Me ke sa ba ma ganin abin da ke nesa ?

Me ke jawo mana larurar kasa ganin abin da yake a nesa? Larurar kasa ganin abin da yake a nesa da kyau na daga cikin matsalolin da suke damun mu. To amma shin ba mu fahimci abubuwan da suke haddasa ta ba ne da kuma yadda ake maganinta ba?

David Robson ya duba wannan matsala.

Lokacin da na ke yaro, sai a hankali a hankali na fara samun larurar gani, lamarin da ya sa na fara amfani da tabaran likita. Lamarin sai ya rika karuwa har ta kai ana ta kara min karfin tabaran. ''Shin me ya sa hakan ?''

Wannan, ita ce tambayar da nake yi wa likitan idona. Yayin da nake kokarin amsa masa abubuwan da nake gani idan yana jarraba karfin idona. To amma lamarin sai ya kai ko da yaushe sai karamin magani yake yi amma abi ba sauki.

A ko da yaushe amsarsa daya ce. Yana dora alhakin matsalar a kan kwayoyin halittata na gado da kuma yawan karatu da nake yi. Abun da mutane da dama suke dauka shi ne amfani da tabaran likita yana kara tsananta larurar rashin gani da kyau.

Wannan ba gaskiya ba ne sam-sam, in ji likitana, duk da dai ba ni da damar in yi masa musu. Ina jin kai ma haka likitanka ya gaya maka idan kana da larurar idanu ta kasa ganin abun da yake nesa da kyau.

To amma wasu bincike da aka gudanar a baya bayan nan sun nuna cewa lamarin ba haka yake ba.

Abubuwa da dama na muhallanmu na zamanin nan da alamu su ke haddasa wannan larura ta idanu. Kuma idan za a dauki 'yan matakai kalilan za mu iya kare 'ya'yanmu daga wannan matsala da ta addabe mu.

Maganar cewa gadon larurar raguwar karfin idanu ake yi, ko alama ban taba yarda da ita ba. In banda ta hanyar amfani da tabarauna na likita to ba zan iya bambance tsakanin dutse da mugun-dawa ba(dabbar daji). Irin ci gaban da aka samu bai kai ace tun a baya an kawar da kwayar halittar da take haddasa larurar idanun ba?

Amma duk da haka wannan matsala ta kasa ganin abin da yake nesa da kyau na cigaba da zama annoba, inda kashi 30 zuwa 40 cikin dari na mutane a Turai da Amurka na bukatar tabaran likita, kuma wannan yawa ya karu zuwa kashi 90 a wasu kasashen Asiya.

Idan har mutane suna da kwayoyin halitta da ke jawo wannan larura ta gani, ya za a yi a ce an kawo wannan karni ba a magance su ba duk da illarsu.

''Bayanin mutanen Eskimo''

A gaskiya rayuwar 'yan kabilar Inuit na kasar Canada ta isa kawar da wannan fahimta ko tunani tun kusan shekara 50 da suka wuce. Yayin da manya 'yan wannan kabila ba su san wannan larura ta gani ba, to amma kusan kashi 10 zuwa 25 na 'ya'yansu na bukatar tabaran kara gani na likita. ''Hakan ba za ta taba kasancewa ba idan da akwai wani abu makamancin kwayar halitta ta cuta da ke rage ganin mutum.'' in ji Nina Jacobsen ta asibitin Jami'ar Glostrup da ke Copenhagen.

Haka kuma a kusan tsawon wannan lokaci, 'yan kabilar ta Inuit suka fara barin rayuwarsu ta gado wato ta farauta da kamun kifi, suka rungumi rayuwar zamani ta Turawa, wanda ake ganin hakan ne ya jawo gushewarsu. Larurar raguwar karfin idanu cuta ce ta zamani, in ji Ian Flitcroft na asibitin yara na Jami'a da ke Dublin.

Ya ce, kwayoyinmu na halittta za su iya taka rawa wajen waye zai iya gamuwa da wannan larura ta idanu, amma duk da haka sai an samu sauyin yanayin muhallin mutu hakan zai fara bayyana.

Wani abu da ake ganin na da nasaba da wannan larura shi ne ilimi ko yawan karatu; wanda wannan na daya daga cikin abubuwan da ake yawan dangantawa da larurar raguwar gani ko karfin ido, wanda da farko za a ga kamar haka lamarin yake, musamman idan ka dubi tarin yawan masu sanye da tabaran likita a duk wani zauren lacca na jami'a ko wani wurin taron da ya shafi ilimi, za ka ga alamun hakan.

To sai dai kuma cikakken bincike ya nuna lamarin bai kai yadda aka dauka ba. Dakta Ian Flitcroft, ya ce, a duk lokacin da aka gudanar da bincike a kan hakan, muka kuma auna yawan karatun da mutane suke yi, sai mu ga lamarin ba haka yake ba, ba dangantakar raguwar karfin ido da yawan karatu.

Wani babban bincike da aka gudanar sakamakon ci gaban da yara suka samu a Ohio, ya nuna babu wata dangantaka tsakanin matsalar raguwar karfin idanu da yawan karatu, ko da yake dai ba za mu kawar da yuwuwar hakan ba gaba daya ya zuwa yanzu, in ji Dakta Jacobsen. Ta ce maimakon haka, mutane da dama suna ganin yawan lokacin da mutum ke kasancewa ne a cikin daki ko gida ke haddasa larurar amma ba yawan karatun ba kadai.

Binciken da aka gudanar a Turai da Australiya da Asiya duk ya nuna cewa mutanen da suke kasancewa a waje fiye da cikin gida da wuya su gamu da larurar raguwar karfin idanu kamar wadanda suke zama a gida yawancin lokaci.

Menene shedar hakan? Wani abu da aka yarda da shi yawanci shi ne, hasken rana yana kara karfin idanu. Misali, shi ne, a kwanan nan, Dakta Scott Read na Jami'ar Fasaha ta Queensland, ya sanya wa wasu yara 'yan makaranta wani agogo na musamman da yake nadar bayanan zirga-zirgar daliban da kuma karfin hasken ranar duk inda suka je, na tsawon mintina 30 har zuwa mako biyu.

Sakamakon da binciken ya nuna shi ne cewa, yaran da idanuwansu suke kalau ba su fi masu amfani da tabaran likita kuzari ko kazar-kazar ba, wanda hakan ya kawar da ganin da ake cewa cikakkiyar lafiyar jiki da kuma motsa jikin suna kare lafiyar idanu.

Maimakon haka, aka fahimci cewa amfanin tabaran kara gani ya dogara ne da yawan lokacin da mutum yake yi a cikin hasken rana, ma'ana idan mutum yana kasancewa a cikin hasken rana bukatarsa da tabaran likita za ta ragu.

Wannan ana ganin watakila saboda hasken rana yana taimakawa wajen samar da sinadarin Vitamin D ne, wanda yake karfafa garkuwar jikin dan adama da kwakwalwarsa, da kuma zai iya kula da lafiyar ido. Wani abu da yawanci aka yarda da shi, shi ne, hasken rana yana sa jikin dan adam samar da sinadarin dopamine, a cikin ido.

Ita kuwa larurar raguwar karfin ido, ko kasa ganin abin da yake nesa, hauhawar girman kwayar ido ne ke haddasa ta, wanda hakan yake sa siffar abin da ido yake kallo ta kasa daidaito akan wajen da ya kamata ta kasance (retina) a cikin gululun idon, wanda shi kuma sinadarin dopamine yake rage wannan matsala, sai idon ya kasance cikin koshin lafiya.

'Tasirin launin wuri'

Wani binciken kuma, yana danganta matsalar larurar raguwar karfin idon ne da launin wuri. Bincike ya nuna cewa hasken launin kore da shudi suna tsayawa ne a cikin gaban bangon da yake samar da siffar abin da ido yake kallo, yayin da shi kuwa haske mai launin ja yana kaiwa ne ga bayan bangon idon.

Wannan ya sa Chi Luu, na Jami'ar Melbourne, a binciken da ya yi kan wasu 'yan tsaki, ya gano cewa, tsakin da ya rena a cikin hasken wuta ja suna fuskantar hadarin gamuwa da larurar ido fiye da wadanda ya rena a cikin hasken wuta ko muhalli mai launin shudi ko kore.

To amma kuma Dakta Flitcroft, shi yana ganin matsalar ta danganta ne ga tarin yawan abubuwan da suke gaban mutum. Ya ce, ''idan ka kalli fuskar kwamfutar tafi-da-gidanka, za ka ga, ba ka ganin duk abubuwan da suke bayan kwamfutar sosai.'' ya kara da cewa, ''To amma kuma idan ka daga kanka daga kwamfutar ka kalli wani agogo da ke can gaba, za ka ga kana ganin, agogon sosai, amma kuma za ka ga akwai kuma wasu abubuwan da suke gefe da ba ka ganinsu da kyau.''

Saboda haka a duk lokacin da ka zuba wa wani abu ido, akwai abin da zai rika yi maka gizo(ba ka ganinsa sosai a kusa da abin da ka sa wa ido). Wannan na nuna cewa an fi ganin abubuwan da suke waje, saboda tazarar da suke da itada ido, kuma hakan yana taimakawa lafiyar ido.

Dukkanin wannan bincike dai ba abu ne da masana ke mahawara ba kawai a fagen ilimi, domin za a iya amfani da su wajen gano hanyoyin magance larurar ido.

Misali shi ne, Dakta Luu yana fatan gudanar da wani bincike da za a sa yara wadanda ba sa iya ganin abubuwan da ke nesa, a wani wuri mai shudiyar fitila, wanda yake ganin hakan zai taimaka musu magance matsalar.

A bincikensa kan 'yan tsaki, Dakta Luu,ya gano cewa sanya 'yan tsakin cikin wurin da yake da hasken wuta shudi ya kawar da larurar da zamansu a cikin hasken wutar mai launin ja ya haddasa musu ta rashin ganin abubuwan da ke nesa.

Flitcroft, ya nuna cewa, a kwai gwaje-gwajen da suke nuna cewa za a kai ga nasarar da tabaran likita zai iya magance matsalar rashin ganin abubuwan da suke gefen abin da mutum ya zuba ido a kansa sosai. Haka kuma yana da kwarin gwiwar cewa wani maganin ciwon ido na digawa mai suna atropine zai iya taimakawa.

Daman maganin an gano yana taimaka wa wajen rage matsalar raguwar karfin idon, ta rashin ganin abubuwan da suke nesa.

Flitcroft,ya jaddada cewa, ya zuwa yanzu dole ne a yi hankali ka da a dauki wani mataki a gaggauce. Misali wata mummunar fahimta, ita ce cewa, tabaran likita yana kara matsalar rashin gani da kyau, wanda, ya ce bincike ya nuna cewa lamarin ba haka yake ba, kuma yakamata mutane su yi watsi da wannan fahimta, yana mai cewa, ''binciken da na yi a kaina ya tabbatar min da wannan mummunar fahimta, kamar yadda wani littafi mai cike da cece-kuce mai suna ''Better Eyesight Without Glasses'' yake yadawa.''

Ya ce, ya daina amfani da tabaransa na likita domin idonsa ya gyaru ya rika gani da kyau, amma abin takaici sai matsalar ta linka biyu cikin shekara uku. ''Idan ka tabbatar 'ya'yanka suna gani sosai to kana yin abin da ya dace.'' In ji Flitcroft.

Ya kara da cewa, ga wadanda suke son daukar wani mataki a yanzu, yawancin masu bincike sun yarda cewa barin yara su yi wasa a fili ba shi da wata illa kuma gwajin da ake yi a wasu makarantun yara a Taiwan ya nuna amfanin hakan.

Wanda ke kara nuna cewa,rayuwar mutum a muhallinsa na ainahi, ba ya sa masa matsalar rashin karfin ido da ke hana shi ganin abubuwan da ke nesa.

Ya ce, ''na so a ce na san duk wannan a lokacin kuruciyata. A yau ina amfani da tabaran likita, wanda ya kusan magance mini matsalar idanuna gaba daya, kuma bushewa da kaikayin da idona ke yi wani lokaci ba wani abin damuwa ba ne. Amma idan na yi tunanin irin matsalar da ke tattare da rashin gani sosai, burina shi ne yaran da za a haifa nan gaba su kasance suna gani garau kamar yadda kakanninmu suke a zamaninsu.''

Ga mai sha'awar karanta wannan labarin a Ingilishi latsa nan http://www.bbc.com/future/story/20150116-why-are-we-short-sighted