wani abu sai na karkata kan bincike kan shekaru, yanzu kuma da na kai 65 ina bincike kan wani abu sabo da na kira ritaya.''

Curtsinger ya kara da cewa, ''wannan abu ne da zai iya sa masu binciken kimiyya su sake tunani a kan nazariyyarsu ta shekarun ritaya (barin duniya). Abu ne da ya fara a ranar da balagaggiya (tamatar kuda) ba ta yi kwai ba.

Menene muhimmancin wannan kwatanci na yin kwai da wannan tamatar kuda?

Ita tamatar kudan 'ya'yan itace ba abin da ta sani sai zuba kwai, domin a rayuwarta tana yin kwai kusan 1,200. To idan ya kasance ta yi rana daya ba ta yi kwai ba, ko da ta dawo daga baya ta cigaba, to ka sani akwai wata matsala.

Sama da shekara goma da ta wuce James Carey na jami'ar California a Davis tare da abokan aikinsa sun nuna cewa ta hanyar gyara mahaifar bera za su iya kara tsawon rayuwar bera.

Masanan sun yi wa wata tsohuwar tamatar bera tiyata ne suka sauya mahaifarta da ta tsufa suka snya mata wata ta wadda ba ta kai ta tsufa ba. A dalilin hakan sai ta rayu fiye da yadda a da aka yi tsammani za ta kai kafin a sauya mata mahaifar.

Mai binciken ya ce akwai shedar da ta nuna cewa tamatar da aka sauya wa mahaifar tana lafiyayyar zuciya da 'yan matsaloli marassa yawa fiye da wadda ba a sauya wa mahaifar ba.

Curtsinger ba lalle ba ne ya yarda cewa mutane ma suna bi ta wannan mataki nasa na ritaya a rayuwa kafin su mutu, amma Mueller yana ganin mutanen da za su mutu, mutuwa wadda ba ta sanadin wani abu na dan adam ba, sai sun bi wannan mataki.

Hakkin mallakar hoto ReynermediaCC by 2.0

Domin tabbatar da hakan masanan sun yi wani bincike a gidan wasu tsofaffi 'yan shekara 90 zuwa 99 a Denmark, inda suka yi nazarin karfinsu da tunaninsu. Bayan 'yan shekaru masanan suka dawo gidan tsofaffin domin ganin su waye suka mutu kuma su waye suke da rai.

Mueller ya ce, wadanda ba suke baya a wadancan matakan da aka yi na gwajin karfi da tunaninsu su ne suka mutu. Wannan ya tabbatar cewa akwai dakushewa ko raguwar karfi da sauran abubuwa na zahiri a jikin mutumin da ya kusa mutuwa.

Msanin ya ce fahimtar wannan ilimi zai iya sa rage yawan lokacin da rayuwar mutum ke tabarbarewa kafin rasuwarsa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Can we predict when we will die?