Me yasa muke da lebe ?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Tsuntsaye na rayuwa lami lafiya, su ci, su sha, ba tare da wani abu lebe ba, haka shi ma kunkuru abin da za a iya kira lebe a bakinsa bai yi kama da na dan adam ba wanda ke da laushi sai shi ma ya zama kamar na bakin tsuntsaye.

Haka kuma sauran dabbobi da ke rukuni daya da mutum wajen haihuwa da reno ko shayarwa suna da wannan halitta da ake cewa lebe amma kuma tasu ta yi ciki ne a bakinsu yayin da shi kuma dan adam ya zama daban a nan inda nasa leben ya yo waje.

Amfani da lebenmu wajen tsotson nono kusan shi ne abu na farko da dan adam ya iya idan aka haife shi.

Kusan ma a ce tsotson nono dabi'a ce da ake haihuwar duk wata dabba mai shayarwa da ita, wadda ba sai ta koya ba.

Yadda jariri yake tsotso hadi da kuma yadda yake kai kansa ko fuskarsa ga duk abin da ya ji ya taba shi ko ya dungure shi a baki ko kunci su ne suka hadu suka zama hanyar baiwar da jariri ke shan nono daga mahaifiyarsa.

Wannan yana farawa ne tun lokacin da aka haifi jariri, inda da zarar wani abu ya taba leben nasa, sai wannan baiwa ko aiki da jikin jaririn kusan a ce yana tattare da shi ya fara aiki.

Yayin da harshe ke yawancin aikin tsotson, labba su ke tabbatar da dauri ko kafuwar bakin a nonon ta yadda jaririn zai rika hadiya.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Wannan yana nufin shayarwa ko ta nonon uwa kai tsaye ko ta roba wato bulumboti (feeding bottle), ba abu ne da kawai jariri yake yi ba, ba tare da wani tsari ko sani ba.

Abu ne kamar tattaunawa inda kowane bangare yake taka rawarsa kamar yadda tsarin halitta ya shirya. Kuma lebe shi ne ginshikin wannan aiki da sauran sassa suke yi gaba daya.

Amfanin lebe bai tsaya ba kawai wajen tsotso har ma da cin sauran abinci da kuma wajen magana.

A fannin ilimin harse ko yare, labba, biyu ne daga cikin wurare da dama na furuci, ko wuraren cikin baki da makogaro da suke taimaka wa wajen shiga da fitar iska daga huhu.

Ka hada labbanka biyu, na sama da na kasa, za ka ji ka futar da sautin p da b da kuma m.

Kuma ka hada lebenka na kasa da hakoranka na gaba na sama daga nan za ka fitar da sautin f da v.

Ana ganin furuci wani muhimmin bangare ne na rayuwar mutum, amma kuma wasu na ganin duk da matsayinsa ga dan adam bai kai sumbata dadi ba.

Sumbata ba abu ne da kowace al'ada ta sani ba a duniya amma akalla kashi 90 cikin dari an sani.

Darwin kansa ya ce, ''akwai mutanen da a al'adarsu ba su san sumbata ba sam-sam.

Amma kuma mu Turawa mun saba da shi sosai kusan ma a ce mun mayar da shi alama ta nuna kauna da kusan ake ganin da ita aka halicci mutum.'' Kamar yadda ya rubuta a littafinsa The Expression of Emotion in Man and Animals.

Ya ce to amma fa ba haka abin yake ba ga mutanen New Zealand da Tahiti da Papua da na Australia da Somal na Afrika da kuma mutanen Eskimo.

Hakkin mallakar hoto Hulton Archive

Idan sumbata ba abu ne da ake yi ba a ko ina a duniya, duk da haka za ta iya kasancewa da tushe a ilimin halittu, watakila sakamakon dabi'un da aka haifi halitta da su da kuma wadanda ta koya.

Saboda ba mutum ba, hatta wasu dabbobi suna sumbatar junansu kamar gwaggon biri wanda yake yin hakan domin sasantawa da juna bayan an yi fada.

A mujallar kimiyya ta Scientific American Mind ta 2008 marubucinta Chip Walter, shi yana ganin sunbata ta samo asali ne daga al'ada irin ta da, inda iyaye suke tauna abinci kafin su bai wa 'ya'yansu.

Ya ce, misali matar gwaggon biri takan tauna abinci ta hada lebenta da na danta ta yad da za ta ba shi abincin a bakinsa.

Ta haka masanin ke ganin haduwar lebe ya zama wata hanya ta kawar da damuwa.

Kuma kasancewar haduwar leben na tattare da bayar da abinci hakan ke haifar da wani jin dadi tsakani.

Baya ga wannan kuma kasancewar lebe wuri ne da ya kasance matattara ta karshen wasu jijiyoyin jikin mutum taba shi yana haifar da wani jin dadi.

Wani mai bincike Gordon Gallup ya ce, ko da a tsakanin mutanen da ba su da al'adar sumbata, namiji da mace sukan kusanci fuskokin juna su lasa ko su tsotsa ko ma su shafi fuskar juna kafin su yi jima'i.

Ya ce to amma wannan sumbata da ake kira sumbatar Eskimo ba wai shafa fuskar juna ba ce kamar yadda a da aka dauka, ana yin hakan ne domin jin kanshin juna.

Ya ce, to mai yuwuwa ne sumbata ma na tattare da bukatar jin kanshin juna tsakanin masu kaunar juna.

Gallup ya gudanmar da bincike a tsakanin wani rukuni na wadanda ake ganin akalla sun kware a sumbata.

Wannan rukuni na jama'a kuwa shi ne daliban manyan makarantu na Amurka.

Hakkin mallakar hoto thinkstock

Sakamakon binciken da shi da abokansa suka gano shi ne, daya daga cikin hanyoyin da manyan mata 'yan makaranta za su iya gane ko mutum ya iya sumbata ko a'a ita ce ta kanshinsa da kuma dandano da sauransu a yayin sumbata.

Kuma kamar yadda binciken nasa ya nuna dalibai mata sun ce kafin su yarda su yi jima'i da mutum sai sun sumbace shi da farko, sun san ko ya yi musu daidai ko a'a.

Har wayau a wani binciken da Gallup ya gudanar, ya rika tambayar mutane cewa, ''akwai wanda ka taba ko kika taba sumbata amma daga baya ka ga ko ki ka ga bai yi miki ba?''

Daga cikin mazajen da ya tambaya kashi 59 cikin dari sun ce, sun taba yayin da kashi 66 cikin dari na mata su ma suka amsa haka.

Duk da cewa binciken na Gallup ya takaita ne a iya daliban Amurka to amma idan aka fadada shi zuwa wasu wuraren da kuma bayanan da aka tattara na bincike akan dabbobi, za a ga cewa lalle sumbata abu ne da ya danganci jin kanshin juna.

Kuma ko mun sani ko ba mu sani ba sumbata na sa mu san cewa wanda muke sumbata ya dace da mu ko bai dace ba.

A don haka ne duk kuskuren da ake iya gamuwa da shi yayin sumbata kamar cizon lebe ko bushewarsa da tsagewa ba abin damuwa ba ne.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Evolution: Why do we have lips?