Kashi nawa na jikinka ka mallaka?

Hakkin mallakar hoto Beyond Words

A dukkanin kwayoyin halittar da ke jikinka nawa daga cikinsu ne naka? Jikinmu daban yake saboda irin baiwar halittar da ke tattare da shi.

Ya kunshi sinadarai da sauran abubuwa da ke da daraja a kasuwa; miliyoyin bayanai da dubban biliyoyin kwayoyin halitta wadanda yawanci ba namu ba ne.

KA SAN CEWA:

• Darajar Bill Gates dala 1,956 kawai

• Kwayoyin halittar da ke kodar mawakin zamani dan kasar Canada, Justin Bieber, sun fi na cikin kwakwalwarsa sau linki biyar

• Kwayoyin halittar jini da ke ba wa jikin gwarzuwar 'yar wasan tennis Serena Williams kuzari biliyan dubu 24 da bliyan dari biyar ne

• Jikin mutumin da ya kirkiro Facebook Mark Zuckerberg yana dauke da bayanai masu yawan miliyan dubu 800 ne ( 800MB)

• Kwakwalwar Shugaba Barack Obama ita ke tafiyar da zuciyarsa; kwakwalwar tana da nauyin kilogram daya da digo hudu (1.4kg), yayin da kwakwalwarsa ke da nauyin kilogram digo hudu kawai (0.4kg)

Barka da zuwa sashen sanin yadda aka yi ka da kuma yadda aka yi ni, wata sabuwar hanya ta fasaha daga BBC wadda ke fashin bakin bayanan jikin mutum.

Abin da za ka yi kawai shi ne ka sanya ranar haihuwarka, da jinsinka (lokacin da ka haife ka) da tsawonka da kuma nauyinka, sannan sai ka zabi irin awon da za ka yi amfani da shi wanda ka ga ka fi so.

Kuma nan take za ka san:

• Sinadaran da ke jikinka, da kuma darajar jikin naka a kasuwa.

• Kwayoyin zarra na halitta nawa ce a jikinka kuma me za a iya yi da su

• Kwayoyin halitta na kitse da na jini da na fata da kuma na kwakwalwa nawa gare ka

• Bayanan da suka danganci kwayoyin halitta a cikinka guda nawa ne

• Mitsi-mitsin halittu wadanda ido ba ya iya gani nawa ne suke rayuwa tare da kai a jikinka

• Ya girma da nauyin kayan cikinka suke

• Kawo yanzu ya yawan fitsari da kashi da maniyyi da kuma kwayayen da ka fitar yake.

• Sau nawa ka kifta ido da numfashi da hamma da tusa

• Da dai sauran abubuwa masu yawa

Bincika ka sha mamaki ka kuma nuna wa abokanka ko dai gaba dayan shafin ko kuma abubuwan da kake son sani idan ka hada muhimman bayanan jikinka.

Wanna shi ne labarinmu, labarin yadda aka halicci ni da kai.

Za ka iya cin moriyar wannan tsari ta wayar salula ko babbar waya mai kwanfuta ( tablet ) da kuma kwamfuta ta tebur. hanyoyin shiga intanet da za su dacewa su ne Chrome da Firefox da Safari da Internet Explorer 10.

Ga yadda aka yi amfani da wannan fasaha ta kididdiga a kan halittar wasu fitattun mutane

Bill Gates;

Ranar haihuwa: 28 ga watan Octoba, 1955. Jinsi: Namiji. Tsawo: 177cm, Nauyi: 67kg Asali : http://www.howmuchisnetworth.com/t11-bill-gates-net-worth-2016

Justin Bieber;

Jinsi: Namiji. Ranar haihuwa: 1 ga watan Maris, 1994. Tsawo: 175 cm, Nauyi: 66 kg

Asali: http://healthyceleb.com/justin-bieber-height-weight-body-statistics/1384

Serena Williams;

Ranar haihuwa: 26 ga watan Satumba, 1986. Jinsi: Mace. Tsawo: 170 cm, Nauyi: 70 kg

Asali: http://heightandweights.com/serena-williams/

Mark Zuckerberg;

Ranar haihuwa: 14 ga watan Mayu, 1984. Jinsi: Male. Tsawo: 175 cm, Nauyi: 73 kg

Asali:http://hollywoodmeasurements.com/mark-zuckerberg-height-weight-body-measurements/

Shugaba Obama:

Ranar haihuwa: 4 ga watan Agusta, 1961. Jinsi: Namiji. Tsawo: 185 cm, Nauyi: 81.6kg Asali: Gwajin fadar White House

https://www.whitehouse.gov/sites/default/files/rss_viewer/potus_med_exam_feb2010.pdf

Domin jarraba wannan tsari ka je kan labarin na Ingilishi, kamar yadda za a iya shiga labarin ta kasan nan.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How much of your body is your own?