Shin addini zai taba bacewa kuwa?

Hakkin mallakar hoto Getty

Akidar rashin yarda da kasancewar Ubangiji na ci gaba da yaduwa a duniya, shin hakan na nufin nan gaba kadan addini zai bace ke nan?

Racel Nuwer, ya gano cewa amsar wannan tambaya ba mai sauki ba ce ko alama.

Miliyoyin mutane a fadin duniya suna ganin idan aka mutu babu sauran wata rayuwa. Kuma suna ganin babu wata maganar tashi bayan an mutu ballantana a yi wata rayuwa ta aljanna ko wuta, a takaice ma dai suna ganin babu Allah gaba daya ma.

To wannan akida ce dai da ke iya bunkasa, duk da rashin tagomashin da ake ganin tana da shi.

A yanzu masu wannan akida ta kin yarda da kasancewar Ubangiji sun karu matuka fiye da a baya. In ji Phil Zuckerman, Farfesa a fannin nazarin halayyar dan adam da nazarin akidar da baruwanta da harkokin addini, wanda yake

kwalejin Pitzer ta Claremont a California, wanda kuma shi ne marubucin wani littafi mai suna Living the Secular Life.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani bincike da Gallup International ta yi a kan mutane sama da 50,000 a kasashe 57, yawan mutanen da suke cewa suna da addini ya ragu daga kashi 77 cikin dari zuwa kashi 68 a tsakanin shekara ta 2005 da 2011.

Su kuwa wadanda suke cewa ba su yarda da Allah ko wani abin bauta ba yawansu ya karu da kashi 3 cikin dari, wanda hakan ya sa yawan wadanda ba su yarda da kasancewar Ubangiji ba a duniya ya karu zuwa kashi 13 cikin dari.

Duk da cewa masu akidar kin yarda da Ubangiji ba su ne suka fi yawa ba a duniya, to amma idan aka yi la'akari da yadda yawansu yake karuwa na wadanda suka yarda da kasancewar Ubangiji kuma ke raguwa, za a iya cewa wannan alamun abin da zai iya zuwa ne nan gaba?

Hakan na nufin cewa ke nan wata rana addini zai bace ke nan gaba daya a fadin duniya?

Hakkin mallakar hoto Getty

Abu ne da ba zai yuwu ba ka ce ga abin da zai faru nan gaba a duniya, to amma idan muka duba abin da muka sani game da addini, abin da ya hada da yadda ya faro tun asali da yadda wasu suka zabi su yi imani da shi , wasu kuma suka ki yarda da shi, za mu iya hasashen yadda dangantakarmu za ta iya kasancewa da Ubangiji a 'yan shekaru ko kuma daruruwan shekaru masu zuwa.

Har yanzu masana na kokarin gano abubuwan da suke sa mutum ko kasa ta karkata zuwa akidar kin yarda da Ubangiji, duk da cewa akwai wasu dalilai na bai daya.

Wani daga cikin abubuwan da ke sa mutun ya rungumi addini shi ne, addini yana ba mutum kariya daga yanayi na fargaba ko rashin tabbas.

Saboda haka ba abin mamaki ba ne kasashen da suka fi yawan mutanen da ba su yarda da Ubangiji ba, su ne suka fi bai wa jama'arsu kulawa a fannin tattalin arziki da siyasa da kuma zaman lafiya.

Zuckerman ya ce,da alamu kyakkyawan tsaro a kasa yana rage tagomashin addini, kuma ya kara da cewa, tsarin Jari hujja da samun hanyoyin fasaha da ilimi suma suna da dangantaka da gushewar addini a wasu kasashe.

Matsalar Imani

Kasashen Japan da Biritaniya da Canada da Korea ta Kudu da Holland da Jamhuriyar Czech da Estonia da Jamus da Faransa da kuma Uruguay, dukkanninsu kasashe ne da addini ke da muhimmanci shekaru goma ko sama da haka da suka wuce, amma yanzu suna daga cikin wadanda ba su da mabiya addini sosai a duniya.

Idan aka duba wadannan kasashe za a ga suna da tsarin ilimi da na tsaro masu inganci, ga kuma rashin wani bambanci na sosai tsakanin masu kudi da talakawa, kuma dukkanninsu masu arziki ne dai-dai gwargwado.

Saboda haka mutanen wadannan kasashe za ka ga ba sa fargaba sosai akan wata matsala da za ta iya samunsu, in ji Quentin Atkinson, masanin halayyar dan adama a Jami'ar Auckland ta New Zealand.

Hakkin mallakar hoto Getty

Raguwar tasiri ko mabiya addini na ci gaba da wanzuwa har ma a kasashe irin su Brazil da Jamaica wadanda addini na da matukar karfi da muhimmanci a wurinsu.

Zuckerman ya ce, ''kasashe kadan ne da shekaru 40 ko 50 suka riki addini da muhimmanci a yau suke hakan.''

Ya ce, ''wadda ta zama daban watakila ita ce Iran, to amma ita din ma akwai abin dubawa, saboda mutanen da ba ruwansu da addini za su iya boye akidarsu.''

Amurka tana daya daga cikin kasahen da suka fi arziki a duniya, wadda kuma take da masu addini sosai, to amma wani bincike da aka yi a kasar tsakanin shekara ta 2007 da 2012 ya nuna cewa yawan Amurkawan da suka ce ba ruwansu da addini ya karu daga kashi 1.6 cikin dari zuwa 2.4.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, raguwa ba tana nufin bacewa ba gaba daya ke nan, in ji Ara Norenzayan masanin halayyar dan adam a Jami'ar British Columbia da ke Vancouver a Canada, wanda kuma ya rubuta littafin Big Gods.

Masanin ya ce, tsaron da ake samarwa wani abu ne da ba lalle ya dore ba kamar yadda ake dauka, domin cikin lokaci daya komai zai iya sauyawa.

Direban da ya sha giya zai iya kade wani dan uwanka ya mutu kamar yadda guguwa za ta iya tashin gari, yayin da likita zai iya kuskuren yi wa mutum magani ya mutu a lokaci daya.

Ganin yad da matsalar dumamar yanayi ke illa a duniya kuma albarkatun kasa ke raguwa, wahalhalu da matsalolin da za su iya biyo bayan hakan za su iya sa mutane su yi ta turuwar rungumar addini domin tsira.

Idan ba su tsira daga wahalhalun ba, za su danganta matsalolin da wani dalili ko manufa abin da, Norenzayan, ya ce to a nan ne kuma fa addini yake bayar da ma'ana ko dalilin wata matsala, fiye da duk wata akida ta kin yadda da Ubangiji da muka sani. In ji shi.

Wannan shi ne abin da ke faruwa yau da kullum a asibitoci da wuraren da bala'i ya fadawa a kasashen duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty

A shekara ta 2011 misali, wata gagarumar girgizar kasa ta auku a Christchurch da ke New Zealand, wanda gari ne da yake da yawan mutanen da ba su yi imani da Ubangiji ba.

Nan da nan sai wadanda bala'in ya fada wa suka rika karbar addini ba ji ba gani, amma kuma sauran sassan kasar suka ci gaba da zama kamar yadda suke da akidarsu ta rashin bin addini.

Duk da cewa ba a ko da yaushe ba ne da kuma ko ina za a iya samun wannan sauyi na tasirin addini sakamakon wani bala'i ko matsala, amma a Japan ma addini ya samu bunkasa sakamakon yakin duniya na biyu.

Ko da a ce an magance rikice-rikicen duniya baki daya, duniya ta zauna lafiya cikin gaskiya da adalci ba tare da wani bambanci ba, ana ganin addini zai ci gaba da kasancewa a tsakanin jama'a, ba don komai ba sai domin cewa imani da kasancewar Ubangiji abu ne da yake kamar jini da tsoka a rayuwar dan adam.

Fahimtar wannan yana bukatar duba nazarin nan da ake kira a turance dual process theory, wanda ya kasa tunanin dan adam gida biyu, Sytem 1 da System 2.

Kashi na biyu dai kusan a baya bayan nan aka samar da shi, wanda yana nufin, tamkar wata murya ce da ke kwakwalwar dan adam da ke tsara masa yadda zai yi tunani da gudanar da abubuwansa.

Shi kuwa kashin farko wato Sytem 1 tunani ne da ke wanzuwa a kwakwalwar mutum, wanda ke samuwa a kwakwalwar ko da a ina aka haifi mutum.

Wannan tunani na kashi na daya shi ne yake bai wa dan adam basira ko dabi'ar kin wani abu misali rubabben nama, shi ne kuma ke sa yaro ya fahimci yare ko harshen iyayensa, ya iya ba tare da ya yi tunani ba a duk lokacin da zai fadi wani abu ko zai yi magana da yaren.

Haka kuma wannan shi ne ke sa yara ko jarirai damar gane iyayensu, can kuma gaba a rayuwa har mutum ya yi amfani da shi wajen fahimtar duniyarsa, ya kuma nemi sanin ma'anar wasu bala'oi ko mutuwar wani nasa.

Baya ga taimaka wa dan adam ya kauce wa wani bala'i kashi na farko na tunanin na dan adam kamar yadda masana suka bayyana shi yake sa addini ya faro ya kuma ci gaba.

Kuma wannan tunani shi ne yake sa dan adam ya gane abin da zai cuce shi ya kauce masa kamar zaki da ya labe ko miciji da ya yi kwanto a ciyawa yana dakon mutum.

Hakkin mallakar hoto Getty

A bisa wadannan dalilai da ma wasu da yawa masana da dama suna ganin addini ya samo asali ne daga halittar tunanin dan adam. In ji Robert McCauley na Jami'ar Emory ta Atlanta a Georgia, wanda ya rubuta littafin, Why Religion Is Natural and Science Is Not.

Norenzayan ya ce,ilimi da nazari ko fahimtar kimiyya da kuma tunani mai zurfi su za su iya sa mutum ya daina yadda da abin da zuciyarsa ta raya masa na fahimta, amma kuma duk yadda mutum ya yi wannan tasiri na tunanin zuciyar tasa yana nan.

A daya hannun kuma ilimin kimiyya wanda wadanda ba su yarda da kasancewar Ubangiji ba da makamantansu suka dogara da shi domin fahimta da sanin abubuwa na rayuwa ba abu ne mai sauki ba.

Domin ko shi kansa ilimin kimiyyar akwai abubuwan da ake dangantawa da shi, wadanda dan adam bai tabbatar da ji ko ganinsu ba a zahiri, kamar murginawar da masu kimiyya suka ce duniya na yi, domin dan adam bai taba ji a jikinsa wannan motsin ba. In ji McCauley.

Haka kuma da yawa mutanen da a duniya suka ce ba su yarda da wani Allah ba ko abin bauta ba, duk da haka suna da birbishin imani da wasu abubuwa na camfi, kamar yarda da fatalwa da ilimin taurari da cewa idan mutum ya mutu zai sake dawowa a wani mutum a wani wuri da suran abubuwa wadanda ba za a iya tabbatarwa ba a zahiri.

Addini na sa hadin kai

Wani abu da addini kuma shi ne yana sa hadin kai da 'yan uwantaka.

Tsoron Ubangiji ko alloli ko wani abin bauta da yake ganin kowa da abin da mutum yake yi, wanda kuma duk wanda ya saba doka zai hukunta shi ya taimaka wajen zaman lafiya da bin tsari a zamanin da. Kamar yadda Atkinson ya ce.

Wani dalili kuma na karshe shi ne wanda ke jaddada tabbata da dorewar addini ta hanyar lissafi.

Bincike ya nuna cewa a ko ina a duniya mutanen da suke bin addini suna haihuwar 'ya'ya fiye da wadanda ba su da addini kamar yadda Norenzan ya ce.

Ya ce, kuma ko da a tsakanin masu addinin, masu bi sau da kafa sun fi masu sassauci yawan haihuwa, kuma kasancewar 'ya'ya yawancin lokaci suna bin sahun iyayensu a addinance da kuma akida, abu ne mai wuya duniya ta kasance ta masu akidar kin yarda da Ubangiji.

Haka kuma a kan wadannan dalilai daban-daban da aka bayyana da wuya a ce an wayi gari addini ya gushe a duniya.

Latsa nan domin karanta na harshen Ingilishi Will Religion Ever Disappear?