Dalilin iyaye na mulmula kan 'ya'yansu

Hakkin mallakar hoto Didier DescouensCC By 3.0

A yankin Patagonia na Latin Amurka, shekaru 2,000 da suka gabata, al'ada ce a tsakanin al'ummar yankin su sarrafa ƙoƙon kan jariransu ya zama yadda suke so.

Hakan zai iya kasancewa wata hanya ta kulla dangantaka tsakanin iyalai.

Ga nazarin Melissa Hogenboom

Idan ka shafa keyarka za ka ji tana da kwari sosai. Amma lokacin da mutum yake jariri ba ta kai haka karfi ba kuma idan aka bi hanyar da ta dace za a iya sauya siffar kan mutum ya zama yadda ake so, sauyin da zai zama na dindindin har abada.

Wannan al'ada ta mulmula kan mutane an gano a tarihi ana yinta a tsakanin al'ummomi a duniya tun shekara 45,000 da ta wuce har zuwa yau. Wasu na yinta domin ado, wasu domin mulki. Amma yawanci sai dai kawai mu yi hasashen abin da ya sa mutane suke yi.

Yanzu dai ana gano cewa wannan ala'ada ce da ta yi suna a tsakanin wasu al'ummomi na yankin Patagonia da ke Latin Amurka shekaru dubu biyu da suka gabata. Wasu gomman kokunan kawunansu da aka gano na karin gaske kan dalilan da suka sa suke yin wannan al'ada.

Hakkin mallakar hoto AlfonsoDurrutyAJPA
Image caption Ƙoƙon kan da aka sake mulmulawa

A shekarar 2009 wasu kwararrun masu binciken kayan tarihi na karkashin kasa sun gano wasu abubuwan ban mamaki na kokunan kawunan mutane a wata makabarta ta zamanin da.

An gayyaci Marta Alfonso-Durruty, ta jami'ar jihar Kansas a Manhattan ta Amurka, zuwa kasar Chile domin ta yi nazari a kan wadannan kokunan kai.

Lokacin da ta je ta fara duba kokunan kan sai ta gano wani abu na daban, inda ta ga kawunan duk suna da wata siffa daban da yadda aka saba ganin kawunan mutane, abin da ba a taba sani ba a kokunan kawunan da a da aka taba samu a yankin na Patagonia. Daga cikin kokon kai 60 18 an sake siffarsu.

In bayan wani guda daya wanda siffar tasa ta fito sosai kuma ta yi daban, kusan dukkanin sauran sai mutumin da ya kware a wannan aiki ne zai iya sanin cewa an jirkita siffarsu.

Hakkin mallakar hoto Didier DescouensCC by SA 3.0
Image caption Yadda kan mutumin da aka sake mulmula shi yake

Mulmula kokon kai ba abu ne mai sauki ba, domin idan yaro ya riga ya girma kan ya yi kwari to ba zai yuwu a sauya siffarsa ba.

Saboda haka dole ne idan har ana son sake siffar kokon kan mutum, dole ne sai an yi tun yana jariri jim kadan da haihuwarsa. Wata hanya da iyaye ko kwararru masu mulmula kai suke yi, ita ce ta daure kan da kyau da tsumma. Wannan sai ya sa kan ya yi tsini ya zama kamar gwangwani.

Sai dai wannan hanyar tana da hadari, domin idan aka daure kan da kyau sosai to zai iya kashe jariri, kamar yadda ta faru a wasu gawarwaki da aka gano a Peru a shekara ta 2008.

Wata hanyar da ake yin wata siffar kuwa ita ce ta sa kokon ya zama kamar fale-fale, kamar yadda ake iya gani a hoto na kasa, wanda ake yi da katako mai fadi (fulanki) kamar allo.

A wannan ana danna kan jariri ne ya kwanta a jikin allon zuwa lokaci mai tsawo, wani lokaci a gaba da bayan kan. ''Za a ga kamar wani ya buga wa bayan kan kofa, ''in ji Alfonso-Durruty.

Hakkin mallakar hoto modified from AlfonsoDurruty et al. 2015AJPA
Image caption Wannan ƙoƙon kan a shafe yake daga ƙeya

''Ana daure jaririn ne a kan allon, saboda haka uwar ba ta da wata fargaba a kan jaririn.. Ga alama wannan tsarin bisa kuskure aka gano shi da farko,''in ji Mercedes Okumura, mai nazarin kayan tarihi na karkashin a dakin adana kayan tarihi na jami'ar tarayya ta Rio de Janeiro a Brazil.

''Bayan wani lokaci sai mutane suka ga kan jaririn ya yi fadi daga nan ne sai mutane suka fara amfani da wannan dabara wajen sake siffar kan jariri ya yi fadi kamar allo.''

Idan aka yi wa kai hakan shikenan ba zai kara taba dawowa yadda yake ba. Wannan wata hanya ce ta aal'ada da mutane ke yi domin sanin kabilarsu ko danginsu. Za ta ma iya kasancewa wata hanya ta neman kyau in ji Okumura.

Masaniyar ta ce, ''akwai kawakkwarar shedar da ke nuna cewa ana yin wannan al'ada ce ba domin nuna wani matsayi ba kawai a cikin al'umma ba, har ma da neman tabbatar da wani matsayi na iko. Saboda haka al'ada ce a tsakanin al'umma da kuma hanyar bambancewa a tsakanin kabila.''

Hakkin mallakar hoto Hermann BrausPublic Domain
Image caption Wani gadon katako da Amurkawa na asali a da suke amfani da shi, su sa kan jarirai ya yi tsini

A wani lokacin ana amfani da siffar kan a matsayin wata alama ta matsayin mutum a cikin al'ummma: haka al'ummar Oruro na Bolivia suke. ''Wadanda suke da babban matsayi a cikinsu kansu ya yi gungurungun sama, masu tsaka-tsakin matsayi , kan nasu ya yi gungurungun kasa, yayin da sauran jama'a kuma kansu ya yi fadi,'' in ji Okumura.

Amma kuma su al'ummar Pantagonia masu yawon farauta a zamanin da ba su yi rayuwa irin ta wadanda ke da wani fitaccen tsari na jama'a ba, inda za a fi ganin wannan bambanci ya fito fili na tsakanin matsayin jama'a, masu matsayi da marassa matsayi..

Maimakon haka sun yi rayuwa ne ta kaura daga wannan wuri zuwa wancan. Saboda haka ne Alfonso-Durruty ta yi mamakin ganin yadda aka samu kokunan kai masu yawa da aka sauya wa siffa a cikinsu.

Ta ce kila ba sun yi hakan ba ne domin wata al'ada ta gane junansu, sai dai watakila domin hakan ya taimaka musu su fadada yankunan da suke rike da su kuma su samu damar mallakar sabbin ma'adanai.

Ita da sauran abokan aikinta ne suka wallafa wadannan bayanai a wata sabuwar kasida a mujallar American Journal of Physical Anthropology.

Za a ga wannan kamar wani bakon abu ne. Ta yaya siffar kokon kan mutum za ta iya taimaka wa wata al'umma samun damar kama karin sabbin wurare?Amma idan ka fara tattara bayanai za ka ga yadda abin zai iya kasancewa.

Hakkin mallakar hoto Didier DescouensCC By 3.0
Image caption Wani ƙoƙon kai irin na mutanen Peru na da, wanda ake sarrafa kan jariri domin ya zama haka

Wadannan mutanen sun rayu ne a wuraren da suke da albarkatu 'yan kadan a warwatse nan da can in ji Alfonso-Durruty. Ta ce a yanayi irin wannan dabarar da za ka bi ka samu cin moriyar alabarkatun ita ce, ku warwatsu ku kama wurare da yawa.''

Hanyar da za ka fi fadada yankunanka ita ce ta kulla zumunta da wasu mutanen. Saboda sake siffar kokon kanka ba abu ne mai sauki ba, ko ka yi na bogi, wadanda suka yi hakan sun nuna masu gaskiya da biyayya ne.

Yin hakan zai nuna kulla dangantaka da sauran jama'a da ke yankin, in ji Alfonso-Durruty. Yin tsage a jiki bazai yi tasiri kamar yadda jirkita siffar kai za ta yi ba.

Nazarin da masanan suka yi ya kara tabbatar da alamun gaskiyar bincikensu domin duk abin da muka ci yana barin dan alamunsa a jikin kashinmu, saboda haka ta hanyar gwaje-gwaje a kan kasusuwansu masanan sun gano cewa mutanen na yankin Latin Amurkan (patagonia) suna cin abinci iri-iri, na tudu da kuma na ruwa, abin da ke nuna sun rayu a wurare daban-daban.

Har yanzu akwai tambayoyi da dama da ke bukatar amsa.

Hakkin mallakar hoto RamaCC by SA 2.0
Image caption Ana ɗaure kan jariri ne da tsumma domin ƙoƙon kan ya zama haka, kamar gwangwani

Misali ba mu san tsawon lokacin da aka kai ana yin wannan al'ada ta mulmula kai ba, maza ne ko mata suka fi yi. Kuma ba mu san wace irin siffar ce aka fi so ba, da dalili.

Mun san cewa jarirai ba su da zabin abin da iyayensu za su yi musu a jikinsu kamar mulmula kansu. Amma idan ka duba yawan mutanen da a yau za a ce suna son a sauya musu siffar jikinsu sosai, za ka ga ba abin mamaki ba ne ka ga wasu iyaye sun yanke shawarar sauya siffar kokon kan 'ya'yansu, musamman ma idan hakan zai sa 'ya'yan su samu wani cigaba a rayuwa iadn sun girma.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Parents reshaped their children's skulls, for their own good