Yadda za ka fi galabar musu

Ta yaya kake jin za ka sa wani ya yarda da ra'ayinka idan kana ganin shi ba daidai yake ba?

Nazarin halayyar dan adam ya nuna cewa hanyar da za ka yi nasara a haka ita ce yadda muka saba yi.

Mutane kan sarke da musu ko muhawara a kan wani ra'ayi na siyasa ko fahimta ta addini ko kuma uwa uba wasan kwallon kafa musamman a tsakanin matasa a yau.

A irin wannan yanayi na musu za ka ga kowa ya kafe a kan ra'ayinsa yana ganin abokin musun nasa ba daidai yake ba, kuma yawanci a tsakanin matasa za ka ga ba wanda yake son ya ba wani dama sosai ya bayyana masa dalilansa kuma wannan shi yake sa kowa ya kara kafewa a kan ra'ayinsa.

To bincike ya nuna akwai hanyar da za ka shawokan abokin musu ko muhawararka ya yarda da ra'ayinka ko kuma akalla ya sassauto a kan ra'ayinsa wadda hanya ce da ta kunshi sauraron abokin musun kuma cikin sauki ba tare da ka takarkare sai ya yarda da ra'ayinka ba.

Shekaru goma sha da suka wuce Leonid Rozenblit da Frank Keil daga Jami'ar Yale ta Amurka suna nuna cewa a lokuta da dama mutum yana ganin ya fahimci yadda wani abu ko wata na'ura ke aiki amma kuma a zahirin gaskiya fahimtarsa 'yar kadan ce ba ta taka kara ta karya ba, duk da cewa shi ba haka ya dauka ba.

Wadannan masana biyu sun kira wannan sani ko fahimta ta mutum, ''the illusion of explanatory depth'' a turance.

A binciken da suka gudanar sun bukaci wadanda suka gudanar da binciken a kansu da kowa ya fadi matsayin fahimtarsa (ma'ana ya sani sosai ko bai sani ba ko kuma bai sani ba sosai) da aikin wasu abubuwa da suka hada da bandaki mai amfani da ruwa da na'urar nuna yawan gudun mota da keken dinki.

Daga nan kuma sai suka neme su da su yi bayani kan yadda kowannensu ya fahimci wadannan abubuwa na aiki kafin kuma su amsa wasu tambayoyi a kai.

A karshe sai binciken ya nuna cewa da yawa daga cikin mutanen ba su fahimci yadda wadannan abubuwa suke aiki ba kamar yadda suka nuna kafin a gudanar da jarrabawar a kansu.

Abin da ya faru inji wadannan masana shi ne muna daukar cewa yadda muka san wadan nan abubuwa na rayuwarmu ta yau da kullum, haka kuma muke dauka muna da cikakken sani kan yadda suke aiki alhalin kuma ba haka abin yake ba.

Yawanci ba wanda yake jarraba mu a kan irin wadannan abubuwa kuma idan muna da tambaya ma a kansu sai kawai mu duba ko mu kalle su mu ce mun gane yadda suke.

Masana tunanin dan adam sun kira irin wannan hali na dan adam ,''cognitive miser'' theory.

Me zai sa mu bata lokacinmu wurin sanin abin da muke tare da shi kuma har ma watakila muke amfani da shi yau da kullum, alhalin a ganinmu za mu iya bayyana komai a kansa ba tare da mun ware wani lokaci mun yi bincike a kansa ko mun yi tambaya a kansa ba?

Abin ban sha'awa a nan shi ne, wannan ba komai yake nufi ba illa cewa mukan yi kokarin boye wa kanmu rashin saninmu ne kawai. Wato muna boye wa kanmu da kanmu jahilcinmu

Wannan abu ne da duk wanda yayi kokarin koyar da wani abu ya sani. Yawanci kana fahimtar wannan abu ne a lokacin da kake nazari ko bibbiyar karatun da za ka koyar ko abin da za ka ba da bayani a kansa ko kuma za ka gamu da abin ne lokacin da dalibin farko ya yi maka tambaya, daga nan ne za ka san cewa lalle kai ma ba ka fahimci abin ba.

Ko ina a duniya za ka ji malaman makaranta suna gaya wa junansu cewa ,'' ai ban fahimci wannan abin ba sai da na fara koyar da shi.''

Ko kuma kamar yadda Mark Changizi wanda masani ni mai bincike da kirkira ya ce, ''na fahimci cewa duk yadda na kai da rashin iya koyarwa ina koyon wani abu a lokacin da nake koyarwar''.

Bayyana kanka;

Sakamakon binciken da aka wallafa kan wannan fahimtar shucin gizo (fahimtar da mutum yake ji ya san abu amma bai sani ba), a shekarar da ta wuce ya nuna yadda za a iya amfani da shi wajen nuna wa wani da yake da wani ra'ayi ko fahimta da ya kafe a kai cewa ba daidai yake ba ko kuma kuskuren ra'ayinsa ko fahimtar tasa.

Ayarin masanan bisa jagorancin Philip Fernbach na Jami'ar Colorado suna ganin za a iya amfani da tsarin binciken ko sakamakon a kan ra'ayin da ya shafi siyasa ko ma wani abin na daban kamar yadda ban daki na zamani mai amfani da ruwa yake aiki.

Watakila suna ganin mutanen da suke da wani tsattsauran ra'ayi na siyasa za su fi sassautowa a kan ra'ayinsu su yarda da na wasu, idan aka bukace su su yi bayani kan yadda suke ganin tsarin da suka kafe a kansa suke goyon baya zai kawo sauyin da suke cewa zai haifar.

Hakkin mallakar hoto AP

Masanan sun gudanar da kuri'ar jin ra'ayin Amurkawa a kan al'amura daban-daban kama daga batun sanya wa Iran takunkumi da batun kula da lafiya da gurbatar yanayi.

Sun zabo mutanen da suka gudanar da binciken da su ta intanet, inda suka bukaci kashi daya su bayyana ra'ayinsu kuma su ba da dalilansu na wannan ra'ayi.

'yan wannan rukuni sun samu duk wata dama da wanda ake musu ko muhawara da shi kan wannan ra'ayi zai samu ta bayyana ra'ayin nasa.

Su kuma sauran da suke daya rukunin ko kashin, masanan sun bukace su, da su yi wani abin ne daban da na wadancan, inda masanan suka bukace su da su bayar da bayani kan yadda suke ganin tsarin da suke goyon baya zai yi aiki.

An bukace su su yi bayani daki-daki tun daga farko har karshe hanyar da za a bi wajen aiwatar da tsarin har ya kai ga sauyi ko tasirin da suke ganin zai yi.

Sakamakon binciken biyu ya bayyana karara, inda rukunin wadanda aka bukace su su bayar da dalilansu na ra'ayin da suka kafe a kansa suka ci gaba da kafewa a kai kamar yadda suke kafin wannan jarrabawa da aka yi musu.

A daya bangaren kuwa, 'yan daya rukunin, wadanda aka nemi su bayar da bayani kan ra'ayin nasu, suka sassauto a kan ra'ayin nasu har ma suka nuna rashin fahimtarsu da ra'ayin nasu.

Mutanen da kafin jarrabawar suke goyon baya ko adawa da batun fitar da hayakin masana'antu da ke gurbata yanayi, suka sassauto a kan ra'ayinsu, suka nuna alamun ja da baya kan wannan ra'ayi da a da suka dauka na goyon baya da tsarin ko adawa da shi.

To wannan hanya ce da za ka iya amfani da ita a duk lokacin da kake kokarin shawo kan wani a kan wani abu da kuke musu ko muhawara a kansa. Abin ya shafi siyasa ne ko addini ko wasan kwallon kafa da makamantansu.

Kai dai abin da a ko da yaushe za ka zama da shiri a kansa shi ne ka tabbatar ka tanadi bayani cikakke kan dalilan da suka sa kake da ra'ayin da ka kafe a kansa wanda kake ganin shi ne daidai, idan ba haka ba kai ne abokin musunka zai yi galaba a kanka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The best way to win an arguement